Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 93

Episode Ninety Four : RIP

Maimoon Book 1 Complete Hausa Novel 3,395 words 0 views Progress saved
Download Book

Ya rike fuskata a hannunsa yana kallon cikin idona yace "kinsan dai da rayuwa da mutuwa duk na Allah ne ko? Kinsan babu wanda ya isa ya raya wani idan har Allah ya rubuta cewa kwanansa ya kare ko? Kuma kinsan babu wanda ya isa ya kashe wani in har kwanansa bai kare ba ko? Iyaye, 'yan uwa, miji ko mata, 'ya'ya dukka Allah ne yake bamu su kuma shi yake karbar su a lokacin da yaga ya dace. Duk lokacin da muka rasa wani abinda ya kamata muyi shine mu gode wa Allah daya bamu su tun farko, har muka rayu dasu muka ji dadinsu suma suka ji namu, dan daga mu harsu na Allah ne. Idan mutum ya riga ya mutu babban abinda yake bukata daga gare mu shine addu'ah, mu nema masa rahamar ubangiji tare damu baki daya, mu kuma yi fatan Allah ya sada mu dashi a aljannah inda zamuyi rayuwa ta har abada ba tare da tsofa ko mutuwa ba. Maimunatu Allah yayi wa Baffa rasuwa jiya da daddare, yau da safe akayi jana'izarsa aka kaishi gidansa na gaskiya." Wani sabon kuka ne ya taso min, yayi sauri ya hade bakinsa da nawa, sai da yaji na tsayar da kukan sannan ya sake ni, na ture shi da sauri na fara kokarin mike wa, ina jin kaina yana juyawa, wayyo Allah baffana, wai baffa ya tafi ya barmu shikenan ba zamu sake ganin sa ba? Na runtse idona ina hango kyakykyawar fuskarsa ta fulani mai cike da kwarjini da fara'a, innalillahi wa inna ilaihir rajiun, sultan naji ya sake rike ni yana kokarin zaunar dani "Moon zaki fadi fa, menene hakan wai? Shi yasa tunda aka kaishi asibiti aka ce kar a gaya miki saboda an san halinki" na juyo da sauri ina kallonsa bibbiyu, nace "asibiti? Au dama bashi da lafiya amma baka gaya min ba? Daya mutum ma har sai da aka binne shi sannan za'a gaya min" ya sake kokarin rike ni na ture shi, yace "to inda an gaya mikin ma menene zaki yi masa? Za ki cire masa ciwon ne ko kuma zaki hana shi mutuwa?" Da karfi nace "I could have been there for him, I could have hold his hands and say goodbye to him" yace "and what difference will that make?" Nace cikin fada "It would have make me feel better". Na rufe fuskata da hannayena na fara kuka a hankali mai shiga zuciya. Duniya kenan, ina nan ina enjoying rayuwata ashe Baffa yana can yana sallama da duniyar gabaki daya. Sultan ya zo ya durkusa a gaba na, har yanzu swimsuit din jikinsa a jike take yace " ya salam, moon da kinsan yadda nake jin kukanki a raina da kin daina, da ina da dama da ba zaki taba kuka a rayuwar ki ba, amma ba zan iya dawo miki da baffa ba, dan Allah ki tausaya min ki daina kukan nan haka" ni haushi ma naji yana bani, daga shi har sauran 'yan gidan mu duk haushi suke bani, tunda duk muna waya dasu kuma duk sun san baffa yana asibiti amma babu wanda ya gaya min. Ya dora hannunsa akan cinya ta na ture hannun na juya baya na na cigaba da kuka na. Ina jin shi ya mike ya shiga toilet, naji alamar shower sai kuma ya fito ya shirya, har lokacin ina zaune ina kuka na, yazo ya zauna kusa dani, na matsa. Yace "am sorry Love, nasan bashi da lafiya amma kinka yanayin da kike ciki, ga problem din bp dinki, wannan yasa aka ce kar wanda ya gaya miki, babu wanda yasan mutuwa zaiyi saboda babu wanda yasan gawar fari sai Allah. Am sorry" yayi kokarin juyo dani in kalle shi amma naki yarda, ya rabu dani yace "zan je airport yanzu in gani ko da akwai plight zuwa Nigeria yau ko gobe. Please dan Allah promise me you will stop crying" ya zagayo ta side din da fuska ta take, ya saka hannu ya bude fuskata dana rufe da hannuna, fuskarsa tayi abin tausayi, ya goge min hawayen fuskata, yace "kinji abinda na gaya miki? Ina so inje in samo mana plight tickets amma bana son in barki kina kuka kuma, please ki daina sai in tafi. In baki daina ba kinga ba zanje in sama mana plight ba ballantana mu tafi Nigeria" na goge fuskata ina kallonsa nace "na daina to" yace "promise" nace "I promise" sai da yaga na tsaida hawayena sannan ya fita, yana fita na hau kan gado na kwanta na cigaba da kuka na.
