Chapter 16
Chapter 16
fitarda hudu,saidai mashkur yahana sutafi da security’s ko bodyguards yace wannan matsalar cikin gida ce. 10:30am dot sukabar garin yola izowa kasar kebbi state. Saikusan 3:30pm sannan suka iso kebbi state,kai tsaye gidansu bunayya suka nufa wato gunsu momy kenan, koda suka iso masu gadi suka tabbatar masu da dady yafita tin d’azu,nandai aka bude masu get suka shiga,mota natsayawa bunayya tabude tafito tafice dagudu tana kiran sunan “momy...momy...momy naaa....” hajiya jolde dake kitchen tana aiki jin muryar farincikinta yasa tafara murmushi sannan tafito tana fadin “na aaam....abar k’aunata” dagudu tazo tarungumeta tareda fashewa dawani sabon kuka. Hankalin hajiya jolde ne yafara tashi tashiga tambayarta abunda ke faruwa,tana shirin fara mata bayani saigasu mashkur sunshigo. Ganin ruwaida da momynsu yasa tawaro ido cikin tsintsar tashin hankali,kallon bunayya tai tace “bunayya a ina kika hadu da waennan ne,su waye su?” ammin mashkur ce tace “dawaennan tambayoyin naki dafara bamu wajen zama kikai tukuna dazaki samu amsoshinki dika kuma a nitse” ba musu kowa momy tamasu bismillah suka zauna. Wayarta tad’auka takira dady tacemasa dik inda yake yadawo gida yanzu,har yatsaya tambayarta abunda ke faruwa saita katse kiran,tsawon 1hr bawanda yakecewa komai har dady yaiso. Kansane yad’auki jiri a lkcnda yagasu ruwaida musamman ma dayaga bunayya kusa da momy saikuma yaga ruwaida kusa da mashkur,shikanshi badanda suke a rarrabeba dabazai iya gane wacece bunayya ba sbd yaga dik fuskarsu iri daya ce hatta hasken fatarsu ma iri d’aya ne. Yana ganin haka yatabbatarda lallai ranarda suke gudu tazo,ahankali yakariso parlon sannan yaje yabama su dadyn mashkur hanu suka musabaha suka gaggaisa sannan yazauna, bayan yazauna saiya fara magana “am...meke tafe dakune...?”Dadyn mashkur ne yafara magana. “Toh dafarko dai munayiwa Allah gdy, saikuma abunda yakawomu shine,munaso muji daga bakinku,shin wacece bunayya agurinku, kunsandai tinda kuka ganmu ahaka to tabbas babban al’amarine yakawomu,munhana kowa yasan wannan lamarin sbd matsalace ta cikin gida,to sbd haka kufad’amana gskyr wannan lamarin sbd bamasan abun yakaimu ga b’acin rayuka namu ran yab’aci haka kuma naku ran yab’aci” shuruu dady yai batareda yaiya cewa komaiba yayinda momy ke zubda zafafan kwallah,haka bunayya ma ganin momynta na kuka yasa itama takasa daina kukan. Nannauyan numfashi dady yasauke sannan yafara magana “toh dafarkodai kamin nafara cewa komai inamai baku hkr dakuma neman yafiyarku akan babban lefinda muka maku tsawon shekaru goma sha tara, tabbas bako tantama shekara goma sha tara ne cif cif, tabbas fatima bunayya yarmu ce,amma azahirin gsky bamune ainahin iyayentaba sbd bamune muka haifetaba.....” wannan kalmar tadaki k’irjin bunayya har saida wata kwallah tazubomata a ido d’aya. Dasauri ta mik’ewa a tsaye tareda fadin “karka gasgata abunda suke fada dady,karka biyemasu dan Allah,wlh ni bazan yardaba banida wasu iyaye a duniya bayan ku,kune iyayena dady dan Allah kada kuce bakune kuka haifeni ba” saita kalli momynta tariko hanunta tace “please...momy ki k’aryata abunda dady yake fada dan Allah” janyota tai tarungume sbd matsanancin kukanda take sam bazata iya juresaba. Dadyn mashkur yace “to Alhmdllh tinda baku wani wahalarda shari’ah ba, to atak’aice dai yarona mashkur wanda school daya da yarku shine yai tsawon bincike harya gano cewa tabbas bunayya jininsa ce,to yanzu kunga ainahin iyayen bunayya” abban ruwaida ne yai saurin karban zancen dafad’in “kusani wlh kun cutarda mahaifiyarta haka nima kun cutarda ni bakad’an ba,amma kunci arzikin baku renarmana ya acikin k’unci ba,alama tanuna cewa ta tashi acikin jin dad’i amma badan hakaba wlh dasaina d’aureku har abadah banga kuma wanda yaisa yafitardaku ba, amma dikda haka inaso nasan yanda akayi yata taje hanunku?” Numfashi dady yasauke sannan yafara basu lbrn komai,tindaga haihuwar ainahin d’anda momy tahaifa har izowa satar bunayya tahanyar tacanjata da nasu