Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,218 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tana kyalli tamkar hasken farinwata a sararin samaniya ranar daren 17. Tsaye tai tana kallon kanta a mirror saitai d’an murmushi wanda bansan ma’anarsa ba. Ahankali taje tad’akko takalmanta hills pink masu kyau tasaka, bayan tasaka sannan tafeshe jikinta da tirare dan bunayya kwaita dasan k’amshi sosai. Bayan tagama sannan tad’akko wata yar jakar hanu itama pink color ce tasaka wayarta aciki sannan tafita. Kai tsaye bedroom din momyn ta tafice, koda taje tana sallah danhaka tatsaya tajira harta k’arisa, bayan tagama saitace “please....! momy borrow me your car” kallonta tai sama da k’asa sannan tai murmushi tace “where are u going bunayya...?” itama D’an murmushin tai tace “am just going to birthday party na jasmine, I think bazanma dad’e ba bcoz....tai inviting samari dayawa, so nikuma I don’t like hakan tasani itama” momy batasake cewa komaiba. Dahanu tamata nuni da key car din tad’auka tareda ficewa. Hmm...lkcnda naga tafito da motarda zata fita daita tsaye nai nawage baki da ido da hanci ina kallo sbd tsabar had’uwarta, haka tafigi motar dak’arfi tafice. Koda taisa kowa Wurin yacika sosai fam da y’ammata da samari, fiye da rabin wurin yayanmu ne na africa, some karatune yakaisu some kuma tareda iyayensu suke kamar bunayya. Tin 8:30pm aka fara party din amma ance sai 12pm za’agama, itakam 10:30pm dot tabar wurin takoma gida abunta, koda takoma dik a gajiye take danhaka wanka kawai tai tabi lafiyan gado. Washe gari ma lettin tashi tai dan sai 7:30am ta tashi, aikwa dagudu tafada toilet tai wanka tafito tafara shirin school, dasauri harta gama ta d’auki school bag dinta tafice, yaukam bata tsaya yin break ba tafice. Kimanin kwana hud’u dady yai a London sannan yadawo, aikwa koda yadawo daga momy har y’ar tata sunyi matuk’ar yin missing dinsa haka shima, kamar yanda yake al’ada agunsa dik yaje idan zaidawo saiyayowa abar k’aunarsa tsaraba, to yanxuma hakan take. Hakan wasu english wears ne yasiyo mata masu kyau kala kala kasancewar tafisan wandina shys yafi siyomata su, zan iya cemaku Alhj kadel shine wanda yake bama bunayya gudumawa wajen tasaka kaya irin na arna, wai acewarsa haka yanayin k’asarda suke yake ai idan sunkoma gida Nigeria zata bar sakasu, hmm. Shys tinda taso har izowa yanzu batasan saka kayan yarenta ba batamasan miye atampa ba sbd itama mahaifiyarta ba sakawa takeba, haka dik wata mace yar asalin Nigeria datazo kasar bawacca kesaka kayan hausawa ko yarenta saidai English wears hakama yayan nasu suma. Yanxin ma wani tsingilallen wando ne ajikin bunayya girmansa iya cinya kai baima k’arisa rufe cinyoyinta ba, sai wata yar singlet fara mai gajeren hanu kanta sam ba mayafi ko d’ankwali, kai idan kaganta sam bazakace musilma bace kuma jinin musilmai. Kwonce take akan kujera tana assignment momynta na a k’asa a kishingid’e tanashan fruits, dady ne yashigo d’auke da wasu kayan a hanunsa,cikin murmushi yazauna yana fad’in “bunayya zomuga kayan nan ko zasu maki” dasauri tamike tsaye tana dariyar murna taxo agabanshi tatsaya. Wani wando ne yad’akko yad’ora a k’ugunta wanda shima girmansa iya cinyoyinta ne, cikin faraa tace “ai xaiyi dady kagama irin najikinane” momy ma dake k’asa tace “zaimata ai, kasan halin k’ugun nata sai a hankali” dariya sukai sudika dady yace. “Bakomai,munji dai inkin isa kiyi kamarsa” tai dariya tace “nikam mema zanyi dashi yanzu nida na tsufa” bunayya tace “laaa....kai momy ina tsufa yake anan, wlh yanxu haka class mates dina cewa suke wai ke yayata ce ba momy na ba” daga momy har dady dariya suka kwashe daita. Bunayya kam tattara kayanta tai tafice d’akinta itama tana dariya, dady yace “sauran kayan suna a bedroom dina kije ki d’akko” toh tace sannan tafice. Washe gari takasance weekend danhaka kowa yana gida, kamar