Chapter 6
Chapter 6
a fuskarta harda gudunta sbd tasan yanayin ciwon nata gashi kuma tanada asma mummuna irinta dadyn ta, aikwa tana isowa tarungume bunayya dikda bacci take, saida taji kyakkyawan bayani agun nurse sannan takwantarda hankalinta amma da hartace zata d’auketa izowa big hospital. Zama tai anan har saida bunayya tafarka sannan hankalinta yakwanta dakyau, bunayya takalli yarinda takawota clinic din wato seatmate dinta tai murmushi sannan tace “thanks allot yar uwa,dikda bamusan junaba amma kin taimakeni” takalli momyn ta tace “momy kimata gdy itace takawoni wannan clinic din” itama momy ta kalleta cikin murmushi tace “sannu da kokari yata, Allah yasakamaki da alkhairi kinji kema Allah yataimakeki kamar yanda kika taimakemu”. Yarinyar murmushi tai tace “bakomai momy ai yiwa kaine, Allah dai yabaya lfy” tace “ameen” bunayya tace “yah sunanki ne hala” cikin faraa tace “Nadiya Abdussalam” cikin murmushi itama tace “Ok...nikuma fatima kadel kabir amma ana kirana da BUNAYYA” tai murmushi tace “nice to meet u bunayya” itama tace “nice to meet u too nadiya”. Momy kam kallonsu kawai take tanajin dadin sosai aranta abar k’aunarta tafara dawo da farincikin ta, sbd tinda suka dawo nan gaba daya walwalarta tagushe. Sai kusan 3:30pm sannan suka fice, har gida suka kai nadiya suka shiga sukamawa iyayenta gdy sosai sannan suka fice. Tin daga lokacin Nadaiya da Bunayya suka zama k’awaye gashi tasu tazo d’aya daita kusan halayensu d’aya dik barkatarsu iri d’aya ce, atare suke zowa party da dare hakama night club atare suke zowa gashi itama tanada tsintsar kyau sosai kamar bunayya saidai bunayya tafita hasken fata da cikar k’irji. ...................... Sannu ahankali karatin bunayya kecigaba da tafiya inda yanzu dika dika sati biyu kacal yarage sufara zana jarabawan karshe ta kammala secondary school dinsu. Danhaka yanzu a koda yaushe cikin karatu suke, gashi tini ankammala ginin company dakuma sabon kantamemen gidanda aka ginamasu wanda zasu zauna aciki idan sunkoma. Danhaka suma su dady shirin tafiya suke gida Nigeria acikin kwanan nan zasubar Bunayya a gidansu Nadiya harsu kammala exam dinsu sai dady yazo yadauketa su fice. Ranarda zasu fice kowa har airport su bunayya suka masu rakiya bayan jirginsu yadaga sannan suka kamo hanyar gida. Bunayya ke driving danhaka yanda taga dama haka take driving din, a maimakon su koma gida sai suka fice yawonsu wuraren shak’atawa da shan mak’u lashe, kowannensu sanye da wandan jeans da riga matsattsu dik surar jikinsu a bayyane take musamman bayansu, hips din bunayya kamar sutsaga wandan, sumarta da ribom daya ta tufketa. Sai kusan 7:30pm sannan suka koma gida, abunka da k’asar jajayen fata dakuma d’aukan rayuwar wasu mahaifiyar nadiya ko tambayarsu inda suka fito bataiba,a dole su sungirma sun mallaki hankalin kansu gasu kuma yayan gold yan ido ba’amasu fada baasan ba’asan b’acin ransu, itama nadiya su biyu ne agun iyayensu ita sai najib kanenta. Hakama suka b’ata dare sunata yin chart dinsu, nadiya tanada samari amma bunayya kam ko d’aya batada hasalima bata taba kula saurayi ko d’ayaba dikda kowa yanda samari keta mata rubibi amma taki bada had’in kai, hasalima haushinsu takeji. Sai 2am sannan nadiya ta kwanta bunayya kam tadad’e dayin bacci. Washe gari dasukaje school sai aka basu hutun sati daya domin suhuta kamin lkcn fara exam yai. Hakan bak’aramin dadi yamasuba dan dai ranar a club sukai dare sai 3am suka koma gida, dasuka koma ma shisha sukadinga sha har 4 basuma san sadda bacci yad’aukesu ba, Sai kusan 8am sannan suka farka. ................... Yau takasance Monday kuma itace ranarda zasu fara zana jarabawa, Danhaka 8am suka fice school sbd by 10 zasu shiga exam din. Sannu ahankali suka fara zana jarabawa cikin nasara, yau biyu kacal sukayi danhaka by 5pm suka koma gida, koda suka koma dik