Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

naiya sbd mahaifiyata ba wacca tafiso kamar Amina matata ta biyu da yayanta, kokad’an bata k’aunar maryam gashi nikuma ina matukar k’aunar maryam. Babban abun tashin hankalin maryam shine, tarin dukiyarda takeda wacca tarasa magajinda koda bayan ranta zai gaji dukiyar, sannan koba komai itama tanasan taga nata jinin a duniya, ahalin yanxu ido rufe take neman yaya wannan dalilin ne yasa nanemi wani doctor a india wanda abokina yahad’ani dashi, Tofa shine yamana wannan aikin har aka samu wannan cikin, ba kalar farincikinda maryam da ahalinta basuji ba sbd samuwar wannan cikin har kyaututtika aka bata wasunsu kuma sunce sai idan tahaihu zasu bata. Doctor idan har ya tabbata wannan babyn yamutu me kake tinanin zai iya faruwa ahalin yanzu...?”. Zama doctor yai akan kujera tareda sauke nannauyan numfashi, yad’auki tsawon sakanni kamin yad’ago yacewa kadel “yanzu mekake buk’atar ayi kenan, ina nufin wane taimako kake buk’atar namaka?”. Dajin haka sai kadel yazauna kan kujera tareda kara matso daita dab da doctor sannan yace “inaso ka taimakeni ka k’aryata wannan mutuwar babyn nawa” cikin rashin fahimta doctor yace “as how...ban...banfahimceka ba” kadel yacigaba da fadin. “Inasan kamana exchange na babyn mu da d’aya daga cikin jinjirayenda aka haifa a yanzu, nikuma namaka alk’awarin kud’i tindaga naira million d’aya har izowa naira million ashirin a kud’in najeria, dan Allah ka taimaka doctor please....!!!”. D’an murmushi doctor haji yai sannan yad’an d’ago daga risinarda kansa da yai tareda mik’ewa a tsaye yai tako d’aya zowa biyu sannan yajiyo yakalli doctor haji yace “wannan abun da zamuyi yanzu kasani yana d’aya daga cikin manyan laifuka a kundin dokar k’asar nan, hakama yana d’aya daga cikin babban laifi na wannan asibitin wanda idan har aka kama dik likitanda ya aikata hakan hukuncinsa d’aurin rai da rai a gidan kaso, sbd haka zan taimakeka a sbd halinda naga kake aciki wanda har kaiya fallasaman asirin gidanka”. Kadel najin haka baisan lkcnda yasauke wani irin nannauyan numfashi ba taredayin wani irin murmushi wanda rabonsa dayin irinsa tin shekaranjiya da hajiyarsa tafara labour. Doctor yacigaba “toh ammafa kasani, karka kuskura koda da b’acin rana wannan asirin ya fallasa sbd kaimafa ba fita zakayi ba sannan kuma kan nabaka babyn saika cike waensu takardu tareda yin signing akan wata takarda, ya ka amince...?” ai dasauri yace “wal...wallahi na amince kuma insha Allah ma wannan sirrin bazai tab’a fallasuwa ba har abadah”. Dan murmushi doctor yai yace “good...yanxu muje d’akinda ake ajiye new babys, akwai wata mata data haifi twins dika mata so zamu d’auki d’ayar saimu ajiye naku babyn, kaga shkn dole ya tabbata nasu babyn ne daya yamutu” kadel dajin hakan sbd tsananin farinciki baisan sadda yarungume doctor haji ba yashiga masa gdy. Nantake yace doctor yaturamasa account number dinshi zaiji dumus. Daganan office din suna fita kadel yacewa su uwani suje gun driver yamaidasu gida su d’akko abinci da sauran kaya kamin afito da baby dakuma hajiya,ba musu sukace toh sannan suka wuce. Aikwa suna wucewa shikuma yawuce gun doctor, dama anwuce babyn d’akinda ake ajiye new baby’s kamin asallami mai haihuwa, danhaka sunsami yanda sukeso. Nan suka shiga aka d’auki d’aya daga cikin twins din aka cire kayan jikinta sannan aka cire na nasu babyn aka sakamawa wannan twins din itakuma na twins aka sakamawa babyn su data mutu sannan aka kwantarda ita kusa da d’ayar twins din sannan suka wuce da dayar twins din. Hmm...farinciki agun Alhj kadel baya misaltuwa haka yaje da babyn har d’akinda jolde take har yanxu tana bacci. Abun mamaki koda jolde ta farka sai aka mik’a mata babynta, tsananin mamakine ya bayyana k’arara a fuskarta wanda takasa