Chapter 33
Chapter 33
momy da ahalinta sunyi b’arin kud’i kamar basusan zafinsuba,hakama bunayya da mashkur sunyi nasu rawar ganin, abban ramadan da hajiyarsu ma sunyi tasu rawar ganin bakad’anba, dik wani abu da uba keyiwa d’ansa abban ramadan yayisa hakama hajiyarsu tayi nata kokarin sosai. Kantama kantaman shanaye abban ramadan yasiyo domin a yankewa d’ansa konace d’an d’anuwansa. B’angaren ahalin momy kuwa hmm abun baacewa komai sai abunda ido yagani kawai. Had’addiyar maiyin lalle da saloon aka kira inda ta tsantsare momy hadda abar kaunarta bunayya, ranar momy tadawo sabuwar amarya kamar yarinya yar shekara ashirin bayan kuma tabama 40 baya, hakama bunayya mashkur yai santin gyaran da akamata dikda a waya yagansa sbd yakoma habuja. Washe gari ranar suna yaro yaci sunan kakansa mahaifin dady KABIR akamasa inkiya da khalifa, biki akayi nagani na fad’a wanda duniya tajisa takuma karad’e da lbrnsa, dik wani almajiri ko mai rauni yashaida da wannan bikin kai hatta masu kud’in sunshaida sbd wannan bikin bak’arami bane. Yaro yaga gata bakad’an ba, daga bisani bayan angama komai kowa yawatse, bunayya ma washe gari takoma school sbd tanada lecture babba. Dahaka dik bak’i suka watse akabar momy da yaronta khalifa. Bayan kimanin wata shida da bikin khalifa akai auren ruwaida da ya ramadan inda amarya ta tare a katafaren gidanta dake GRA NEPA birnin kebbi, to Alhmdllh masha Allah ubangiji yasanya alkhairi ibada zaman lfy ameen. Bayan kimanin wata biyar da auren ruwaida da ya ramadan kuma akayi na hamdallah da mahbub aminin mashkur lkcn cikin ruwaida na wata uku su bunayya kuma suna 400level suna gab da kammala karatinsu na degree a biochemistry. Saidai har yanzu babu lbrn ciki bare alamunsa agun bunayya,yanzukam abun yad’agamawa momy hankali sosai, nanfa akashiga neman magani da gwaje gwaje gun likitoci kuma a sibitoci kala kala,saidai koina akaje sai ace lkcne dai baiyiba amma dikansu lfynsu kalau, wannan ne dalilinda yasa hankalin bunayya bai tashiba har yanzu, damuwarta d’aya son yayanda mashkur keyi sosai, tinda aka yaye khalifa yaje yad’akkosa kokad’an bayasan yatafi sai idan yakoma habuja sai bunayya tamaidasa sbd itama school take. Itama abun harya fara damunta sbd yanda taga mashkur yake nunak’aunarsa ga yara,bama khalifa kadaiba dik yaga yara kamar yakwacesu yakeji musamman yanzu dabasuda k’ananan yara a gida dik sungirma. Ahaka ahaka harsu bunayya suka kammala karatinsu kuma Alhmdllh tafito da grade mai kyau, nantake momy tad’aurata akan k’asaitaccen business d’inta, tazaunarda ita takoyamata harkan business sosai,kankaceme bunayya tamafi momy kwarewa a harkan, itakanta momy har mamakin y’ar tata take, saidai awani b’angaren kuma gdy ga Allah take daya bata ita amatsayin y’a. Acikin wannan lkcn ne abban ramadan yazo yarok’i momy akan tai hkr amaida aurensu da dady, dafarko k’in amincewa tai saidaga baya dasu bunayya suka bakinsu sannan ta amince. Saidai tace bazata koma can gidansa ba ana gdanta zata zauna,dikda haka yace ya amince din, nan aka sake d’aura auren. Bunayya taji dadin hakan sosai hakama hajiyarsu dady tanuna farincikinta sosai. ................... Sannu ahankali bunayya tacigaba da gudanarda kasuwancin, acikin k’ankanen lkc bunayya tashahara tai fice acikin duniyar kasuwanci,saiyazama kowanne company naso yahad’a had’aka da companyn momy kokuma yasaka hanun jari a companyn. ................. Acikin yan shekaru bunayya tazama fitacciya kuma shahararriyar yar kasuwa wacca duniya tasanta kuma take fad’arta,abun harya shafi mijinta mashkur danshima alak’arsa da bunayya tasa yafarfad’o da kamfaninikan mahaifinsa, dikda yariga bunayya fara kasuwanci amma saiyazamo tafisa ilimi a harkan,dole yadurk’usamata yakwashi ilimin abun shima ya hab’baka. Momy batada damuwa koguda d’aya tana zaune zaazo akawomata balance na billions of money amatsayin ribar wata shida ko bakwai, ita tinima tadaina fita aiki saita mata dad’i, companynda suka bud’a ita da dady kowa tini