Chapter 25
Chapter 25
ke...! barina na auri bunayya shine mafi a’ala agareki,inasan bunayya kuma AURENTA ZANYI......! daga mijinki uban d’anda ke cikinki a yanzu haka,ki kulamin da d’ana sainazo kawomaki amaryata” tana kawowa nan saitai baya jiri yad’ibeta zata zube kasa dasauri uncle Aminullah yai rik’eta tazube ajikinsa somammiya. Tashin hankali wanda ba’asaka masa rana, dasauri aka wuce da momy hospital yayinda uncle Muhammad yakira AIG of police dakuma IG d’insa yazubemasu mak’udan kud’i sannan yace yana buk’atar akawomasa kadel nanda kwana d’aya kacal,dik inda yaje afad’in duniyar nan yana buk’atarsa nanda kwana d’aya kacal. Wannan karon kam ran uncle Muhammad yamatuk’ar b’aci kuma yayi alk’awarin hukunta dady hukunci mafi muni. Nantake aka baza neman dady ruwa a jallo tamkar wanda yai kisan kai,kankace me koina anji neman Alhj kadel wanted. ......................... Wani d’an gidane sukaje daita wanda baifi d’aki d’aya da parlor da toilet ba,saida suka iso daita sannan suka bud’e mata idanuwanta suka kwance mata hannayenta,bud’e idonta dazatayi sai taga dadynta tsaye agabanta yahard’e hannayensa,cikin tsintsar mamaki tace “dady...!”. Ahankali yamatso kusa daita sannan yafara magana “karki sake kirana da dady,daga yanzu kid’aukeni amatsayin mijinki ba uba ba,sbd gobe iwarhaka kinzama matata dole kizama matata bunayya kokinaso ko bakyaso dole ne” ahankali tafara magana itama. “Koda zai tabbata zaka zamo miji agareni bazan tab’a daina kiranka dady ba,wai wane irin shaid’an ne yahau kanka dady na,wane irin shaid’an ne wannan dayake cusamaka sha’awar aurena aranka bayan kaima dakanka kasani fad’ar wannan kalmar ma a tsakaninmu k’azanta ce,ni y’ace agareka kuma har gobe ina kallonka amatsayin ubana wanda yahaifeni,koda da rana d’aya bantab’a kallonka amatsayin ba ubana ba,taya zaka kusanto wannan k’azamar kalmar atsakaninmu dady,haba haba kadawo hayyacinka mana kakumayi gaugawar korar shaid’an dinda ke haskomaka ni dakuma shaawar aurena”. Cikin zafin zuciya yadamk’o sumarta har saida tai k’ara sbd zafinda taji cikin kakkausar murya yace “kidaina yaudarata da waennan zantikan naki bunayya,sbd bamakawo saina aureki,ina sonki bantab’a yimaki kallon y’ata,sbd haka dolene kishirya k’arb’ata amatsayin mijinki” yana gama fad’ar hakan yajefarda ita sannan yajuyo gun yaransa yace. “Ina buk’atar kuje kuyoman visa na malaman nan guda biyu yau dinnan sbd inaso mubar k’asar nan gobe tinda sassafe,kunga kuma malaman nan sune zasu d’auran sbd haka dole dasu zaayi tafiyar,saikuma ina bukatar masu lalle da gyaran amare acan k’asar Abu Dhabi domin su gyaraman amaryata” cikin tsintsar girmamawa sukace “Ok Sir....angama” saiyajiya yafice kawai. D’aukan bunayya sukai suka tura acikin d’ayan d’akin suka rufe,saida dare sannan suka kaimata abinci aciki, banda kuka ba abunda bunayya takeyi tarasa mezatayi ta kub’utarda kanta gashi ba waya hanunta sun karb’e. ..................... A b’angaren su momy kowa,gaba d’aya k’asar Nigeria ba inda ba’asaka neman Alhj kadel ba,anma saka mak’udan kud’i wa dik wanda yagansa yafad’a,kafafen sadarwa na gidajen radio da tv dakuma social networ,hakama filayen jirage da bododi na iyakar k’asa,kai koina da koina ma neman dady ake ruwa a jallo,police da sojoji ba bacci sai patrol ake. Aslm my people..... am ina mai baku hkrn jina shuru edays,wlh wata yar matsalace ta taso amma Alhmdllh komai normal yanzukam,ngd da k’aunarku kan littafena,love u all my fam 💋💔 #/Comment nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI...._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _35/36....._ Acikin daren ranar k’asar kebbi zaka d’auka gomnan jihar aka sace gaba d’aya sbd yanda sojoji da police ke nuna tsaurin bincike,sai laifin ma yashafi kowa da kowa sbd dik wani d’an k’aramin laifi antonoshi, rashin driving license da kama yan shaye shaye masu yawon dare dik sai kamasu ake. Bacci ya gagari momy hakama su uncle