Wajan karfe daya ya dawo, inajin shigowarsa na rufe idona kamar bacci nake yi. Ya dan jima a tsaye yana kallona sannan ya hawo gadon ya dan taba jikina, yace "my God, kukan ki ka cigaba kenan ko? Bayan kinyi min alkawarin ba zakiyi ba" bance masa komai ba, naji ya sauka daga kan gadon, na bude idona ina kallonsa naga ya dauko first aid box din mu ya dauko min magunguna na, ya dauko bottle water ya bude ya hawo gadon ya mikar dani tsaye ya bani nasha. Na koma na kwanta ina kallonsa nace "so.., when are we going?" Ya dan shafa kansa yace "babu plight zuwa Nigeria yau da gobe, sai jibi idan Allah ya kaimu." ya miko min tickets guda biyu na karba ina kalla, that means sai Baffa ya kwana uku da mutuwa sannan zanje gida. Na lunshe idona ina jin jikina yana relaxing saboda maganin da nasha. Ina nan a kwance ina kallon sultan yana kokarin fara hada mana kayan mu, yayi waya restaurant ya fada musu abinda zasu kawo mana for lunch, da kyar na tashi nayi sallah na koma na kwanta. Bana kukan yanzu amma kuma raina gaba daya babu dadi, duk maganganun da muke yi da baffa ne suke dawo min rai na. Irin nasihohin da yake yawan yi mana akan gudun duniya, akan zumunci, akan biyayya ga iyaye da kuma miji. Da kyar sultan ya matsa min na danci abinci na koma na kwanta. Karfe biyar na yamma sultan ya gaji da zama shi kadai ya fita waje, sai kuma gashi ya dawo da sauri yazo ya daga ni tsaye ya fara kokarin cire min riga, na rike hannu sa, "sultan menene haka?" Bai ce min komai ba ya dauko wata rigar mai kauri da dogon hannu da collar ya saka min, ya saka min hula da safa ni dai duk ina kallonsa, nace "ina zamu je kuma" yace "kifi zaki je ki kamo mana ki gasa mana muci da daddare" na dan bata fuska nace "kifi kuma? Ni ban iya kama kifi ba" yayi murmushi yace "yau zaki koya, common, let's go" ya kama hannuna muka fita. A hankali naji na dan fara sakin raina, bawai na daina jin zafin mutuwar bane ba, na dai daina jin haushin sultan. Wani boat muka dauki haya muka shiga, daga ni sai shi, shi ya tuka ya kaimu tsakiyar ruwa sannan ya dauko wani dan kwando ya bude ya dauko wata kugiya ya daura zare a jikinta, sannan ya zagayo ya zauna a baya na, ya saka kafafuwansa a both sides dina, ya kama hannayena da nasa, ya saka fuskarsa a wuyana yace min a cikin kunnena "I am going to teach you how to catch a fish" cikin raunanniyar murya nace "sultan Baffa ne fa ya mutu, how can I just be busy catching fish bayan Baffa ya bar duniya?" Yace "mutuwar Baffa tana nuna mana abubuwa da yawa, daya daga cikinsu shine; there is an ending to life. Duk shekara, duk wata, duk sati, duk yini, duk awa, duk minutes, duk second din daya wuce ba zai dawo ba. What we need to do is to make the best of our time kafin namu lokacin muma yazo. We should live our life because it is a gift from God. Baffa yaji dadi, yayi rayuwa mai tsaho kuma mai kyau, ya tafi ya bar zuri'ah mai albarka. Wani tun kafin yayi aure ma yake mutuwa, wani tun yana yaro ma kafin yasan menene rayuwa yake mutuwa, wani ana haihuwarsa yake mutuwa, wani kuma tun a cikin mahaifiyar sa yake mutuwa, shi ko duniyar ma bai gani ba ballantana yaji dadinta. Wani kuma zai yi rayuwar mai tsahon har yakai kamar shekarun Baffa amma kuma sam babu abinda ya tsinana a cikin ta, babu abinda in ya tafi za'ace ga abinda ya bari na alkhairi sai dai na sharri. Amma baffa kuma fa? Ko mu daya bari ba mun isa mu taya shi gode wa Allah ba? Mu taya shi neman rahamar ubangiji ba?. Mutuwa is a circle of life, wani ya mutu sannan a haifi wani. Jiya da baffa ya mutu hundreds of babies were born all over the world, sannan hundreds of people sun mutu tare dashi" ya dora hannayen mu akan babyn mu da yake ta tsalle tsallensa babu abinda ya dame shi, yace "ranar