babyn” cikin tsintsar bacin rai dadyn ruwaida ya mik’ewa tsaye cikin fushi yaje yadamko hanun bunayya tareda fadin “baku cancanci nabarku haka kawaiba batareda nasaka maku da mafificin alkhairi ba, tindaga kan wannan doctor din har izowa ku namaku alk’awarin sakayya mai girma” yana gama fad’ar hakan yakama hanyar fita, dasauri momy taje gun dady tana cemasa “karka bari yatafiyarmin da y’a dan Allah,yata kadel ka karb’oman abata please wlh bazan iya rayuwa babu itaba dan Allah kadel” tana magana cikin matsanancin kuka, dady tarungumeta yana fadin “come down jolde,kidaina kukan nan kada kijanyowa kanki matsala,kamar yanda kike kaunar bunayya haka nima nake kaunarta kuma bazan taba bari yatafi daita ba harsainai yanda dik zanyi nadawo daita hanunmu sbd mune iyayenta,wlh koda zan rasa dik abunda na mallaka ne sainadawo da bunayya gidan nan,just come down jolde”. Itama bunayya kuka mai tsanani takeyi tana kiran momynta,haka itama momyn kuka take sosai wanda tama manta rabonta da tai irinsa. Bayan yafita sai mashkur yacewa su momy “dan Allah kuyi hkr dady,insha Allah zamu shawo kan dady zai hkr,bunayya zata dawo hanunku insha Allah, just come down momy” momy kam takasa hkr sai kuka take kaman ranta zai fita. Itafa bata taba tinanin wannan ranar zatazoba shys ma batai shirin zowanta ba,gashi yau anrabata da abar kaunarta farincikinta,shin wace amsace zasubama duniya a lkcnda aka fara tambayarsu,shin tayama zata iya rayuwa babu bunayya akusa daita,sam hakan bazai taba kasancewa ba. ................. Tinda aka tafi da bunayya har izowa yanzu kuka take,tak’i ci tak’i sha idanuwanta dik sun kukkumbura sbd kuka har wata yar rama tai sbd wahala. Daga d’aki sai d’aki bata fitowa koina,mahaifiyarsu tayi iya kokarinta amma takasa shawo kanta sai kiran momy da dady take. Bayan kwana biyu kacal da faruwar wannan lamarin mahaifinsu bunayya yashirya tareda dadyn su mashkur suka tafi k’asar Uganda. #/Comment nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI...._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _25/26....._ Har izowa yanzu bunayya takasa kwantarda hankalinta,banda kuka da kiran momynta ba abunda take,koda umman su ta ankara wani zazzab’i mai k’arfi yarufeta gashi tana fama da ciwon maranta lkc yayi,takasa fad’awa kowa sai ramlat ce tagane kasancewar atare suka kwana dan ruwaidah nagidansu mashkur. A gigice taje tafad’awa ummansu tazo,haka suka b’allamata magunguna amma tak’i sha gashi sai murk’usu take gakuma jikinta yai gaja gaja da zazzabi yai zafi sosai gakuma amai datakeyi. Tak’i tasha magani haka kuma tak’i yarda akira doctor kokuma aje hospital daita sai kiran momynta take tana kuka. Tintanada k’arfi har k’arfinta yafara raguwa,hankalin ummansu yatashi matuk’a gashi dadyn ruwaida bayanan, cikin tashin hankali takira mashkur sbd dadyn mashkur sunyi tafiya outside. A hargitse mashkur yazo gidan,koda yazo wani mini towel ne ajikinta amma dikya b’aci da amai gashi sai murk’ususu take tana kuka tana kiran momynta,jinin period kuma yafara zubarmata sbd takasa iya tashi bare tagyara jikinta, hankalinsa ne yamatuk’ar tashi ganinta ahaka,gaba daya rikicewa yai ya rud’e yama rasa mezaiyi gashi itama ummansu kuka take sbd ganin halinda yar tata take aciki, gashi tasani rabonta dataci abinci tin ranarda lamarin ya auku,sbd haka harda yunwa nadamunta. Gaba d’aya mashkur rikicewa yai sai kawai yakwasheta yawuce toilet sannan yakira ummanta yace tazo tagyara mata jikinta shikuma yafito yacewa ramlat taciromata riga mai saukin sakawa zasuje hospital ne. Dasauri tad’akko daidai lkcnda umma tafito da bunayya tana taimaka mata suka fito,rigar kawai umma tazuramata mashkur yazo baijira komaiba yad’auketa suka fita,gaba daya tagalabaita yatsanta bata iya d’agawa sai sunan momy kawai take kira,umma kawai tashiga motar tace ramlat takula da gida da sauran kannenta. Kai tsaye hospital din momyn mashkur mai suna Sir haroon memorial hospital suka fice,suna isowa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34