Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,251 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

gida Nigeria. Bayan dawowarsu ne momyn mashkur tasami dadynsa tarokesa akan yaroki abban ruwaida yabar bunayya tacigaba da rayuwarta da iyayenta na rik’o sbd zahirin gsky bazata iya rayuwa babusuba haka suma, nantabashi lbrn halinda momy take ciki a yanzu dan suma sunje dubata. Dadyn mashkur yamata albishir dacewa sunbarmawa su dady bunayya har abada tinda dai basumata mummunan rik’o ba, hasalima suna matuk’ar k’aunarta, momy taji dadin wannan zancen matuk’a. Tana batun takira umman ruwaida saigashi itama takirata,ashe itama zancen ne take batun tafadamata, mashkur ma lbrn yarizkesa yai farinciki matuk’a har saida yakira bunayya yatayata murna. Tinda yake baitab’a ganin tsintsar farinciki a fuskar bunayya ba kamar yanzu, dik halinda take na k’unci tanajin wannan lbrn saita wartsake kamar baitaba sai farinciki take tana murna,nantake tafara shirin tafiya gida. Washe gari harda su dady suka shirya suka tafi kebbi gaba daya, koda sukaje har ansallami momyn bunayya tana gida kuma Alhmdllh tasamu sauki kwananta biyu da dawowa. Anan dai aka jajantawa juna tareda bawa juna hkr akan abunda yafaru, daga bisani abban ruwaida yadamka bunayya ahanun dady da momy amatsayin babbar kyauta yace “nabaku ita har abada kuma kusani nayi matuk’ar farinciki da irin rik’onda kukamata,so gatanan nabaku amana kucigaba da bata kulawa kamar da, Allah yayafemana kura kuranmu yabamu ikon bautamasa da karfinmu da lfyr mu” nan kowa ya amsa da Ameen. Gdy mai yawa momy tadingayiwa abban ruwaida harda durkusawa kan guiwowinta dan farinciki saida tazubda kwallah bunayya tazo tarungumeta tana dariyar farinciki abundai gwanin ban shaawa, basubar garin kebbi ba saida momy tashiryamasu liyafa tagani tafada inda kowa yai hani’am da cikinsa,baya nan kuma tabi kowa da kayatacciyar kyauta. Sun rabu da juna cikin farinciki bunayya na mak’ale da momynta kamar zata koma cikinta tasake haifota,yau da’alama shagwabar tamotsa,tana makale daita takemawa su mashkur bye bye, da zai wuce saida mirtsiketa a ciki tamasa gwalo tana dariya dan cewa yai tazo suje yola saisu koma school atare tace tak’i. Suna kallon motocinsu har suka kure sukabar unguwar sannan suka koma ciki. Ranar dai kwanan farinciki momy da bunayya sukayi,yau dady yafewa bunayya momy yai dan atare suka kwana d’akin bunayya dan yau shagwabar tamotsa. ..................... Bayan faruwar wannan lamarin wata zumuncice mai k’arfi tashiga tsakanin iyayen bunayya nagaskiya dana raino, a yanzu sundawo tamkar yan uwan jini, yanzu dik su bunayya sukai hutu a yola take k’arisa hutun,tasaba sosai da yan uwanta. A yanzu tasan yanda zumuncinsu yake da mashkur,wato da mahaifinta da mahaifin mashkur uwa d’aya uba daya suke, hajiya maimoon da Alhj murtala sune iyayen bunayya nagaskiya, doctor zainab haroon da doctor Abdallah sufi sune iyayen mashkur wanda doctor Abdallah shine Vice President a jihar yola shikuma barrister murtala shine PA din governor na garin yola,mahaifiyar bunayya tanada wani poundation na tallafawa gajiyayyu dakuma marayu. To wannan kenan. .................. Amintakar bunayya da mashkur sai k’ara k’arfi take a yanzu tinda sukasan matsayin junansu agunsu. A yanzu bunayya takammala 100level zasu shiga 200level,inda shikuma mashkur yake acikin shekararsa ta k’arshe takammala masters degree dinsa, to Alhmdllh. A yanzukam rayuwa mai cike da dad’i da tarin farinciki ke gudana a tsakaninsu. #/Comment nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI......