Chapter 12
Chapter 12
suma har sungama,gdy yawa yarinyar data zauna mata,hamdallah ma suna fitowa tashirya tafice asibitin,shima daganan can yafice,koda yaje harsu dadyn bunayya sun isa,momynta nakusa daita ta rungumeta tana bata tea. Ahankali yashiga yagaidasu dady suka amsa cikin sakin fuska sannan yadubeta yacemata “sannu Fatima, yah jikin” ahankali tadaga masa kai tareda fadin “naji sauki” police dinda suka shigone sukamawa su dady bayanin saurayin shine yataimaki bunayya,badandashi ba daba’asan inda wannan lamarin zai tsayaba,amma yanzu Alhmdllh ankama sauran yaran suma yanzu haka sunacan a tsare. Gdy sosai su dady sukamasa tareda tambayar sunansa yace “MASHKUR” cikin faraa. Bunayya kowa sai kallonsa takeyi cikin tsintsar mamaki, suna nan hamdallah tazo tareda sauran corse mate dinsu. .................. Tsawon kwana uku bunayya tad’auka a hospital din kamin asallameta,a d’an zamanda tai sannu ahankali harta fara sabawa da mashkur, tasake masa fuska sosai tamkar d’an uwanta najini. Kullum idan zaizo saiyayomata cike ciken kayan mak’u lashe waenda yasan tafiso. Sannan shike sakata agaba tasha magani,haka idan za’amata allura saiyai tsaye sannan zata tsaya amatasu. Dasuka koma school ma baidaina kula daitaba fiye da kularda iyayenta kebata sbd yafisu kusanci daita a yanzu tinda shi gashi gata, hakan ne yak’ara janyo kusanci tsakaninsa daita dakuma iyayenta sbd sunajin dadin yanda yake kula daita. Sannu ahankali har shak’uwa mai k’arfi tashiga tsakaninsu batareda sunsaniba, bawanda zai iya wuni d’aya batareda yaga d’ayansa ba, yanzu har yaya da k’anwa ake kiransu. Manage it pls...👏love u all my fam.💋💔 #/Comment nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI...._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _19/20...._ Sannu ahankali shak’uwa da kusanci sukacigaba da shiga tsakanin mashkur da bunayya, har yanxu baidaina kula daita ba dakuma yimata yan nasihohi akan takare martabarta ta y’a mace, Alhmdllh kuma tanajin maganarsa sosai sbd ayanzu jinsa take kamar d’an uwanta najini. Idan baiganta wajen karatuba kokuma masjid kokuma restaurant tosaiya nemi hamdallah yatambayeta ina take, nan hamdallah zata fadamasa, haka itama idan tai kwana biyu bata gansaba dakanta take zowa nemansa agun abokanansa jalal da majnun. Suna acikin wannan yanayin har suka kammala zana jarabawa sukai Hutu. Kokad’an bunayya bataji dadin hutun ba sbd yanda tafara shak’uwa da sabon brother d’inta. Bata ankaraba damuwar rashin ganinsa kwana biyu tafara kusantota, saitaji batasan zama acikin mutane any time tana d’aki itakada’ai tana tinanin brother d’inta, gashi tai ragon tinani batada ko number dinsa hakama dik abokanansa bawanda takeda number dinshi bare takira tace a turomata. Haka taita fama da kewarsa dakuma damuwarta har momy ta fahimci tanada damuwa,amma data tambayeta saitace bakomai gajiya ce kawai ke damunta, saidai momy kam bata yardaba sbd taga tarin canji agun bunayya. Yau takasance Monday itakad’aice a gida momy da dady dik sunfita office,yanzu tariga tasaba da hayaniya sam bata iya zama itakad’ai,danhaka tashirya tadauki motarta tafice gidansu hajiyar dady, acan tawuni sai dare sannan tadawo. Haka tadingayi kullum har tai sati daya da dawowa school,kuma tanajin dadin zowanta sbd koba komai tana rage kad’aici da tinane tinanen brother d’inta mashkur. Yau takasance Saturday danhaka su dady nagida kowama yana gida tinda weekend ne, dady da ya Amir suna waje bakin lambu sunashan iska,itakuma bunayya da momy suna cikin gida a parlor hadimai kuma kowanne yana aikinsa. Zaune kawai take amma gaba d’aya ruhunta da zuciyarta basa a gangar jikinta,ta lula tai nisa sosai acikin duniyar tinanin MASHKUR, itafa sai yanzuma take hango tsintsar kyanda yakeda harma take ganin dik kyanda ake fadar tanadashi gani take kamar mashkur yafita, komai nasa is accurate from face to his foot, mashkur irinsane yammata ke mafalkin samu arayuwarsu, kai auren irinsama fitinane wlh sbd yammata