b’oyewa har saida tamawa kadel magana, anan take ya fayyace mata yanda sukayi, wani irin kuka ne ya kwace mata taita yinsa tana fadin “badan nafita gori da wulak’ancin mahaifiyarka ba sannan nasamu magaji nakuma sami wanda zan rik’a gani amatsayin jinina ba nima nasamu wanda zan kira da d’ana akuma kirani da mama wlh da bazan karb’i wannan jaririyar ba” haka taita kuka tana kallon wannan babyn daketa faman bacci. Saida tai 6hrs da haihuwa sannan aka sallamesu. Hmm koda suka koma gida tini gidan yacika fal da mutane masoya,fiye da rabin unguwar maza da mata sunzo tayasu murna, sukowa sai farinciki suke suna wasan hak’ora, nantake jolde takira gida Nigeria tasanardasu ta haihu hakama k’awayenta da dik wani masoyinta yaji wannan abun alkhairin daya sameta. Aikwa daga mai kiran waya sai mai turo tex message na taya murna, hakama kadel sai kiran mutane yake yana fad’amasu tamkar yanzune aka fara haifarmasa, shikansa yasan farincikinda yakeji a yanzu ko sanda aka haifa masa d’ansa na farko baiji kamarsa ba. Bayan kwana biyu da haihuwa suka tattara suka koma gida Nigeria. Hmm....readers naso kuga abunda ake kira gata na duniya kuma na zahiri, gidansu maryam jolde babban gida ne irin wanda ake kira da family house, kaka mace da kaka namiji da uwa da yayye maza dakuma matansu da yayansu dik suna acikin gidan,sannan jolde itace auta a gidansu kuma itace mace ta biyu da aka haifa a gidan, and’auki san duniya and’ora mata to wannan san ne yanzu yadawo kan y’arta data haifa a yanzu. Haihuwar tazamo tamkar itace ta farko da akafarayi a gidan, yaran gidan kowa sai zumud’in d’aukan babyn sukeyi wacca tini suka rad’a mata suna FATIMA ZAHRAH wato sunan kakarsu hajiya baaba sai suna kiranta da zahrah. Saidaifa wata sabuwa inji yan chacha, har yanzu zahrah taki tak’arb’i nonon jolde idanma tad’auketa takaimata nonon a baki saita tsala ihu taita kuka, danhaka ba yanda aka iya dole aka cigaba da bata madara. Haihuwar zahrah tazamo tamkar itace haihuwa ta farko da aka farayi a tsakanin wannan ahalin biyu,maana dangin mahaifinta dana mahaifiyarta musamman ma na mahaifiyarta. Tinda suka iso Nigeria aka fara fitarda naira ana b’arinta domin shirye shiryen shagalin biki tamkar ba’asan zafin kud’inba. Alhj kadel tamkar yanzune aka fara haifa masa ya, baya iya wuni d’aya baizo yaga lafiyar yarsa ba, zan iya cemaku fiyeda rabin sonda yakemawa jolde yakoma kan zahrah, hakama k’annensa mata da maza damacan su jolde sukeso basasan kishiyarta Khadija momyn ammar, toh sumadai su ammar din sunso suzo suga yar kanwarsu amma mahaifiyarsu tahanasu, gaba daya ma ta kwashesu sunwuce London dikda ba’ayi hutun makaranta ba. Hajiyar kadel kowa tini tacanjawa jolde fuska,yanxu kamar ta had’iyeta takeji damacan rashin haihuwar ne yasa batasanta, yanzu kwa harda kyautar galleliyar mota tamata, kai masha Allah wannan yarinyar tazo da tarin alkhairai. Ranar suna haka akai shagali nagani na fad’a,yanda akayi bikin tamkar jikar shugaban k’asa, bikin yak’ayatar sosai yarinya dai taci sunanta na fatima zahrah wato sunan kakarta mahaifiyar jolde, saidai mahaifiyarta tace arik’a kiranta da BUNAYYAH, toh masha Allah ubangiji ya raya Bunayya ameen. Bayan sati biyu da biki kadel yakoma Uganda sbd kasuwancinsu amma time to time yakan hawo jirgi yazo yagansu yakoma. Kulawa ta musamman akebama jolde da babynta bunayya, koda suka cike wata biyu sunyi b’ulb’ul dasu gwanin birgewa bunayya tai kiba barakallah gata daka ganta kasan jinin fulani ce kanta dikya cika da suma kamar ba’amata askin suna ba. Sati daya suka k’ara akan wata biyu suma suka tattara suka koma Uganda. ...................... Maryam Ahmad Abdallah inkiya JOLDE haifaffiyar k’asar kebbi state ce acikin bagudo L/gvmnt,

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});