Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Episode Twelve : This is Me

Maimoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,508 words 0 views Progress saved
Download Book

Note: duk maganar da akeyi da Ibrahim da turanci akeyi, amma zamu keyi da hausa saboda a samu sauki fahimta. Ayi karatu lfy

"Da gaske sisters ne su? " ya fada yana kallon sauran 'yan ajin. Duk ajin ya dauka "eh sir sisters ne, baka ga suna kama ba? " ya sake kallon mu yana girgiza kai, "ni ban ga kama ba" Hafsat ta kara kulewa ta hade rai sosai, shi kuma sai ya kalleta yayi dariya yace " ok Big Sister, kiyi hakuri na takura ma kanwarki. In babu damuwa to in dawo desk dinki mana maimakon nata? " Hafsat ta bude baki tana kallonsa da mamaki, sannan tayi sauri tace "a'a yi zamanka anan" yayi dariya sosai har habarsa ta lotsa sannan yace "dama nasan zaki ce haka, nima kuma nafi son zama anan" nidai duk ina jinsu bance komai ba. Sai da period dinsa ta fita sannan yace min "kar ki manta alkawarin mu, ni kadai nasan abinda zanyi miki in kika yi min irin ta rannan" da haka ya fita daga ajin. Yana fita Hafsat ta jawo kujerar ta kusa da tawa tace " alkawarin me mutumin nan yake magana akai? Yaushe kuka hadu har kika yi masa alkawari ba tare da nasa ni ba? " na kalleta nace " wani lokacin Hafsat ina mamakin mutane in suka ce na fiki surutu, sa idonki yayi yawa Hafsat " nan Hafsat ta kuma kuluwa tace " au haka ma zaki ce ko? Duk abinda nakeyi fa dan ke nakeyi. Mutumin nan daga ganin sa ba mutumin kirki bane, bana son kowacce irin alaka a tsakanin ku. I am trying to protect you" nace " ni kuwa Hafsat kina bani mamaki duk sanda kika ce Ibrahim ba mutumin kirki bane ba, how do you know? Kin san kullum daddy yana ce mana never judge a book by it's cover, ba dai dai bane ba kawai ki yanke hukunci akan mutum ba tare da kin fahimce shi ba" tace "OK kina so ki gayamin cewa ke kina so ki fahimce shi kenan ko? " nace mata "exactly " Amira ta taso tazo gurin mu tace "pls guys not here, zamuyi maganar in munje hostel" Hafsat ta cigaba da balbalin fada ni kuma na tashi kawai na fita daga class din. Kan veranda na zauna ina tunanin yadda zan bullowa wannan lamarin, nasan Hafsat akan gaskiyarta take fada, duk da ina da karancin shekaru amma na gane duk abubuwan da Ibrahim yake min da duk kwana kwanar sa nasan inda ya dosa. Kuma ni kaina basai wani yayi min fada ba nasan nayi kankanta da zuwa inda ya dosa. Abu na biyu kuma Ibrahim bayarabe ne, ni kuma bafulatana bana jin tarayyar mu dashi zatayi kyau. Murmushi nayi sanda na lissafo fuskar mommy inta samu labarin ina dating yaroba guy. Amma koma menene zai kasance yau zamu zauna muyi magana da Ibrahim, zan bukaci ya fada min duk abinda yake zuciyar sa ni kuma zanyi masa bayanin cewa abin ba me yiyuwa bane. Ina so mu samu maslaha a tsakanin mu.