da za mu haifi babyn mu, ranar hundreds of people zasu mutu. And what favor of our Lord do we deny?" Na lumshe idona ina ina jin dadin iskar gurin, ina jin dadin dumin jikin sultan, ina kuma jin dadin kalamansa, sannan inajin dadin motsin baby na a ciki na, what favor of my lord do I deny? Allah yayi min komai, ya bani komai, why should I be sad dan ya karbi abu guda daya daga cikin dubun daya bani? Na bude ido na ina kallon clear ocean din nace "I thought we are suppose to be fishing? Ya dan yi dariyar jin dadi yace "yes Love". Mun kama kifaye da yawa, dan sai da muka cika dan basket din da muka taho dashi, daga baya sai muka fara zaba, duk wanda muka ga mummuna ne sai mu mayar dashi cikin ruwa, gaba daya hankali naji ya kwanta, babu wani sauran bakin ciki a tare dani, nishadin mu kawai muke muna dariya, in mun kamo kifi yana ta tsalle mai in kankame sultan wai tsoro nake ji kar ya cije ni, in mun mayar dashi ruwa kuma sai muga sun fita a guje, nan ma muyi tayi musu dariya. Bamu ankara ba sai gani mukayi rana zata fadi, nan muka tsaya muna kallon rana tana setting on the ocean, rana tana gama faduwa kuma sai duhu ya fara saukowa, nan take naji tsoro ya kamani, na duba naga we are in the middle of nowhere, babu gida gaba babu gida baya, na zaro ido ina kallon sultan nace "sultan yanzu idan shark yazo ya cinye mu fa" yace "kin san kuwa akwai sharks a ruwan nan ba" da sauri na kankame shi "na shiga uku, shikenan a teku zamu mutu, ko gawar mu ma ba za'a gani ba, wayyo Daddy" dariya sultan yake min sosai sannan yace "am just joking, babu shark anan" ni dai ban yarda ba nace ya mayar damu hotel din mu. Hankali na vai kwanta ba sai da naji kafa ta ta taka kasa tukunna. Muna zuwa sultan ya dau basket din kifin ya kai restaurant din gurin yace su gyaro mana shi su kawo mana tare da kayan barbeque. Da daddare kifin mu muka gasa muka ci a matsayin abincin dare. Da daddare na tashi na gabatar da salloli na roka wa Baffa rahamar ubangiji.
Washegari ma Sultan bai barni na zauna ba ballantana inyi tunani ko kuka. Ya dauke ni muka tafi shopping. Kaya masu yawa ya saya mana ni da shi, bamu dawo dakin mu ba sai azahar, muna zuwa muka hada duk kayan mu da ba zamu bukata ba sultan ya dauka ya tafi shipping station din gurin ya bayar za'a kai mana har gida abuja. Tun da ya dawo yace min yau zai kai ni wani special guri muyi last dinner tunda gobe da safe zamu bar kasar. Muna sallar magrib muka shirya, ni kaina nasan munyi kyau, dama gashi na kara fari, in ka ganni ma ba zakace na taba shiga rana ba, ga kuma kibar ciki data kara min cika da budewa sosai, hips dina kamar wanda aka dauko aka dora min. Na saka riga da skirt bakake masu adon red, nayi rolling red veil wanda ya kara fito da hasken fata ta, kayan kuma tunda masu girma ne sai suka boye girman cikina. Sultan kuma suit ya saka ash, ya saka red shirt a ciki, ya taje kansa ya kwantar da gashinsa sai kyalli yake yi. Na zauna kawai ina kallonsa saboda kyan da yayi min. Golden brown skin dinsa tana reflecting duk fitilar data haska shi. Duk wanda ya kalle mu sai ya kara. Wani restaurant mukaje mai suna Ithaa, a karkashinin ruwa restaurant din yake, lifter zaka shiga tayi kasa da kai sannan sai kadan yi tafiya kadan a cikin wani glass corridor zuwa cikin restaurant din. Dan karami ne kuma shima duk da glass aka yi shi dan haka ji zaka yi kamar a tsakiyar ruwa kake, ni dai ji nayi kamar glass din zai fashe ruwa a shigo ya cinye mu. Gurin mutane 14 kawai yake dauka, amma fa abincinsu number one ne gurin dadi. Muna ci muna zuba soyayyar mu, dan gurin babu wanda ya damu da abinda wani yake yi. Bamu muka dawo dakin mu ba sai after ten. Muna zuwa muka kammala harhada sauran kayanmu mukayi sallah muka kwanta.