bazasu barka kai yanda kakeso dashiba. Wani dan murmushi tai wanda batamasan tayisaba lkcnda tatino da bakinsa mai d’aukeda pink lips sadda tayanke da wuka tayakaita clinic ana dressing din wajen tana kuka shikuma yanamata wasa yana tsokanarta dikdan tabari ayi dressing din agama. Itakanta tasan yana matuk’ar shagwab’ata tamkar yayanta na gaskiya. Tanacikin tinanin batasan momy nakirantaba har saida ta tab’ata sannan tai firgigit tadawo hayyacinta, momy tace “what’s wrong with u bunayya....are u okay, me kike tinanine haka bunayya inata kiranki amma bamakya jina” murmushi tai tareda rufe fuskarta cikin yanayin kunya,karo nafarko kenan data farajin kunyar mahaifiyar tata tace “am okay mom...bakomai” momy ta tab’e baki tareda fadin “idan tai wari maji” saitai dariya momy tace. “Kije dadyn ki yana nemanki a waje” ohk tafada tareda mik’ewa tafice. Ahankali take tafiya izowa lambu, sanye take da wandan jeans blue iya guiwa da riga mai gajeren hanu pink, kanta yar hulace akai. Tindaga nesa tahango mutum durk’ushe a kusa da dady suna magana saidai bata hango fuskarsaba bayansa ne kawai take hangowa. Tana isa saitace “dady...” saiya kalleta cikin murmushi yace “mashkur ne yazo yanzu” saida gabanta yafad’i dataji sunan mashkur. A fili tamaimaita mashkur cikin tsintsar mamaki, mik’ewa yai tsaye yana dan murmushi,waro dara daran idanuwanta tai cikin tsintsar mamaki tareda rufe bakinta lkcnda sukai ido biyu. Dakyar taiya cemasa “Mashkur sannu da zowa” sbd tsananin mamaki, cikin murmushi yace “yawwa Fatima, yah kike” tace “lfy klw “ dady ya mik’ewa a tsaye suka fice izowa cikin gida itakowa dagudu tafice bedroom d’inta tana cewa momynta “momy ga mashkur nan yazo”. Itama momy mamaki tai sosai tace “mashkur fa, wannan zowan bazata fa bako sanarwa”. A babban parlon dady suka fice inda aka cikashi da abinci kala kala da kayan fruits dana snacks kala kala, dady yasakashi dole saida sukaci abincin atare, bayan sungama sannan momy tashigo tareda bunayya. Cikin matuk’ar girmamawa yadurkusa yagaida momy itama ta amsa masa cikin faraa da sakin fuska, momy tace “gsky munji dadin wannan ziyarar taka sosai mashkur, Allah yamaka albarka kuma acigaba dayin hakan, tahakane zumunci zai dore” yai murmushi yanajin dadin yanda irin taryanda suka masa. Gogar kowa sai murmushi take tana satar kallonsa sbd yamatukar yin kyau sosai,shaddah ce gizna light blue ajikinsa d’inkin riga da wando da hula mai ratsin blue ajikinta, watch dinsa silver color dakuma zobon azurfa a hanunsa, kyan fuskarsa sai dad’a karuwa yakeyi yak’ara gyara sajensa hakama sumar kansa baka wulik sai shining take sbd tasha gyara. Cikin wayo da dabara tagama masa wannan kallon tsabtar,momy tafita hakama dady yayi side din momyn ammar,yarage subiyune kawai acikin parlon. Kallonta yai ahankali yace “yau kuma kunyata akeyi” saitai dariya tareda sadda kanta k’asa batareda tace komaiba, cigaba yai da magana “nasan kinyi mamakin ganinako” saitace “sosai makowa, am very surprised” saiyai murmushi. “Toh ba abun mamaki bane agareni sbd nakasa hakura da rashin ganin ya k’anwarta nabiyota har gida domin naganta” dariya tai sannan tace “ai nad’auka ko nikad’aice nai missing dinka” waro idanuwansa yai yace “tabdi, ai namafiki yin missing d’inki” saitai murmushi kawai. Ahankali yadinga janta da fira sukaita firarsu, yad’an jima anan kamin daga bisani yamasu sallama yafice. Ranardai acikin farinciki bunayya takwana dan dare kuma saigashi yakirata sukaita shan firarsu, tindaga lkcn basu sakeyin koda wuni daya bane batareda sunsan halinda junansu suke aciki ba. Sannu ahankali shak’uwarsu tagaiga dik familyn mashkur bawanda baisan lbrn bunayya ba kuma yakesan yaga bunayya da ido, haka itama bunayya dik gidansu kowa yasan da me d’inta kamar yanda take kiransa brother me,saidai shikam har fuskarsa an sani sbd harsu hajiya yaje yagaidasu. Ahankali har hutunsu bunayya yakare suka koma school suka cigaba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34