Da aka tashi bayan munyi sallah munci abinci Amira ta jamu dakin su tana so ta daidaita tsakanin mu da Hafsat. Na zauna a nutse na yiwa Amira bayanin abinda yasa nake son muyi magana da Ibrahim. Muna ta maganar mu Hafsat tayi banza ta rabu damu, saida Amira tace mata "baki ce komai ba Big Sister" ta fadi big sister din da tsokana, irin yadda Ibrahim ya ce mata dazu a class. Ta juyo ta kallemu tana yamutsa fuska tace "She can do as she wants, ni dai tasan cewa komai tayi kamar tayi a gaban mommy ne dan wallahi sai na gaya mata" Amira tace "Haba Hafsat pls let her go, inta dawo zata gaya mana duk abinda sukayi dashi daga nan za muyi shawarar me zatayi next" Dakyar Amira ta lallaba Hafsat ta barni na tafi da sharadin cewa duk abinda yace min zanzo in gaya mata.
Naje nayi wanka na shirya a tsanake, dama ni ko a gida ba kwalliya nake ba ballantana a school na saka hostel wears dina, har na nada vail dina sai kuma na chire na dauko dogon hijab din Hafsat na saka. Ina fita na nufi library, tun daga nesa na hangoshi a zaune a side din library din da table a gabansa dauke da littattafai, amma kuma ba karatun yakeyi ba waya yake dannawa. Na karasa da sallama, ya dago kai ya kalleni da murmushi a fuskarsa, daga gani ya dade a zaune a gurin. Ya nuna min kujerara kusa dashi yayi min nuni da in zauna. Maimakon in zauna a kusa dashi din kamar yadda ya bukata saina dauki kujerar na zagaya daya side din na zauna ina fuskantarsa. Ban gaishe shiba nace masa "am here, what do you want ?" Ya sake yin murmushi yace min good evening ma'am" sai kuma naji kunya ban gaishe shiba nace "good evening sir" ya cire glasses din idonsa yana murza idon yace "har na fara tunanin bazaki zo ba, na dauka yau ma Hafsat ta hana ki zuwa" na kalleshi da mamaki nace "ya akayi kasan ita ta hanani zuwa rannan? " yace "da ban sani ba, sai dazu data cemin ita sister dinki ce sannan na fahimci ita ta hana ki zuwa" muka yi shiru baki daya na wani lokaci sannan ya cigaba da magana a hankali " am sorry for shiga rayuwarki da nayi kwana biyu. Nima bansan mai yake hawa kaina ba tun zuwa na makarantar nan, ina so ki fahimci cewa bani da wani mugun nufi a kanki sai alkhairi insha Allah. Tun ranar da kika amsa question dina a class naji kin burgeni, bayan na fita daga ajin ku na je staff room nayi tambaya akan ki anan na fahimci cewa you are a genius " nayi saurin katse shi nace "am not a genius " yayi dariya yace "research ya nuna cewa babu genius din da ya taba yarda cewa shi genius ne" ban bashi amsaba na sunkuyar da kaina kasa. Ya cigaba da cewa "tun daga nan na zama interested akan ki, lokacin ne nayi miki offering friendship. Kuma ina saka ran babu wani abu da zai rusha friendship din mu" ya sake yin shiru kamar ya gama magana sai kuma yace "ita zuciya tana da wahalar fassarawa, na kasa fahimtar me zuciya ta take nufi dake. Kullum sai inji ina so in ganki, inna ganki kuma sai inji bana so mu rabu, in ban ganki ba kuma sai inji na rasa farin ciki na" ya sake yin shiru yana shafa gashin kansa. "What do you want from me? " na sake tambayar sa a karo na biyu. Ya yi tagumi da hannayensa duk biyun ya sauke lumsassun idanuwansa a kaina sannan cikin muryar rada yace " ina so ki kara kahuri dani mu cigaba da friendship din mu, nasan wannan feeling din da nake ji akanki zai wuce wata rana. Ina so please kiyi tolerating dina for the time being. In kina ignoring dina zan iya aikata wani abun da ba dai dai ba". Duk bayanin da yake yi ina jinsa kuma ina analyzing duk maganganun sa. Na bude baki zanyi magana kenan sai ya daga min hannu ya dakatar dani yace "kar kice komai yanzu, ki bari sai kinje hostel kinyi tunani akai tukunna. Ina so mu cigaba da zama a friends but i have feelings for you. Nace masa to zanje inyi tunanin kamar yadda yace.

Muka danyi shiru na wani lokaci sannan ya ce " kafin kiyi tunanin amma ina so in dan baki brief labari na saboda ki fahimceni sosai. Kamar yadda na sanar dake ni bayarabe ne full blood. A yanzu shekaruna ashirin da biyar da haihuwa. Mahaifina ya rasu tun ina five years old. Nine babbar a gurin parents dina, sai kanne na mata su biyu. Bayan rasuwar mahaifina mamana ta sake aure ta haifi maza su biyu. Step father dina babban malamine a garin Ibadan, a gurinsa na koyi karatu sosai. Ya rike mu ni da sisters dina tamkar shi ya haifemu dan idan ba gaya maka akayi ba ba zaka san ba shine baban mu ba. Daga mamana har step father dina basu yi wani karatun boko sosai ba, baban mu dai yana dan taba kasuwanci kadan sai kuma islamiyya da yake koyarwa a unguwar mu, dan haka mu ba masu arziki bane sosai sai rufin asiri dai dai gwargwado. Allah ya bani kwakwalwar karatu na arabi da boko, wannan yasa baban mu ya sakani a makarantar kudi dan insamu ilimi mai kyau kuma Alhamdulillah na samu. Duk kudin babanmu akan karatuna yake karewa, sauran siblings dina duk a makarantun government suke, a cewar baba ni zan kula dasu inna samu aiki. Bayan na gama secondary school ne na samu na fara aikin teaching a wata primary school dake unguwar mu. Shekara ta uku ina teaching ina samun salary na baba yace lallai saina koma makaranta nayi degree, Allah ya taimakeni na samu admission a university of Ibadan nayi degree na a fannin mathematics. Na samu kyakykyawan sakamako na fita da first class shine NYSC suka zabe ni aka turo ni nan".