Muhammad,hajiyarsu momy kowa sai nafiloli take tana kaiwa Allah kukansu had’eda tsinewa dady albarka. Har kusan 2am amma bawani lbr,uncle uthman yasake kiran DSP jamil ko ansamu wani lbrn yacemasa har yanzu shuru, ganin lmrn ya girmama yasa akakoma ga Allah akacigaba da nafiloli, babban tashin hankalin momy shine rashin sanin halinda bunayya take a ciki saikuma addu’arta itace kada dady yasaka ad’aura masa aure da bunayya. Koda lbr yarizk’e su mashkur a gigice mashkur yaiso kasar kebbi tin around 8am su dadyn sa ne suka iso 10am, hankula sun tashi matuk’a. Hakama hajiyarsu dady yanzukam kokad’an bata goyi bayan dady ba hasalima ranta yai mummunan b’aci akan halin akuyancinda dady keyi, da bakinta take fad’ar “wannan wane irin abune wane irin haline wannan,ka raini yarinya a hanunka ta tashi taganka amatsayin ubanta amma yanzu kace wai itace kakeso da aure, wannan abun ko agarin maguzawa bantab’a jin irin wannan lbrn ba”. Abban ramadan ransa yai matuk’ar b’aci su yaya ammar da ya amir kowa kuka suke sosai dandai bayanda suka iyane dady mahaifinsu ne amma dasunyi Allah wadarai da halin dady. .................... Har safiya ta waye bunayya batai bacci ba,sai kuka take tana adduoi na neman kariya daga sharrin dady,tayi iyayinta domin tasamu hanyar guduwa amma bawata damar yin hakan, d’akinda take a ciki ma window d’aya yakeda kuma dik a rufe take da k’arfe sanyin ac ne ke d’umama d’akin kawai, k’ofa kuma a rufe take gam gashi tanama jiyo sautin maganganun bodyguards din dady. Ahaka tacigaba da adduoi tana kaiwa Allah kukanta har safiya tawaye,yaye labulen window tai taga haske hakan ya tabbatar mata da safiya tayi,danhaka tashiga toilet dinda ke cikin dakin ta d’auro alwala tafito,mayafinta dasuka d’auremata hanu ta yafa takabbara sallah. Tana cikinyi sai d’aya daga cikin masu tsaron yashigo ya ajiyemata wata leda sannan yafita, bayan taidar bata tab’a ledar ba, tana zaune tana adduointa saigashi yasake shigowa,fuskarsa ba annuri ko faraa a tamke take babu alamar rahama a tattare daita yacemata “gakayanan kisaka oga yazo zamu wuce” uffan batace dashiba harya fita kuma batako kalli ledar ba. Bayan dakamar 10mnts yasake dawowa tana zaune abunta tana adduoi dake bakinta,yana ganinta inda yabarta a zaune ko tab’a kayanda yakawomata bataiba ai dak’arfi yaje ya wanketa da kyawawan marika har biyu sannan yadamk’o sumarta har saida tabuga wata iriyar k’ara sbd azaba,cikin kakkausar murya yace “kid’auki kayan nan kisaka dan ubanki, nabaki minti biyar kacal idan bahakaba zaki yabawa aya zak’inta” saiya jefarda ita tafad’i a kwance sannan yad’akko ledar ya wurgamata yafice. Kuka take sosai goshinta har yabige haryai d’an jini hancinta ma yazuboda jini, da hanunta ta goge jinin sannan ta tashi tadauki kayan tasaka, doguwar jallabiya ce da hijab brown da nik’ab, bayan tasaka sannan tai zamanta anan. Bayan dakamar 5mnts yaron yadawo yafizge hanun bunayya suka fita dasauri, sai agaban dady yatsaya daita tareda fad’in “Sir...komai yazama ready yanzu” cikin k’asaita irinta dady yad’aga masa hanu alamar ok sannan yamik’e tsaye cikin izza. Shikuma yaron yajawo hanun bunayya suka fita, mamaki ne yacika bunayya ganin yanda dady yacanja kamanni a fuska,a jikinsama k’ananun kaya ne wandan jeans da riga, a fuskarsa kuma yasaka k’asumba da saje sannan yasaka wata suma akansa, gaba d’aya dai yacanja,ita kanta badanda tasan dadyn taba da sam bazata iya shaidashi ba. Motocinda sukazo aciki yanzuma acikinsu suka shiga, kai tsaye hanyar abuja birnin tarayya suka kama kasancewar acan zasushiga flyt dinsu. Motarda bunayya take aciki ba ita dady yake cikiba. Yaranda dady yake tareda su sun matuk’ar sanin b’oyayyun hanyoyi nacikin daji, danhaka bakan titi sukabi ba, ta keta daji suke sosai suna tafiya sbd koina a tsaye yake,idanma sunka kai inda sukaga alamar akwai tsaro saisu kauce wannan hanyar subi wata.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34