Chapter 27
Chapter 27
sunbata daddad’ar rayuwa wacca take cike da tarin farinciki da jin dad’i. Saikusan asuba sannan bacci yad’auketa. Washe gari ranar d’aurin aure anko tayi da momyn ta, wata tsadajjiyar shadda suka saka gizna light blue mai shegen kyau akamasu dinkin gown aka saka mata stones agaba, bayan sunshirya sai akamasu pictures masu kyau. ...................... Around 10am dot aka d’aura auren MASHKUR ABDULLAHI da FATIMA KADEL KABIR akan sadaki mafi tsoka naira dubu d’ari cif masha Allah,abban ramadan shine uba shiya bada auren inda abban ruwaida yazama uban mashkur ya karbi auren. Allah isanyawa aure albarka ameen. Can nahango ango acikin dandazon bil adam sai washe hakora yake yana musabaha da mutane masu masa Allah sanya alkhairi yana amsawa, shi da babban amininsa mahbub wanda suka taso tare tin yarinta har girma kayansu iri d’aya farar shaddah mai manyan riguna maikyan gaske,dakaganta kasan taci kudi sosai kodan irin yanayin d’inkinda akamata kasan bak’arama bace. Ya ramadan hargun mashkur yaje yabashi hanu yamasa Allah sanya alkhairi cikin sakin fuska sannan yawuce, sai bayanda yawuce ake fadamasa shine wanda yafara san bunayya kuma d’an kanen dadyn bunayya ne, nantake kishi yamotsawa mashkur saiya tab’e baki kawai. Saikusan 1pm sannan sukabar jihar kebbi suka fice yola adamawa, acan d’inma canja kaya yai suka fice gunda zasu gudanarda tasu walima kan amarya taiso. ...................... A b’angaren amare kowa,tinda aka fad’a an daura aure bunayya take tana kuka tamak’ale gun momy tana kuka tin tanayi momy na rarrashinta cikin taisasan kalamai har tazo tasaka zuciyar momy tai rauni takasa hkr itama tafara kukan. Dakyar aka samu suka hkr aka fice da bunayya gunda zaayi walima. And’auki tsawon lkc ana gudanarda walimar inda wata shahararriyar malama ta gudanarda walimar, tayi nasihohi sosai akan zaman aure nasihohi masu ratsa jiki waenda suka k’ara narkarwar bunayya da jiki, bayan angama sannan aka d’akko amarya tareda k’awayenta izowa gida. Bayan sun iso ne aka fara shirin tafiya yola kai amarya, aunty kuluwa ce tai tsaye wajen shirinta, saida tashirya tsab sannan suka sakata agaba sunamata hud’uba, momy aunty kuluwa yaya hauwa da aunty Rukayya da dai sauran yan uwan momy mata. Sund’an jima sunamata nasihohi sosai akan tarik’e mijinta dakyau ta k’aunacesa kamar yanda shima yanunamata k’auna, lefenta nacan gidanta ankaimata sbd al’adar gidansu dady ce ba’akarb’an lefe saidai mijinki yamaki ya ajiyemaki a gidansa idan kikaje yabaki, to itama mashkur yamata nagani na fad’a, set din akwatayya biyar kuma kowacce Alhmdllh kawai zaace, bayan wanda abban ramadan yamata wanda dama hakan su sukeyi, shima yamata set uku na akwatayya shima kuma yayi kyau sosai, dik d’inkunanda tasaka na biki shine yamata su, haka suma su ya Amir sunmata nasu amatsayinsu na yayyenta ya ramadan ma yasiyamata galleliyar mota amatsayin kyautarsa bayan kuma kayan d’aki dasuka siyamata amatsayinsu na manyan yayye. Sbd haka suma karta yarda tasakesu tarik’esu gam hanu bibbiyu. Hakama iyayenta na yola karta yarda tasakesu tarikesu kuma tabasu girmansu da Allah yabasu, sannan tama mijinta biyayya, takumayi hakuri sbd zaman aure saida hkr yakeyin kyau har aji dadinsa. Sundaimata nasihohi sosai har saida motoci sukazo zaatafi sannan suka bari, momy narikeda bunayya itama tarike momy gam tanata kuka,ita kuka momy kuka dakyar aka rabasu aka shigarda bunayya acikin mota sannan suka wuce tana kallon momynta itama tana d’agamata hanu. Saida akaje daita gidan hajiyarsu dady itama tad’ora da tata nasihar daga bisani aka sake kaita parlon abban ramadan shima yamata tasa nasihar sosai akan zaman aure, Sai kusan 3:30pm sannan sukabar jahar kebbi suka kama garin yola adamawa,har yanzu bunayya kuka take sosai tanajin kewar momynta na ratsa jikinta sosai. Around 7:45pm dot suka isa garin yola