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Episode One : The Beginning of the Beginning
  2. 2 Episode Two: Meet my Family
  3. 3 Episode Three: Loved by All
  4. 4 Episode Four: Moon's Sister
  5. 5 Episode five: The Strangers
  6. 6 Episode six: The Challenge
  7. 7 Episode Seven: The Thin Tall Man
  8. 8 Episode Eight: The New Imam
  9. 9 Episode Nine: Give Me a Chance
  10. 10 Episode Ten: I Don't Know
  11. 11 Episode Eleven : The Protector
  12. 12 Episode Twelve : This is Me
  13. 13 Episode Thirteen : This is Me 2
  14. 14 Episode Fourteen : The Limit
  15. 15 Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
  16. 16 Episode Sixteen : The Letter
  17. 17 Episode seventeen: Reply
  18. 18 Episode eighteen: what's Next?
  19. 19 Episode Nineteen: The Goodbye
  20. 20 Episode Twenty: The New Job
  21. 21 Episode Twenty one: Amira
  22. 22 Episode Twenty Two: Efisowa
  23. 23 Episode Twenty three: The Break up 💔
  24. 24 Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
  25. 25 Episode Twenty five: The Eclipse
  26. 26 Episode Twenty Six: A Step Further Away
  27. 27 Episode Twenty Eight : University of Oxford
  28. 28 Episode Twenty Nine: The Message
  29. 29 Episode Thirty : The Final Blow
  30. 30 Episode Thirty One: Let it go
  31. 31 Episode Thirty Two : Munnir
  32. 32 Episode Thirty Two : Mahdi
  33. 33 Episode Thirty Three: Zayed
  34. 34 Episode Thirty Four : Back to Square One
  35. 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
  36. 36 EpisodeThirtySix: Interesting
  37. 37 Episode Thirty Seven : The Dinner
  38. 38 Episode Thirty Eight : The Shadow
  39. 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2
  40. 40 Episode Forty :TheShadow 3
  41. 41 Episode Forty One : Born for This.
  42. 42 Episode Forty Two : Born for This
  43. 43 Episode Forty Three: America
  44. 44 Episode forty four : America 2
  45. 45 Episode Forty Five : The Rush
  46. 46 Episode Forty Six : The Repentance
  47. 47 Episode Forty Seven : Amir
  48. 48 Episode Forty Eight : Awkward
  49. 49 Episode Forty Nine : Ya Habeeb
  50. 50 Episode Fifty : Munir 2
  51. 51 Episode Fifty one : Mommy
  52. 52 Episode Fifty Two : The Journey
  53. 53 Episode Fifty Three : Daddy
  54. 54 Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
  55. 55 Episode fifty five : Her Father's Daughter 2
  56. 56 Episode Fifty Six : What You Sow
  57. 57 Episode Fifty Seven : What You Sow 2
  58. 58 Episode Fifty Eight : I Missed You
  59. 59 Episode Fifty Eight : For You, Only You
  60. 60 Episode Sixty : The Prince
  61. 61 Episode Sixty One : Save the Date
  62. 62 Episode Sixty Two : The Manager
  63. 63 Episode Sixty Three : Amira 3
  64. 64 Episode Sixty Four : The Past and the Future
  65. 65 Episode Sixty Four : The Visitors
  66. 66 Episode Sixty Six : The Wedding
  67. 67 Episode Sixty Seven : The Wedding 2
  68. 68 Episode Sixty Eight : The Wedding Night
  69. 69 Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
  70. 70 Episode Seventy : The Wedding Night 3
  71. 71 Episode Seventy One : The Honeymoon
  72. 72 Episode Seventy Two : My Everything
  73. 73 Episode Seventy Three : His Father's Son
  74. 74 Episode Seventy Four : The Cook
  75. 75 Episode Seventy Five : The Emir
  76. 76 Episode Seventy Six : The Visitors
  77. 77 Episode Seventy Seven : Amina
  78. 78 Episode Seventy Eight : The Storm
  79. 79 Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
  80. 80 Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
  81. 81 Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
  82. 82 Episode Eighty Two : The Light
  83. 83 Episode Eighty Three : The News
  84. 84 Episode Eighty Four : Little Love
  85. 85 Episode Eighty Five : Ibrahim
  86. 86 Episode Eighty Six : The Phone Call
  87. 87 Episode Eighty Seven : Riyadh
  88. 88 Episode Eighty eight :Khairat
  89. 89 Episode Eighty Nine : Khairat 2
  90. 90 Episode Ninety : His Mother's Son
  91. 91 Episode Ninety One : His Mother's Son 2
  92. 92 Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
  93. 93 Episode Ninety Four : RIP
  94. 94 Episode Ninety Five : The Light
  95. 95 Episode Ninety Six : The New Bride
  96. 96 Episode Ninety Seven : The Real Prince
  97. 97 Episode Ninety Eight: My Baby
  98. 98 Episode Ninety Nine : New Little Love
  99. 99 Episode Hundred : Not The End.