Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Aurenta Zanyi Book 1 Complete Hausa Novel 1,226 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suka shiga holl din inda suna isa akafara sake sauti akad’auki tafi sannan masu hotuna suka fara aikinsu, kusan 30mnts ana hotuna na waya dana camera saida mc dinda zai gudanarda shagalin yazo yakwace ango da amarya sannanfa aka daina. Cikin k’ank’anen lkc akafara gudanarda abunda yatara mutane, Dinner tayi matuk’ar k’ayatuwa bakad’an ba,abokanan ango dana amarya sun cashe san ransu ango sai dariya yake famanyi yawani mak’alewa bunayya,itakowa har yanzu takasa sakewa da kewar momynta. Yan uwa da abokanan arziki kowa yanuna farincikinsa, matuk’a anyi b’arin naira wajenyin lik’i kamar baasan zafintaba musamman abokanan ango dansu da dollars ma sukayi lik’in, hakama k’awayen momyn bunayya dana momyn mashkur suma dik da dollars sukayi likin abun saima yakusa yazamo gasa atsakaninsu, anyi b’arin dalolikam ba adadi. Dik wani shagali da’ake gun dinner an gudanarda shi, ancashe matuk’a, around 1:30am dot aka gama komai akafara watsewa kowa yafara kama gabansa, angwaye saida suka sauke amarya da abokananta sannan suka fice. Kowa yagaji matuk’a danhaka wanka kawai akayi akaci abinci masu sallar isha sukayi sannan kowa yabi lafiyan gado asuba tagari. #/Comment Nd’ Share #/Aufana for life. [7/22, 23:41] Mugirat Musa: _*AURENTA ZANYI....._*🌷 _Wattpad@Aufana8183_ _39/40...._ Yaukam bunayya tayi baccin gajiya, da asuba bayan tayi sallah ma sake kwanciya tai bacci mai nauyi yasake d’auketa, saikusan 10am sannan tafarka,koda tafarka su hamdallah harsun gama had’a breakfast danhaka tafice toilet tai wanka sannan tafito tashirya cikin wani tsadajjen material light pink mai kyau. D’inkin gown ne da d’ankwali sai mayafi white color da wasu plat shue white color suma, bawani make-up tai powder ce kawai sai lipsticks da kwalli amma tayi kyau sosai abunka da amarya sai kyalli take tana shining, bayan tagama shirin sannan tafita tasauka k’asa gunsu hamdallah. Atare sukayi break sunata firar shagalinda akayi na jiya gun dinner sunata dariya har suka kammala, bayan sungama sai suka dawo main parlor suka zauna. ................... A b’angaren angwaye kowa, sunacan gidansu mashkur a side d’in mashkur, tini suka kammala had’a masa kayansa tsab izowa gidansa, su mahbub sai sharri suke masa wai yaje gidansa yabarmasu gidansu sun koresa, shikwa sai murmushi yake dayake mashkur ba ma’aboci irin yawan maganarnan bane. Bayan sunshirya tsab saisuka shiga cikin gida suka gaishe dasu dady sannan suka fita, sunyi matuk’ar yin kyau sosai daka gansu kasan y’ayan masu gomnati ne, sunacikin naira suna wanka daita, acikin dank’ara dankaran motocinsu suka fita kowacce kagani kasan bak’arama bace. Kai tsaye gidan amarya suka fice acikin mota sai iskanci sukamawa ango mashkur sunamasa irin wasan abokanan ango dai,shikowa sai hararansu kawai yake yana murmushi. Bayan sun iso sukai parking suka fito sannan suka fice izowa ciki. Su bunayya na cikin parlor sukaji sallama dakuma hayaniya kamin ayi nocking, nafisa ce tad’an leka saitaga ashe angwayen ne, aikwa dasauri tafadamawa su bunayya nan aka shiga k’imtsawa, saida suka gama kimtsawa sannan tabude k’ofar. Atare suka shigo nan aka shiga gaggaisawa sannan suka zauna,bayan sun zauna nan fira tab’arke tsakaninsu, dik abunda akeyi bunayya dai bata saka bakintaba tai zamanta tana saurarensu idan akai abun dariya tayi murmushi tai zamanta takuma rufe jikinta da mayafinta. Hmm readers nifa har mamakin hankalin da bunayya tai nake,kamar ba bunayyar London ba, Lol Allah ik’ara shiryardamu Ameen. Mashkur kowa yanad’an tsoma bakinsa aciki, sadiq da mahbub sunfi kowa surutu hamdallah kowa tace tafisu bakin nan akaita kacamewa anayi, kamin daga bisani suna bamawa kowacce k’awar amarya tirmin zane na super wax wacca ak’allah kud’inta zasukai 35 thousand naira dakuma kud’i naira dubu ashirin sannan had’eda kayan biki waenda akayi, saikuma dankara dankaran motoci har uku waenda zasu maidasu har gidajensu. Godiya su hamdallah