tabarmasashi yayansa ke kula dashi su ya Amir sbd shikam lafiya tamasa zarra, yanzuma da k’afar k’arfe yake tafiya da sandar k’arfe yake dogarawa, shys yanzu sam baya fita koina. Dikda haka bunayya batabarsu ya amir hakaba, suma tasakasu acikin business din, hakama ya ramadan domin sabon companynda tagina a USA shine manager acan yanzu hakama yanacan tareda uwar gidansa ruwaida da yaransu biyu sultan da sultana. Alhmdllh albarka sai dad’a shigowa take acikin ahalin, saidai har yanzu matsala daya suke fuskanta wacca take damunsu itace rashin haihuwar bunayya, hajiyarsu dady kowa tace tarihine yake maimaita kansa, saidai sukam su bunayya yanzu sunbarma Allah ikonsa tindadai an tabbatarmasu da dikansu lafiyarsu k’alau kawai lkcne baiyiba. Danhaka sukabarwa Allah ikonsa sukacigaba da rayuwarsu,momy tai kuka sosai harta godewa Allah, daga bisani itama tabarwa Allah ikonsa. bunayya tad’akko sultan d’ansu ruwaida suka maidashi gunsu suna rayuwarsu cikeda farinciki dajin dadi. ..................... After 5yrs...... Rayuwa tacigaba da tafiya cikin farinciki walwala dakuma jin dad’i, kimanin shekara goma kenan da auren bunayya da mashkur. Wata ranar Monday ce bunayya ta tashi batajin dad’i amma batawani damuba tasha magani, yawan jiri da kasala da yawan bacci keta faman damunta kullum saitasha maganin zazzab’i taji sauki washe gari kuma ysake dawowa. Ahaka ahaka harta kashe kwana sati d’aya tana fama amma bata sanarda mashkur ba, dikta zauna saitaita kallon kanta da jikinta yanda tacanja a kwana biyun nan,dikda ita farace amma wannan hasken datai yabata mamaki ga bobbs d’inta sai kara ciccikowa suke gashi kowa yaganta saiyai magana wai sai shining take, aa abun sai mamaki yake bata itadama take fama da zazzab’i kwana biyu kuma zaace tai kiba tana shining. Ahakadai harta kwashe wata d’aya sai wataranar Thursday da maraice zazzab’i mai k’arfi yarufeta,amai taketayi kamar zata amayarda abunda ke cikinta. A haukace takira mashkur yadawo gida yakwasheta sukai hospital. Tin a gwajin farko ya tabbatarda ciki wata biyu, kamindai result yafito suka doramata drip tareda alluran bacci, sai awashe gari sannan aka kawo result. Kallo d’aya mashkur yayiwa result din yak’aryata abunda ke rubuce akanta, saida doctor yacemasa “of course Mr mashkur abunda kagani is true gsky ne” sannafa ya yarda ya durk’usa yai sujudul shukru yarungume Doctor cikin tsintsar farinciki sannan yayiwa doctorn kyautar mak’udan kudi da galleliyar mota, doctor yaita gdy yaita gdy. Nantake mashkur yafara kiran mutane yana fadamasu, nantake hospital din tacika da mutane masoya yan uwa dakuma abokanan arziki, da bunayya tafarka kunya takamata dan haddasu momyn mashkur sunzo dayake suma sunzo yola ne yin wani aikin companyn dake yolar natsawon wata uku kamin sukoma habuja kuma. Kankaceme lbrn cikin bunayya yakarade koina kowa sai kiran mashkur yake yana tayasa murna da farinciki. Bayan kwana biyu aka sallamesu suka koma gida akacigaba da rainon cikin acan. Kulawa tamusamman akebama bunayya da abunda ke cikinta, mashkur kokad’an bayasan tai wani aikin koda d’auke plate dinda taci abinci ne, yak’ara k’aro mata ma’aikata sunkai shida sbd kawai akulamasa da baby’s dinsa sbd tini akai scanning dayakai 7-8months aka gano twins ne mace da namiji. Yanzu bunayya tadaina fita aiki tinda cikin yakai 6-7months ya ramadan ne yacanjeta harta haihu. ................ Ahaka ahaka har cikin yakai 9months akafara shirye shiryen tarban haihuwa,kankaceme komai na buk’ata na haihuwa mashkur yasiya tindaga na yaran harna mamansu, saidai cikin haryawuce 9months amma ba’a haihuba gakuma cikin yagirma sosai yai k’ato yanakuma wahalda bunayya sosai tagaji dashi tamatsu bata rabudashiba tahuta. Ranarda dik yacika 10months cif ranar bunayya ta tashi da wata wahaltacciyar nak’uda, tin tana jurewa harta kasa gashi mashkur yafita,ahaka taita murkususu itakad’ai acikin parlor tad’auka zata iya jurewa hartakai kusan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34