Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,262 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tsawon sati d’aya,itakuma bunayya gashi basu kammala exam ba. Dahaka aunty kuluwa tahak’ura har suka kammala exam din sannan tadawo gida dikta rame. ...................... Kamar koyaushe momy ce zaune akatafaren parlon ta tanashan fruits tana kallon news a aljazeerah channel, bunayya kowa kwance take akan center carpet tanacin tufa,sanye take da kayan bacci riga da wando iya guiwa,kanta bakomai sumarta dikta barbaje akan pillow dinda kanta yake akai. Ahankali momy takalleta tace “waikekam bakya shirin komaine,naga bakima damuba matsayinki na amarya” wata iriyar kunyace taji takama saitai d’an murmushi murya k’asa kasa tace “toni wane shirin zanyi ne bayan wanda ku kukeyi” waro ido momy tai tace “lallai yarinyar nan,amaryace zatace wane shiri zatayi na bikinta,koda yake bazanga lefinki ba tinda bashiga mutane kikeba bare kisan yanda akeyi” saitace “to kingani,nikam ina nasan shirinda akeyi”. Momy tasake cewa “to batun k’awayenki fa,su wayene zasumaki k’awayen amarya ne?” d’an tinani tafarayi sannan tace “kingadai hamdallah itace babba saikuma nabila da nafisat kannen ya ramadan,to saikuma su rufaida da rumaida yayan uncle Muhammad, sukenan sun isa” momy tace “shkn,akwai five hundred thousand naira zan baki dik abunda suka fad’amaki yakamata kuyi saiku diba kuyi,uncle Muhammad ma ya aikomaki da two hundred thousand yace abaki,saikuma k’awata hajiya mamu ta yobe ta aikoman da fifteen thousand naira gudumawa,anfa turoman da kudi sosai gudumawa anjima idan mun zauna dik zan fad’amaki insha Allah” murmushi tai na farinciki da jin dad’i tace ok kawai. Cigaba ake da shirye shiryen shagali ta koina b’angarorin hud’u,momy tazage sai faman kashe kud’i take domin ganin tayiwa y’arta tilo gomasha na arziki. Bayan kwana hud’u da dawowar bunayya abban ramadan yazo yabama momy hkr akan dan Allah tashirya taje tabama hajiyarsu hkr ita da bunayya sbd yanaso yazamana koda za’amayarda magana wata rana yazamana batada lefi,kuma yanaso ad’aura auren bunayya anan gidansu dady amatsayinta na y’ar dady. Momy dafarko taso tak’i amincewa da buk’atarsa amma daga baya data tino da martabar y’arta bunayya ma zata k’aruwa idan har aka d’aura aurenta anan gidansu dady saita hkr tabama zuciyarta hkr ta amince zataje d’in. Washe gari kowa tashirya tareda bunayya da driver sukaje gidan,fuskar hjy ba yabo ba fallasa ta taryesu abun harya bama momy mamaki yanda taga tasake masu fuska hadda tambayar bunayya ya karatinta tace Alhmdllh. Batareda b’ata lkcba momy tagabatarda abunda yakawosu nan ta durk’usa agaban hajiya dikda d’an matashin cikinta amma bata damuba tashiga bama hajiya hkr akan abunda yafaru, abun mamaki saiga hajiya tana fadin “bakomai ai sharrin shaid’an ne,Allah iyafemana baki d’ai kuma a kula da yanayin jiki sbd kare lfyr abunda ke ciki” cikin yanayin sakin fuska momy tace toh taredayin gdy. Basu wani dadeba suka koma side din hajiyarsu ya ramadan,hajiya taji dadi sosai da yanda hajiyarsu dady tahak’ura,haka shima abban ramadan yaji dad’in abunda momy tayi har yaita mata gdy sosai tareda addu’ar fatan Allah yak’ara nisantarda shaidan atsakaninsu. Ranar kusan gidan suka wuni sai kusan la’asar sannan suka koma gida,bunayya tahad’e dasu nafisa akaita yawo ana zumunci anakuma firar yaushe gamo. Labarin auren bunayya da mashkur yarizk’e dady a bazata,wani abokinsa ne yakirasa yana zaune a office yana signing kan wasu files,cikin rashin jin dad’i abokin nasa kemasa magana “haba kadel,yanzu amintakarda ke tsakaninmu tacancanci ace katashi aurarda y’arka har ana saura yan kwanaki amma baka sanardamu ba,wlh kabani mamaki Alhj kadel” dasauri dady ya mik’ewa tsaye tareda dakata yin signing din. Mamaki ne yabayyana a fuskarsa sosai amma saiya b’oye yacemasa “Am...am....dan Allah Alhj zayyad kayi hkr,abubuwane sukayi yawa shys banturo maku da invitation card ba,but....am very sorry please...!” sai mutumin yace “Ok....no