sukayi sosai, daga bisani angwayen suka fita. Anan su hamdallah suka wuni saikusan 5:45pm sannan suka kammala shirin tafiya gida, bunayya tarik’e hanun hamdallah tana hawaye musamman lkcnda suka fito zasu shiga motoci aifa nan tak’ara rikicewa wai karsu tafi subarta, kuka kowa take ba kaukautawa tanata sharan kwallah danma tana ganin idonsu mahbub ne da yanzu tafara dirar k’afafuwa tana kukan mai sauti to saidai bahali. Dakyar hamdallah tasamu tafukce hanunta tashige mota sbd ita kad’ai ake jira, shima saida mashkur yacire hanun sannan tasamu tafice,hamdallah ma saida tai kuka sbd ganin bunayya nayi,aikwa motocinsu na tashi bunayya tafice dagudu cikin gida tahaye sama tashige bedroom d’inta tarufe k’afar. Su mashkur kowa bayan su hamdallah sunfice fita sukayi daga digan. Bunayya kowa dataga ba sarki sai Allah saita d’akko wayarta tadingayin game tana rage tsawon lkc, saida akayi magrib taji ankira sallah a masallacin unguwar sannan ta tashi tashiga toilet tad’auro alwala tafito. Bayan tafito sannan ta shimfid’a sallaya takabbara sallah. Bayan tagama saita d’akko Qur’an tafara karantawa, bata tashi daga kan sallayarba har saida tai sallar isha sannan ta tashi. Parlor tasakko sbd jin cikinta yafara mata salati, kitchen tashiga tasakko sauran abincinda sukaci d’azun tareda su hamdallah sannan tafito parlor. Tv tabud’e sannan tazauna tafaraci tana kallon tashar Zee world, ahankali harta gama takwashe kayan takai kitchen sannan tadawo tai kwanciyarta tacigaba da kallo. Kallo take amma kokad’an hankalinta bayakan kallon,ta lulane acikin kogin tinani,tinanin sabuwar rayuwarda zata fara da yayanta mashkur take wanda a yanzu yake amatsayin mijinta na aure, wani d’an murmushi tai lkcnda zuciyarta tacemata “to yanzu taya zaki iya kallon mashkur amatsayin wai mijinki, taya hakan zata kasance” saitai yar dariya tareda furta “tabd’ijam....akwai jan aiki,wai yanzu da mee ne mijina, to tayama zan iya zama gida d’aya, d’aki daya, harma gadon bacci d’aya dashi amatsayin miji,bacin ni kunyarsama nakeyi tin acan baya, to barema yanzin,oh ni yar momy” tak’arisa cikin yanayin mamaki da al’ajabi. Tai zurfi acikin tinanin bata ankaraba taji ana nocking, ahankali tamik’e taje a bakin k’ofar har zata tambaya waye saitaji maganar mashkur dasu mahbub alamardai angwayen ne suka iso, danhaka dasauri taja mayafinta babba tarufe jikinta harda fuskarta sannan tabud’e k’ofar,tana budewa batama jira shigowarsuba tajuya. Sukwa ganin haka yasa bayan sunshigo suka tsayarda ango saida yai yan adduoi sannan suka shigo parlor. A kujerarda bunayya take zaune tasadda kanta k’asa tareda janyo mayafinta ta kare fuskarta,akanta mashkur yazauna dab da ita sukuma su mahbub suka zauna a sauran kujerun. Mahbub aminin ango wanda bashida kamarsa shine yafara magana, bayan sallama ta addinin islam saiya fara da janyo hankalin ma’aurata akan sanin menene ma shi kanshi auren tukuna, saida yai doogon sharhi akan kalmar aure ita kanta kamin yajega jan hankalin ma’aurata akan sudage akan ibadarda sukeyi ta aure sannan yacigaba da basu shawarwari daga k’arshe yabisu da kyakkyawor adduar zaman lfy kawarda fitina tsakaninsu dakuma kawo zuriah d’ayyiba ameen. Bayan yagama sai sadiq ya amsa yacigaba,shima yakusa d’aukan 20mnts yana tinatardasu hak’kokin miji akan matarsa dakua hakkokin mata akan mijinta, daga bisani yarufe dayiwa amarya da ango kyakkyawor adduah tareda fatan alkhairi asabuwar rayuwarsu. Hakama sauran ukun mujahid, ilyas dakuma mustapha, bayan sungama saikuma suka shiga yimasu nasihohi da tinatarwa kan zaman aure,hak’uri, juriya,kwantarda zuciya, yafiya, dakuma rufe sirrin juna, su mahbubfa sunyi kokari matuk’a sun nuna su abokanaine nagari. Daga bisani suka d’ora da tsokanar ango suna dariya shima yana dariya,bunayya kowa tinda ta sadda kanta k’asa bata d’agoba harsuka gama sukamasu saida safe suka fita shima yabisu domin yimasu rakiya. Saida suka fita sannan tad’ago da kanta tareda sauke numfashi, ledarda suka ajiye kan center table takalla

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});