Washe gari da sassafe jirgin mu ya tashi, na leka ta window ina kallon islands din nace a hankali "Adiós Maldives, sai mun dawo" sultan yana kusa dani yace "we will come back for sure". Jirgin mu yana gama settling a sama na cire seatbelt dina na tashi na dawo kan cinyar sultan na kwanta, ban jima da kwanciya ba bacci ya dauke ni, sama sama naji sultan yana cewa plight attendant ta kawo mana bargo, ya dan kwantar da kujerar sa ya lullube mu da bargo. Gaba dayan mu bacci mukayi, dan sai da jirgi zai sauka a malam Aminu kano international airport sannan aka tashe mu. Muna fita reception muka tarar da Mahmud abokin sultan na kano wanda sultan ya kira ya gaya masa zamu zo yana jiran mu. Na kalli agogo naga 9:30am. Ikon Allah, banbancin lokuta a tsakanin garuruwa kadai ya ishi mutum abin mamaki. Mun baro Maldives 8:30, munyi tafiyar at least five hours amma kuma munzo Nigeria at 9:30am, to ina four hours din suka tafi?. Sai da muka tsaya muka danyi takeaway din abinci kuma sultan ya chanza kaya zuwa manyan kaya da hula sannan muka dauki hanyar 'yalleman. Sai a lokacin baji mutuwar tana sake dawomin a raina, muna zuwa kofar gidan naga cikar mutane a gurin, dan gabaki daya garin ma kusan a cike yake da mutane tunda yau ne sadakar uku. Kafin muyi packing na kira Amina nace tazo mu shiga tare saboda bana son shiga ni kadai. Ina shiga naga kowa ido shabe shabe da hawaye ai nan take na fara nawa nima, sai kuma kowa ya dora daga inda ya tsaya, naje na fada jikin Inna muna yi tare. Uncle Aliyu ne ya shigo da fadan sa, yace "dama tunda na jiyo sabon kuka nasan sarauniyar kuka ce tazo, menene haka maimunatu? Ana kokarin ayi masa adduoi ke kina kokarin ki tayar mana da sabon kuka ko?" Nan take na hadiye kuka na, na dau charbi ina ja amma ban san me nake cewa ba, hawaye ne kawai yake bin fuskata ina kallon irin jama'ar da Baffa ya bari, ga dakinsa nan kamar zai fito daga ciki. Sai yamma sannan jama'a suka dan ragu, sai a lokacin na samu naga Hafsat wacce itama nata cikin ya fito ba laifi, Daddy kuwa sai da daddare sannan na samu nayi masa gaisuwa. Washegari wajan 12:00 na safe duk kusan jikoki mata muna palon hajja a zazzaune sai ga aike wai inzo dakin inna nayi baki daga abuja sun zo min gaisuwa. A raina nace 'lallai Yaya da kokari, wannan tafiyar aita yi mata nisa da yawa, tunda munyi waya ba shikenan ba?' Na kama hannun Zainab amaryar yaya Walid muka tafi tare. Amma ga mamaki na ina shiga palon sai ganin Ummee nayi a zaune akan kujera tana kallona, na saka hannu na na mitstsike idona wai ko ba dai dai na gani ba amma still ita dince, da nani, da matar galadima da kuma Saratu da Huda. Na karasa gurinta da sauri na fada jikinta, ta rungume nu tana cewa "careful, kar kiji ciwo kuma" na fara kuka tana rarrashina, da hannu ta saka take goge min hawayena, duk mutanen gurin kallin mu suke da sakakken baki, nace "Ummee how comes you are in Nigeria? When did you come? Did Sultan know you are here?" Ta share min hawaye tace "I will tell you all about it later. Now let's pray for the dead" ta ringa jero adduoi muna amsawa. Na aika Zainab ta kira Hafsat, sai gasu tare da Amina, suka zo suka gaishe su. Haka mutane suka ringa shigowa suma gaishe da Ummee, wasu ma tsegumi ne yake kawo su. Hajja ta fara mita "idan nace sayar da yaran nan akayi sai ace min ba haka bane ba, in uta Hafsat ance balarabe ta aura to ita kuma maimuna fa? Ita data auri bahaushe menene hadin ta da larabawa?" Daga Mommy har Inna babu