problem,Allah isanya alkhairi” yace ameen sannan sukai sallama. Dady yakasa zaune yakasa tsaye acikin office din,daga k’arshema saiya fice daga office d’in kawai. Kimanin sati d’aya yarage afara gudanarda shagalin bikin,gida yafara cika da bak’i na nesa dana kusa,hajiyarsu dady ta aiko aka d’aukarmata bunayya aka kaimata,saida tai kwana biyu acan tana mata nasu gyaran na tsofaffi sannan aka maida,washe gari kuma tafice bagudo gun aunty kuluwa domin afaramata gyaran amare. Su ruwaida sun iso tareda ramlat kanwar mashkur hakama nadiya k’awar bunayya ta London tazo tareda momynta da nabil kanenta,hamdallah tazo tareda bunayya suka tafi bagudo,kai mutanedai sai zowa suke daga k’asashe daban daban dakuma garuruwa daban daban. Bayan tafiyar bunayya dakusan 9hrs saiga kiran aunty kuluwa yashigo wayar momy,bayan tad’aga tana batun tafara magana sai aunty kuluwa tafara da cewa “wai jolde me bunayya ke nufine,wlh kifad’amata idan yaturo a d’auketa bazataji da dad’i ba,haba dan Allah,wannan wane irin iskanci ne tin yaushe matar nan kejiranta afara abun nan amma har yanzu tak’i tazo” mamakine ya bayyana a fuskar momy kamin tace “banganeba aunty, bunayya fa tin 9am sukabar birnin kebbi zowa nan bagudo,yanzu kuma kusan 9hrs kenan da tafiyarsu amma ace har yanzu basu isoba” itama aunty kuluwa mamakin ne yabayyana a fuskarta tace “tin 9am sukabaro birnin kebbi fa kikace” tace “Eh wlh,amma bara nakirata naji” tace toh sannan takatse layin. Nan tashiga kiran layukan bunayya amma dik akashe suke,dasauri takira layin hamdallah sai wani namiji yad’aga,dasauri momy tace “hel...hel...helo hamdallah” sai yace “baita bace Malala,ni sunana Inspecter faruk,muntsi yaran nan ne a kan titi su biyu dika a some a yanzu haka suna babban asibitin FMC dake cikin birnin kebbi l/gvmnt,sbd haka kuyi hanzari kuzo” dasauri kwallah nazubomata tace “amma inspecter su uku ne had’i da driver ina d’ayan” saiyace “to mudai su biyu muka gani mace da namiji” ai dasauri momy tace “ohk...gamunan zowa” sannan takashe. Dasauri takira aunty kuluwa tafadamata sannan tafada anan cikin gida halinda ake ciki. Dasauri aka cika mota uku aka fice FMC,koda akaje hamdallah da driver ne babu bunayya,wani jiri yad’ibi momy tai baya zata fadi dasauri aka rik’eta, Alhmdllh hamdallah ce bataji rauniba amma driver kam yaji rauni sosai har yanzu bai farkaba,hamdallah ce tadinga bayanin yanda abun yafaru. Suna cikin tafiya saiga wasu motoci guda hudu sun sha gabansu,nan wasu mutane suka fito aciki sukazo fuskokinsu rufe suka kama bunayya zasu tafi daita, nan driver yaje yariketa yace bainda zasuje daita,nan suka suka shiga dukansa har saida yafad’i suma sannan suka harbesa da bindiga ak’afa sbd yadage bazasu tafi da bunayya ba,harbin ne yasa yasuma sannan suka fice daita”. Momy dafe kanta tai tashiga karanto “innalillahi wainna ilaihi rajiun” sannan tafashe da kuka, kankaceme lbr yabaza gari ansace amarya bunayya y’ar shahararren d’an kasuwan nan dakuma shahararriyar yar kasuwar nan. Gida momy suka dawo tana zaune tadafe kai kuka kawai takeyi uncle Muhammad dasu uncle Aminullah da dai sauran yan uwanta suna zagaye daita, uncle Muhammad sai faman zarya yake acikin parlon, kwatsam saiga sak’o yashigo wayar momy ta email d’inta, kamar karta duba saikuma tad’akko wayar tabud’e tafara karantawa kamar haka “maryam....kina tinanin b’oye kanki da b’oyeman mata dakikayi shine zaihanani mallakarta amatsayin matata,to wlh kisani aurena da bunayya tamkar rubutune akan dutse bamakawa sai anyishi, kuma kisani ko kinaso ko bakyaso saina saka bunayya tazama kishiyarki,inaso kisani ayanzu haka bunayya tana hanuna kuma kifad’awa wannan d’an uwan naki dayace zai aurawa mashkur bunayya idan har yaisa yana tak’ama naira da k’arfin iko yazo yahanani auren bunayya” Dasauri tamike a tsaye tareda nunawa su uncle Muhammad tacigaba da karantawa a bayyane “Maryam.....kisani inama bunayya soyayyarda bantab’a yiwa wata y’a maceba ciki kowa hadda

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});