adamawa, kai tsaye gidansu mashkur aka wuce daita, abban ruwaida da dadyn mashkur suna parlon dadyn mashkur suna shan coffee. Bayan anshiga daita ciki yan uwan momyn mashkur mata biyu suka taryi amarya,parlon momy suka shiga daita sukamata yan nasihohi kamin daga bisani suka kaita gunsu dady, acan dinma nasihohin su abba suka mata, har yanzu bunayya takasa daina kuka. Mashkur nagun abokanansa sunajiran lkcn tafiya dinner yai sufara shiri sai ruwaida takirasa tafadamasa sun iso tareda amaryarsa yanzu haka sunanan gida,wani irin farinciki yaji ya lullub’eshi kamar yaje ya rungume bunayya. Bayan su dady sunmata tasu hud’ubar sannan aka d’auketa izowa ainahin gidanta na sunnah na aure. Hmm.....Masha Allah nafurta lkcnda naga motocin amarya sunyi parking acikin wani kantamemen gida wanda ya amsa sunansa gidan, hak’ika Allah yayiwa d’an adam babbar baiwa, idan kaga wannan gidan na bunayya sam bazakace mutum yaginasa ba, zamaka d’auka computer ce taginasa kokuma kace bama ginasa akayiba kawai kafasa akayi ya tsaya. Bayan amarya tafito sannan aka shiga daita izowa cikin gida, ta babbar k’ofa akabi izowa main parlor cikin basmala taredayin adduoi takuma saka k’afar dama sannan tashiga cikin parlon. Kai tsaye aka haura daita sama izowa bedroom d’inta, gidan hawa biyu ne bedrooms dik asama suke k’asa babban parlor kitchen da toilet sai d’akun masu aiki. Bayan sunshiga sannan sukai sallar magrib kowa yai wanka, 8:30pm suka fara shirin tafiya dinner, suna zaune mai make-up din bunayya tazo tareda wacca zatayi make-up din kawayen amarya da dai sauran tarkacen amaryar. Acikin 2hrs aka gama gyara amarya tsab acikin wata arniyar wedding gown mai fitinannen kyau, musamman data had’u da jikinda yafita kyau da tsada dakuma k’arko, saita zauna ajikin kamar damacan dan jikin aka d’inkata kasancewar ta kanti ce aka siyo ba d’inkawa akayiba mashkur ne ya aiko dasu. Make-up dinta yakara fito da ainahin kyanta sosai hancin nan yakara tsayi bakin nan yasha janbaki kala kala,dik yanda zan misalta maku kyan bunayya readers bazaku ganeba tawuce hakan saidai na kwatanta maku kawai. Rigar pich and cee green color ce mai dan haske, dan kwalin ma cee green ne sai daurin yakara fitoda fuskarta tana shining, bata saka brez ba sbd yanayin rigar baya bukatar brez aikwa bobbs dinta sundan taso asama, takalmanta da jakarta silver color ne. Bayan angama komai sai ruwaida takira danhaka akazo d’aukansu. Rigar amarya tayi tsayi sosai a bayanta tai kamar jela tana ja da k’asa dole saida aka tallabe bayan aka rik’e sbd karya kadata, saida aka bud’e mata murfin mota tashiga suka sako jelar aciki sannan suka rufe. Daddad’an k’amshin tirarensa wanda ko amafalki tajisa tasan nashine sbd agunsa kad’ai tasan tiraren takuma tabajinsa yasa tajuya gefenta ahankali takallesa, ahankali kuma tasake juya fuskarta izowa gabanta, wani irin yanayi mai dad’i yaji yashigesa har saida yai murmushi, ahankali kuma yakai hanunsa kan nata tareda matsa yatsunta batareda yadubetaba. Dan rintse idanuwanta tai alamar taji zafin matsar amma bata kallesaba sai kawai tajanye hanun nata kawai, dan matsawa yai kusa daita yana fuskantarta sannan yakai hanunsa yashafa cikinta tareda yimata cakulkuli kadan, hakan yasa tadanyi murmushi shima saiyai murmushi. Duk’o da fuskarsa yai daidai tata sannan yafurta “u look so beautiful, nayaba wannan kwalliyar tamun kyau sosai” yak’arisa yana juya hanunta yana kallon lallenta, ahankali kuma yai kissing din hanun. Hararanda mahbub yamasa ta glass ce yasa yagyara zamansa yana dariya. Bawata doguwar tafiya sukaiba suka iso gunda zaa gudanarda dinner din, bayan motoci sungama parking sai mahbub yazo yabid’ewa bunayya murfi tafito sannan shima mashkur yafito. Atare suka jera ango da amarya sai kawayen amarya da abokanan ango suka take masu baya, ahaka har
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34