_*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _27/28....._ Ahalin yanzu bunayya sunshiga 200level danhaka karatu suke sosai ba kama hanun yaro,tana matuk’ar san karatinta sosai shys take k’ara burge mashkur yake k’arajinta da wani matsayi acikin zuciyarsa. Bunayya da mashkur ne zaune akan kujeru agunda su bunayya kezowa karatu,wajen k’arkashin wata bishiyace mai bada kalolin iska masu dad’in gaske,musamman yanzu dayake yanayin damina,anyi ruwa yau da safe kusanma wuni akai ana ruwan,danhaka yanayin garin gwanin dad’i da bansha’awa, Ba rana sai lushi ga gajimare dik sunrufe sararin samaniya. Mashkur wani aikin yake kan laptop dinsa inda itakuma take game da wayarsa tata wayar tanakan cinyarta,surutu taketa zubamasa shikwa yana binta da ummm...um...um. Tintana maganar itakad’ai harta gaji tafarajin yunwa, shagwab’e fuska tai kamar zatai kuka tace “da meeee....” batareda yad’agoba yace “na am, menene?” cikin yanayin shagwab’ar tace “uhm...uhm..nifa nagaji wlh yunwa nakeji”. Batare yakalleta ba yace “Ok....je kici abinci mana,ni ina nan,idan kingama kizo ina nan so nake nak’arisa aikin nan naturasa zowa anjima” wata harara tamasa tareda turo d’ank’aramin bakinta kamin tace “what do you mean wai...nifa restaurant nakeso muje wlh,ni bazan iya zowa nai girki yanzuba,nagaji dacin indomie dinnan kasani kuma hamdallah taje weekend nikuma ba iya girkin tuwo nai dayawaba” yar dariya yai mara sauti sannan yace “Shkn naji,muje restaurant din” dariya tai tareda mik’ewa tsaye cikin farinciki hadda d’an tsallenta. Shikowa sai dariyanta yakeyi a zuciyarsa yana fadin “bunayya...bansan yaushe zaki girmaba,koda yake shekara 19 ai baza’ayi mamakiba dan kinyi yarinta gakuma tsabar shagwab’a datamata yawa ba” yana tinanin har suka kama hanya suna tafiya tanamasa shegantaka harda cewa yagoyeta wai. Hararanta yai yace “idan nagoyeki ai yau bazan iya tashiba sai amun gyaran targad’e a bayana” shagwab’e fuska tai tace “kai da mee...danka goyeni shine zaamaka gyara,nida ko wani k’ibar kirki banida shi,kuma banida nauyin kirki” dariya yai sannan yace “tabdi, kece bakida nauyi da kiba, ranar dana d’aukeki zan saka a mota dabakida lfy ko,saida nakusa fad’uwa k’asa dan nauy...” aibaiko k’arisaba tasakamasa kukan shagwab’a. Dariya yadinga mata harda rik’e ciki, juyawatai tayi fushi bazataci abincinba, dakyar yasamu tahak’ura tajuyo suka tafi. Yau takasance weekend suna hostel a zaune,fitowarta kenan daga wanka tana d’aure da towel a jikinta, biscuit takeci pure bliss mai dad’in gaske tanasan biscuit din sosai. Hamdallah nagefenta tana had’a miya ta abincinda take dafa masu,kallan bunayya tai tace “waike bazaki tashi kije kisaka kayaba,kinyi wanka amma har jikinki yabushe baki shafa koda mai ne ba bare kisaka kaya” tab’e baki tai sannan tace “Allah ni yau ganda nakeji wlh, man ma idan zan samu ashafaman inaso wlh” dariya hamdallah tamata tace “lallai kanwar mashkur dinnan,yayan nan naki yana k’ara shagwab’aki da momy” itama dariya tai tana fara shafa man. Bayan tashirya acikin wata abaya maroon color tasaka skin tide dark blue na jeans aciki da yar singlet fara aciki sannan ta taje sumarta gu d’aya hasken fuskarta yafito fas...golding eyes d’inta suka fito sosai goshinta sai haske yake yana shining, hamdallah bayan itama tashirya saita sakata agaba tamata simple make-up powder jan baki sai kwalli, hmm aikwa readers naso kuga bunayya a lkcn,tai matuk’ar kyau ba d’ankad’anba kamar kasaceta ka gudu, nan tamata rolling da veal maroon nantake tafito shuwa arabs ta asali. Cikin murmushi hamdallah tacemata “kinyi kyau matuk’a yar uwa,gsky kinada kyau sosai tubarakallah masha Allah,wannan shine ake kira da tsintsar kyau na asali,inama da mee...d’inki yana kusa yaga wannan kwalliyar, kai barama nakirasa da wayata” dariya take tafizge wayar tana fad’in “ba da mee ba,ni gun sabon saurayina zanje nanunamasa yaji dad’i yai farinciki”. Dasauri hamdallah tab’oye wayar tana dariya tafita, Bayan yan mintina sannan suka fita atare,itama hamdallah yau abaya tasaka red color amma itakam tai make-up sosai sbd yau weekend ne dole sufita yawo. Koda suka iso bakin get mashkur nanan yana jiransu acikin mota,ashe hamdallah nakiransa yakira wani abokinsa yakawomasa wata galleliyar mota Lang rover mai kyan gaske baka wulik sai shining take. Mamaki ne yacika bunayya daganinsa hamdallah takashemata ido daya sai itakuma ta harerata sannan tabude marfin gaba tashiga itakuma hamdallah tashiga a baya. Tana shiga yai murmushi tareda

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});