a hajiye suke danhaka wanka sukai suka canja kaya bunayya tasaka k’aramin wandan jeans girmansa iya cinya da riga wacca ko cibiyarta bata rufeba dan kana ganinta azahiri, nadiya kuma wata rigace tasaka girmanta iya cinya batama rufe cinyoyin dika ba. Sbd gajiya yasa basuyi batun fita ba,bayan sunci abinci sukai zamansu a parlor suna kallo da chart. Around 9 suka fita shan ice-cream,basu wani jimaba suka dawo gida. Haka suka cigaba da gudanarda rayuwar su yanda sukeso,yayinda kuma a b’angare d’aya suke cigaba da zana jarabawansu. Kimanin wata daya da sati daya suka kwashe suna zana jarabawan sannan suka kammala, ranarda suka kammala kowa hadda biki school din tamasu tareda basu kyautittika kala kala wanda bunayya ta amshi kusan uku,sunyi hotina kala kala da teachers dinsu dakuma principal dinsu da kuma sauran d’alibai yan uwansu. Daga bisani kowacce tai nata itakadai domin tarihi, bayan angama komai sannan kowa yawatse. Washe gari bunayya ta shirya kayanta izowa gida Nigeria kamar yanda iyayenta suka mata Izini. Tayi matuk’ar jin babu dad’i a lkcnda zata fice airport, dan ji tai kamar tafiyar har abada ce zatai, tareda iyayen nadiya suka tafi dakuma nadiyar da kanenta, lkcnda jirginsu zai d’aga ita kuka nadiya kuka haka suka rabu cikin kewar juna. 11am dot jirginsu yad’aga izowa gida Nigeria, k’asar haihuwa k’asar gado. #/Vote nd’ Comment #/Aufana for life. [7/22, 23:40] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI...._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _11/12......_ Almost 8hrs suka d’auka suna tafiya kasancewar jirgin yana tsayawa yana sauke fasinjoji a sauran k’asashe. 8pm....dot jirginsu yasauka babban birnin tarayya abuja,suna sauka takwaso kayanta taje tazauna tana jiran azo d’aukanta. Batafi 10mnts da zamaba saiga dank’ara dank’aran motoci sunyi parking agabanta,tana ganin hakan tasan cewa sune sukazo d’aukanta. Ahankali tamik’e a tsaye tana gyara rigarta data d’age saiga dady da momy da wasu maza uku da mata biyu sa’annin bunayya sunfito daga motocin,dasauri tawaro idanuwanta waje cikin farinciki kamin taje dasauri tarungume dadyn ta tana fadin “oyoyo dady me” shima dariya yake cikin tsintsar farinciki ya k’amkameta a jikinsa tareda sumbatarta yana fadin “welcome back to ur father land my happiness” tace “thanks my dady” sannan taje tarungume momyn ta tana fadin “I really miss u my mom” cikin tsintsar farinciki da k’aunar abar k’aunar tata tace “Miss u too my sweetheart, am so happy to see u nd’ am very appreciate to u, may God bless u, inafatar kindawo lfy”. Wani irin farinciki takeji daganin iyayen nata,juyawa tai izowa sauranda ke gefensu tace “su waye waennan momy..?” sai jolde tace “au...am sorry waennan matan Aysha and fadila mak’otanmu ne anan kuma yayan k’awayena ne, sa’anninki ne dika” saitai murmushi tareda basu hanu suka gaisa cikin sakin fuska. Saita sake waigowa agun mazan tace “waennan kuma cousins dinki ne waenda ke karatu anan” suma cikin faraa tadaga masu hanu tareda fadin “Hy...Hy” suma sukacemata “Hy...nd’ welcome back” tace “thanks”. Daganan aka saka kayanta amota suka shiga suka fice,bayan motoci uku dasuka shiga wasu motacin ukun na bayansu dake d’auke da bodyguards dinsu. Koda suka isa kowa awani dank’areren gida naga sunshiga k’ayatacce mai kyan gaske,bayan motoci sunyi parking suka fito saiga hadiman gidan sunzo suka durkushe sunamawa bunayya barka da dawowa ta amsa masu cikin sakin sakin fuska. Daganan suka fice izowa cikin gida. A parlor suka fara zama kamin daga bisani tashiga bedroom dinta domin yin wanka, bayan tai wanka tacanja kaya izowa wando da riga na hutawa marasa nauyi sannan ta kitse sumarta batareda tasaka rivom ba sannan tafesa tirare tasaka takalmanta tafita parlor. Koda taje ita kad’ai ake jira ai dinner
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34