Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,241 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da karatu. Ahalin yanzu Mashkur da bunayya sunzama aminan juna waenda suke fadawa junansu sirrinsu,tini mashkur yai bincike akan bunayya batareda tasaniba,a yanzu yasan wacece ita haka kuma yasan dikkannin halayenta dakuma d’abiunta. Yana matuk’ar kula daita tamkar k’anwarsa ta jini,yai amfani da k’arfin amintakarsu wajen canjawa bunayya d’abiunta na jajayen fata,kamar saka k’ananun kaya,yawo ba mayafi ko hijab,dakuma saka karatin addini agaba kamar yanda tasaka na zamani, yanzu a MSSS tana d’aya daga cikin shuwagabanni na school din, kai saida takai takawoma aka bata muk’amin AMIRAH dama mashkur shine AMIR shike bada sallah amasallacin school din. A yanzu gaba d’aya bunayya tacanja,a yanda kasanta da yanzu idan kaganta sam bazakace ita bace, a kullum tana cikin jallabiya tai rolling da veal saita rufe koina nata inda ake gani sannan zatajita daidai. Dakansa yakaita kasuwa yasiyomata atampopi da riguna masu kyau dogaye da jallabiyoyi da hijabs kala kala, sannan yakaita gun telo akamata dinkuna sannan yasaka aka koyamata saka kaya atampa dakuma d’aura zani, a yanzukam tadawo cikekkar hausa fulaninta. ................... Dadyn bunayya yafara damuwa da yanda bunayya ta shak’u da mashkur gashi har yan gidansu sunsan mashkur har suna maganarsa,babban tashin hankalinsa shine,yanda yaji hajiyarsu tace wai tabama mashkur dama idan har son bunayya yake da aure to yai gaugawar turo magabatansa sbd yanzu takai munzalin aure. Dikda baiji amsarda mashkur din yabadaba amma yana cikin matuk’ar tashin hankali,gashi yatabbatar da cewa mashkur da bunayya suna son junansu. Babban kuskurensa shine,daya bari har mashkur yarab’i bunayya har suka shaku da juna haka,to yanzu miye mafita...? wannan itace tambayarda yakemawa kansa wacca yake neman amsarta. Acikin yan kwanakin nan gaba daya acikin tashin hankali da tarin damuwa yake, tin yana b’oyewa har momy tafahimta wanda har saida takaiga tambayarsa meke damunsa yace bkmi. ..................... Kamar kullum yauma zaune suke a restaurant sunacin abinci, bunayya hamdallah dakuma mashkur, suna cikin ci sai aka kira hamdallah a waya ta tashi domin amsawa. Mashkur yadubi bunayya yace “bunayya mai kama dakefa ta dameni akan saina kawo masu ke sunganki, haka kuma nafada maki momy na tanaso taganki,bama sukad’ai ba dik yan gidanmu bawanda bayaso yaganki sbd jin labarinki dasukeyi a bakina,sbd haka yanzukam yadace ace ki amince muje koda wuni daya ne saimu dawo koh, dan Allah please....! haba yar k’anwata” murmushi tai ganin yanda yaketa mata magiya gashi tasani yai kanwa uku ko hudu daita tinda yanzuma degree na biyu yakeyi anan wato masters degree. Cikin shagwab’a tace “nidai bazaniba,salon naje suce banida kyau kafini kyau” waro idanuwansa yai yasake baki har saida tai dariyarsa sbd yanda yai abun yace “ni...rufamin asiri yar k’anwata,idan inada irin kyanki ai sainai yanga kamin nazab’a mata”. Hararansa tai tace “to yanzinma mekakeyi banda yangar, yan 200level da yan 300level nawane keyoman shopping dik dan nace ka amince kasosu,shekaranjiyar nan aunty badiya tasiyoman sweets da chocolate kuma kasani,kawai kaidai bakatashi bane saikagama yanga, kokuma ni saina gaji da wannan yangar taka nazab’ama dakaina ba” takarisa tana hararansa. Dariya yakeyi yakai hanunsa yaja doogon hancinta tai yar k’ara tareda yin kukan shagwaba,aikwa nan yashiga rarrashinta,saidayadinga bata abinci dakansa abaki sannan tahakura, yana dariya yace “my yar shagwabana kin amince zakije kigasu ruwaida koh...?”