wanda ya tanka mata, ni dai ina nannade a jikin ummee ina lussafin ya akayi ta baro saudiyya ta taho Nigeria har tazo 'yalleman. Sai bayan sun ci abinci sun huta sannan na dauki waya ta na zagaya baya na kira sultan, yana dauka nace "kasan da zuwan Ummee kuwa?" Yace "wacce Ummee kike magana akai" nace "Ummee dai tamu, gata nan a dakin Inna" dariya yayi kadan yace "Moon rasuwa fa akayi, why are you making jokes" na koma na leka dakin ta taga na ganta akan sallaya tana addu'ah nace masa "wallahi va tsokanar ka nake ba Ummee ce suka zo da su Nani daga Abuja" ya kashe wayar, na koma dakin still ina kallonta, tayi min murmushi ta nuna min kusa ta ita alamar inzo in zauna. Da la'asar su Nani suka koma, amma banda Ummee da Huda, Ummee tace "sai gobe daddyn sultan zai zo sai mu tafi tare" ni dai kawai kallonta nake da mamaki. Sai bayan mun raka su mun dawo sannan nace mata "Ummee sultan fa bai san kinzo ba" tace "eh, bai sani ba" nace "dan Allah in kira shi ya ganki?" Ta dan dungure min kai tace "wai ke nan mai miji ko?" Na langwabe kai ina rokonta, tace "Ok, da daddare sai yazo mu gaisa, yana ina?" Nayi mata bayanin yana gidan nuraddeen, a can ya sauka.
Sai daga baya mutane suka gane Ummee surukata ce, sai kuma aka koma gulmar yadda muke da ita babu alamar sutukuta. Mommy sosai ta karbi Ummee suna ta hirar su, daga dukkan alama tasu tazo daya, ballantana nasan Mommy da son 'ya'yanta, soyayyar da taga Ummee tana nuna min ma kadai ya isa itama ta so ta. Da daddare bayan an watse sai few mutane, na kai Ummee palon waje, na kira sultan. Yana shigowa tsayawa yayi yana kallonta ya kasa magana, ta tashi ta rungume shi da sauri "my little love, how was the honeymoon?" Muka kalli juna ni da sultan, tace "do you guys enjoy Maldives?" Tayi dariya ganin yadda mukayi da fuskokin mu ta zauna muma muka zauna muka saka ta a tsakiya tace "kun dauka wai bamu san inda kuka tafi ba? Maldives kukaje, kuka sauka a hotel din soneva jani, cabin no 12" sultan ya bata rai "saka wa kikayi aka bi mu?" Tayi dariya tace "bani na saka ba, babanka ne, tun sanda kace masa zaku tafi ya aika wani a can Riyadh ya tsaya a airport yaga wanne plight kuka hau ya gaya masa, sannan ya kira Maldives din ma ya saka wani ya jira ku a airport yaga saukar ku kuma ya biku har hotel din da kuka sauka sannan ya gaya masa" sultan ya mike tsaye ya fara zagaye dakin "shikenan yanxu mutum bashi da private life kenan" ina dariya a raina ina cewa "sultan har yanzu America bata barka ba". Ya dawo ya zauna yana kallonta yace "to ya akayi kika taho Nigeria kuma keda akayi banning from leaving Saudi" Tace "They can't stop me from coming to Nigeria if am married to Nigerian".
Lol, we have new amarya in town.

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Episode One : The Beginning of the Beginning
  2. 2 Episode Two: Meet my Family
  3. 3 Episode Three: Loved by All
  4. 4 Episode Four: Moon's Sister
  5. 5 Episode five: The Strangers
  6. 6 Episode six: The Challenge
  7. 7 Episode Seven: The Thin Tall Man
  8. 8 Episode Eight: The New Imam
  9. 9 Episode Nine: Give Me a Chance
  10. 10 Episode Ten: I Don't Know
  11. 11 Episode Eleven : The Protector
  12. 12 Episode Twelve : This is Me
  13. 13 Episode Thirteen : This is Me 2
  14. 14 Episode Fourteen : The Limit
  15. 15 Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
  16. 16 Episode Sixteen : The Letter
  17. 17 Episode seventeen: Reply
  18. 18 Episode eighteen: what's Next?