yanda suka saba weekend a gidan gonarda momy tasiya anan Australia sukeyinsa domin susha fruits kamar yanda suka d’aukarwa kansu shan fruits dik a weekend domin samun wani sinadari a gangar jikinsu. Danhaka tin 9am suka shirya suka tattara sudika a gidan hadda masu girki da shara da dai gyaran gidan, mota uku suka cika suka fice. Koda suka isa tini antsabtace gidan danhaka bawani wahala, Bunayya dai swimming pool tafice taita wankanta sukwa su momy garden suka fice domin shan fruits. Bayan bunayya tagama sannan taje tacanja kaya izowa wandan jeans bak’i girmansa iya guiwa da riga bak’a mai dogon hanu, bayan tashirya sannan tajegunsu momy. Da dare sunjima sosai sunashan fira kamar yanda suka saba, dady nabasu labarin yarintarsa shi da yan uwansa sai shan dariya suke hadda rik’e ciki, sai kusan 10pm sannan sukaje suka kwanta shima saida sukaga bunayya tai bacci dan dadyne ma yad’auketa yakaita bedroom d’inta sannan sukuma suka fice. Washe gari haka suka wuni cikin nishad’i acikin garden, sai 5pm sannan suka tattara suka koma gida. Haka farinciki da jin dad’i suke cigaba da gudana acikin wannan ahalin. Bunayya tacigaba da karatinta cikin walwala yayinda iyayenta kuma suke cigaba da gudanarda kasuwancinsu acan, yanzu abun harma yak’ara hab’aka dan sun fara ginin k’aton company a gida Nigeria mai d’aukeda tambarin sunan BUNAYYA, sunce sungaji da yawon k’asashen nan. Dady kuma yace yanaso yahad’a kan iyalinsa gu d’aya kodan shak’uwa tashiga tsakaninsu kuma susan danginsu dakyau,amma wannan na london wannan Australia tin tasowarsu har girmansu taya zasusan danginsu kuma suso junansu. Danhaka yamatsawa ma’aikatan ginin dasu matsawa aikin. Anahakan saiga wani business din yafito masu wanda zasu samu riba sosai acikinsa a London, danhaka suka tattara sukabar Australia suka koma London, saidai ba’a wuri d’aya suke dasu momyn ammar ba. Kokad’an bunayya bataji dadin dawowarsu London ba sbd yanda tashak’u matuka da friends dinta,takuma saba sosai da k’asar tanajin dadin kasar sosai, Bayanda taiya haka tacigaba da rayuwa a London inda izowa yanzu harsunyi wata biyu da dawowa harma tafara zowa school a sabon school dinda aka maidata yanzu. #/Vote nd’ Comment.. #/Aufana for life. [7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....*_🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _9/10....._ Rayuwa tacigaba da tafiya kamar yanda aka saba cikin farinciki da walwala. Kamar kullum yauma cikin sauri take shirinta nazowa school, saidai yaukam ta tashi batajin dad’in jikinta,ciwonta na mara yana nema ya tashi, danhaka yau sai a slow,bayan tagama sannan tafito dining room domin yin breakfast,almost 10mnts tab’ata kamin ta kammala break din sbd cin abinci bunayya fa saimai hkr, idan kana jiranta tafara cin abinci saikai hkr sbd bataci da sauri barema yanxu datakejin jikin nata. Bayan tagama sannan taje ta sumbaci momynta a kunce hakama dadyn nata kamar yanda yazama al’ada agaresu tareda masu bye bye sannan tafice. Har izowa yanzu takasa sabawa da sabuwar school dinsu gashi mararta sai faman ciwo take mata, abokiyar zamanta sai kallonta take yanda taketa faman murk’ususu amma takasa cemata komai sbd iyakacinta da bunayya hello hy shkn, gashi su biyune kadai akan kujerar kasancewar haka tsarin yake. Tausayin bunayya yacikata sosai ganin yanda takeshan fama, dakyar tasamu teacher dinsu yagama darasin yafita, yana fita tariko hanunta tareda fadin “fatima meke damunki ne, tashi muje clinic” sbd azabarda takesha yasa bataimata musuba ta tashi dakyar suka fice. Suna zowa a bayaninda tamawa nurse yasa tafahimci period dinta ne zaizo, danhaka tamata wani injection tabata magani tashi sannan tad’oramata drip, bayan angama sannan suka kira iyayenta. Hmm...zo kuga abun mamaki readers koda momy taiso school din hawaye faca faca

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});