. Gyada masa kai tai alamar eh sai yai murmushi tareda fadin “dik ranarda mukaje sainabaki wani surprise mai girma,zan sanardake wani sirri wanda tsawon shekaru bakisanshi ba” kallonsa tai cikin rashin fahimta saiyai murmushi kawai batareda yasake cewa komaiba. Bayan sungama sannan suka tattara suka koma school. #/Comment nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _21/22...._ Tin ranarda sukai maganar zuwa gidansu mashkur yaketa shirye shiryen tafiyar, itakam gogar indama akai zancen anan tabarsa tama share zancen sbd batawani d’aukesa serious ba. Zaune take abakin room d’inta tana gyaran k’umbarta saiga hamdallah tazo,wata leda tamik’a mata ta amsa sannan tace “da me yana nemanki pa tin d’azun,yana nan abakin get” ohk...kawai tafada sannan tamike tashiga ciki, Wani k’aton hijab tad’akko tasaka kasancewar towel ne ajikinta sannan tasaka takalmanta tadauki wayarta tafice. A jingine da bangon gini ta taddasa tarungume hannayensa, yana ganinta saiya gyara tsayuwarsa,bayan taiso cikin faraa tace “da me...yadai” cikin murmushi yace “batun tafiyarmune,shine nace bara natinamaki yaune fa” waro idanuwanta tai alamar mamaki sannan tace “yaufa...?” yace “Eh...” hmm...tasauke numfashi tareda dan b’ata fuska sannan tace. “Ni gsky banshirya tafiya yauba” hararanta yai kamin yace “sbd me” ta tab’e baki tace “haka kawai” saiyace “indai bakida wani dalili to ba’abunda zaihana tafiyarnan yau,tinda dai naga alamar bakyasan zowa bayan nafad’amaki hadda momy na tace tanaso taganki”. Murmushi tai tareda dan rufe fuskarta da tafin hanunta daya sannan tace “am sorry,bahaka bane wlh” saiyace “to yane idan bahaka bane” gyara tsayuwarta tai sannan tace “Is okay, shkn na amince muje yaud’in” murmushi yai sannan yace “haba kokefa my happiness” dasauri takallesa sbd kalmarda taji yafada shikwa baiko damuba yajuya yad’akko wata leda yamika mata yace. “Kisaka waennan kayan zasufi maki kyau” ahankali takarba sannan yajuya,har yai nisa saikuma yad’an waigo yace “nabaki 15mnts kishirya” saita juya tana murmushi. Tana dawowa kowa ba b’ata lkc tashirya tsab cikin kayanda yakawomata, sket da riga ne nawata tsadajjiyar atamfa red white and black color mai shegen kyau da tsada,mayafi red color, kayan sunkamata sosai kuma sunmata kyau matuk’a, matasan zamanta sunfito dakyau hakama dukiyar fulaninta har suntaso sama sbd cikarsu tubarakallah masha Allah, fuskarta saida hamdallah tazauna tatsara mata make-up sbd tasan halinta ba make-up zatayiba. Wata tsadajjiyar sarkanta na gold da yan kunne da zobe dakuma awarwaro tasaka waenda dady yabata kyauta lkcnda yadawo daga Dubai, takalmanta ma red color ne hils masu kyau, tai kyau matuk’a kamar kasaceta ka gudu sbd tsananin kyanda tai, ba namijiba ko mace taganta dole taji kishi. Saida yakirata sannan tafito hamdallah tarakota, tinda yahangota yafara kallonta yana wani killer smile yana kare mata kallo har saida takariso kusa dashi, cikin murmushi yace “gsky gsky zaniya rantsewa da Allah ince bantab’a ganin kinyi irin wannan kwalliyar da wannan kyanba, hamdallah kodai wannan aikin kine...?” yafada yana kallon hamdallah cikin tsokana. Dariya hamdallah tai sannan tace “aa nadai d’an taimakane kawai” saiyace “aahh...tinda akace taimako nasan kece kikayi wannan aikin, toga wannan sbd kada kiyi wahalan banza” saiya mika mata kudi masu tsoka yasake cewa “amma dai yakamata kidage ki koyawa k’awarki gsky ko Allah zaisa afara banbanceta da namiji” hamdallah na dariya tamasa gdy tareda fatan sauka lfy yashiga mota yana amsawa. Gogar kowa tacika fam harta shige mota tini takame kujerar baya tashige,batama yiwa hamdallah bye bye ba sai itace taketa mata tana dariyarta, shima harya shiga motar dan murmushin b’oye na tsokana yakeyi harya tada motar yabar school din,saidai yana kallonta ta madubin dake kusa dashi. Harsun hau kan titi saiya faka motar sannan yafito yabud’e mata kofa yace “madam kifito kikoma seat din gaba sbd gsky ni ba driver bane” ko kallonsa bataiba saima murguda masa baki datake, dariya kaman ta kashesa amma yadake yasake cewa “nifa ba driver bane madam” kallonsa tai ta harerasa tace “bazanyiba,gwandama katada motar mutafi dan bazan fitabaf...” batako rufe bakintaba yaduko yad’auketa cak. Fizge fizge tafarayi tana fadin “bazanjeba kasaukeni ni komawa zanyi school bazanjeba ma” bude murfin kofar yai yasakata sannan yamayar yarufe sannan yajuya dayan side din yashiga yatada motar suka fice.

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});