  19. 19 Episode Nineteen: The Goodbye
  20. 20 Episode Twenty: The New Job
  21. 21 Episode Twenty one: Amira
  22. 22 Episode Twenty Two: Efisowa
  23. 23 Episode Twenty three: The Break up 💔
  24. 24 Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
  25. 25 Episode Twenty five: The Eclipse
  26. 26 Episode Twenty Six: A Step Further Away
  27. 27 Episode Twenty Eight : University of Oxford
  28. 28 Episode Twenty Nine: The Message
  29. 29 Episode Thirty : The Final Blow
  30. 30 Episode Thirty One: Let it go
  31. 31 Episode Thirty Two : Munnir
  32. 32 Episode Thirty Two : Mahdi
  33. 33 Episode Thirty Three: Zayed
  34. 34 Episode Thirty Four : Back to Square One
  35. 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
  36. 36 EpisodeThirtySix: Interesting
  37. 37 Episode Thirty Seven : The Dinner
  38. 38 Episode Thirty Eight : The Shadow
  39. 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2
  40. 40 Episode Forty :TheShadow 3
  41. 41 Episode Forty One : Born for This.
  42. 42 Episode Forty Two : Born for This
  43. 43 Episode Forty Three: America
  44. 44 Episode forty four : America 2
  45. 45 Episode Forty Five : The Rush
  46. 46 Episode Forty Six : The Repentance
  47. 47 Episode Forty Seven : Amir
  48. 48 Episode Forty Eight : Awkward
  49. 49 Episode Forty Nine : Ya Habeeb
  50. 50 Episode Fifty : Munir 2
  51. 51 Episode Fifty one : Mommy
  52. 52 Episode Fifty Two : The Journey
  53. 53 Episode Fifty Three : Daddy
  54. 54 Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
  55. 55 Episode fifty five : Her Father's Daughter 2
  56. 56 Episode Fifty Six : What You Sow
  57. 57 Episode Fifty Seven : What You Sow 2
  58. 58 Episode Fifty Eight : I Missed You
  59. 59 Episode Fifty Eight : For You, Only You
  60. 60 Episode Sixty : The Prince
  61. 61 Episode Sixty One : Save the Date
  62. 62 Episode Sixty Two : The Manager
  63. 63 Episode Sixty Three : Amira 3
  64. 64 Episode Sixty Four : The Past and the Future
  65. 65 Episode Sixty Four : The Visitors
  66. 66 Episode Sixty Six : The Wedding
  67. 67 Episode Sixty Seven : The Wedding 2
  68. 68 Episode Sixty Eight : The Wedding Night
  69. 69 Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
  70. 70 Episode Seventy : The Wedding Night 3
  71. 71 Episode Seventy One : The Honeymoon
  72. 72 Episode Seventy Two : My Everything
  73. 73 Episode Seventy Three : His Father's Son
  74. 74 Episode Seventy Four : The Cook
  75. 75 Episode Seventy Five : The Emir
  76. 76 Episode Seventy Six : The Visitors
  77. 77 Episode Seventy Seven : Amina
  78. 78 Episode Seventy Eight : The Storm
  79. 79 Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
  80. 80 Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
  81. 81 Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
  82. 82 Episode Eighty Two : The Light
  83. 83 Episode Eighty Three : The News
  84. 84 Episode Eighty Four : Little Love
  85. 85 Episode Eighty Five : Ibrahim
  86. 86 Episode Eighty Six : The Phone Call
  87. 87 Episode Eighty Seven : Riyadh
  88. 88 Episode Eighty eight :Khairat
  89. 89 Episode Eighty Nine : Khairat 2
  90. 90 Episode Ninety : His Mother's Son
  91. 91 Episode Ninety One : His Mother's Son 2
  92. 92 Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
  93. 93 Episode Ninety Four : RIP
  94. 94 Episode Ninety Five : The Light
  95. 95 Episode Ninety Six : The New Bride
  96. 96 Episode Ninety Seven : The Real Prince
  97. 97 Episode Ninety Eight: My Baby
  98. 98 Episode Ninety Nine : New Little Love
  99. 99 Episode Hundred : Not The End.