Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Episode Seven: The Thin Tall Man

Maimoon Book 1 Complete Hausa Novel 1,261 words 0 views Progress saved
Download Book

Washe gari first period muke da mathematics. Dan haka tunda na shirya nayi breakfast sai na dauki jotterta, calculator, sannan na duba syllabus naga abinda ya kamata muyi yau sannan na fice sai library. Ina zuwa na tarar librarian din ma zuwanta kenan. Ko gama cleaning library din ba'ayi ba. Na samu guri na jira har suka gama sannan na shiga. Miss Martha, librarian din mu ta tambayeni ya akayi banje class ba, na amsa mata da cewa teacher din mu bayanan kuma inada assignment da nake so in karasa. Ina shiga mathematics section na wuce, na debo textbooks din calculus har uku sannan na samu secluded guri na zauna na fara calculations dina hankalina a kwance. Saboda ina ganin a haka sai nafi ganewa akan ace wannan yaron ne zai koya min. Double period ce damu dan haka a lissafina zaiyi one hour 20min. Ina yi ina duba agogon hannuna har naga one hour ta wuce saura 20mins kenan. Hankali na gaba daya yana kan calculations dina saboda sosai nake jin dadin product rule din da nake yi a lokacin. Ji nayi tamkar ana kallona, da sauri na dago kaina tare da cire earpiece din kunnena. Ido muka hada dashi ga mamaki na sai naga ya sakar min murmushi. Daga dukkan alama ya jima yana kallona. Nayi saurin dauke kaina tare da sunkuyar da ido na kasa ina mamakin ganin shi a nan bayan nasan ya kamata ace yana class dinmu yana koya musu maths. "Mind if I join" ya fada cikin muryarsa mai sanyi. Ba tare da na sake kallonsa ba na ce "no". Kujerar kusa dani ya ja ya zauna. Ta ke naji na shaki kamshin sa. Na dan matsar da kujera ta kadan saboda kafadan shi da naji yana taba tawa. A hankali ya fara yi min magana wanda na tabbatar da ace da akwai mutun a kusa dani bazai ji me yake cewa ba. " Why aren't you in class" "am sorry" na fada a takaice. "Sorry for what" ya fada tare da adjusting kujerar sa yadda zai fuskance ni sosai, na kara jan kujerata baya sannan nace "for not attending your class". Murmushi mai sauti yayi sannan yace" it is not my class, it is OUR class, we are all suppose to be participating in it". Yayi shiru sannan ya kara da cewa " by the way, we miss u in class today. The class was exciting though, but I thought it would have been more exciting if u were there. So I asked of u and was told to check the library. And here u are. So, why are u here?" Ya tambaya yana kallon cikin idona. Na dauke kaina ina inda inda cike da jin kunyar abinda nayi. Ya saka hannunsa ya juyo da fuskata gare shi muke kallon juna, cikin muryar rada ya ce min "you think I am not good enough to teach you, right?" Kunya ce ta kamani, nayi sauri na kwace fuska ta daga hannunsa, nasa hannaye na na rufe idona cikin kunya nace masa "no" da dan karfi. Ga mamakina sai kawai naji ya kama dariya nima bansan sanda na fara dariyar ba. Sai da muka dena dariyar sannan ya dauki jotter din da take gabana tare da cewa " let's see what you have been doing for the past one hour" ban ce masa komai ba. Sai da ya gama studying abubuwan da nayi sannan yace " wow, we were in class tying to solve some few problems while you are here already done with the term. Na zaro ido nace "am not done with the term sir, am not even close" ya rungume hannayensa a kirjinsa, abinda na lura cewa dabi'ar sa ce. Yace " you are special, do you know that? Nayi sauri nace " no sir, am not. Kawai dai ina da son karatu ne" na fada ina kokarin kare kaina. Kallona kawai ya tsaya yana yi chike da rashin fahimta. Sai a lokacin na kalleshi sosai. Ba bahaushe bane. Na sunkuyar da kaina. "What tribe are you?" Ya tambaye ni cikin sanyin murya wadda itama by now na fahimci hakan yanayinsa ne. "Fulani" nace ina wasa da 'yan yatsuna. Yace " but what you just spoke is Hausa, right?". Nace "yes" yace " so u are Hausa Fulani " na girgiza kaina alamar a'a. Bai sake min wata tambayar ba. Can ya ce " I am yaroba. I am from Ibadan, Oyo state. My name is Ibrahim Adeniran Oluwaseun. Will you do me the honor of been my friend? " ya miko min hannunsa alamar shaking. Na gado kaina na sake kallonsa. Fatarsa ba mai haske nace kamar tawa ba kuma baka bace ( wankan tarwada). Dogo ne sosai sannan siriri ne dan bashi da kiba sam amma kuma straight bayansa yake tsahonsa bai sa ya rankwafa ba. Yana da doguwar fuska da dogon hanci da yalwataccen gashin gira. Bakinsa mai dan fadi ne mai dauke da siraren lips wadanda a yanzu suke dauke da murmushi. Fuskarsa tana zagaye da siririn saje da dan karamin gemu a habarsa. Fararen glasses be sanye a idonsa wadanda suke lumsassu kamar na maijin bacci. A hankali na sauke ajiyar zuciya tare da cewa " I am Fulani from Jigawa State. My name is Maimoon Muhammad Dikko. Yes, I will like to be your friend and I am sorry for missing OUR class today" " it is OK friend" ya fada yana sauke hannunsa ganin bani da niyyar shaking dinsa. Agogo hannuna na kalla, ga mamakina sai naga next period har tayi nisa. Da sauri na mike ina harhada takarduna hankalina duk ya tashi. Shima ya mike tare da daukan jotter da nayi calculations yace 'I will look this calculations over if you don't mind" "no problem" nace ina sauri duk hankalina yayi class. A bakin kofa ya sameni ina signing out. Ina fita ya biyo baya na, sai a lokacin na sake lura da tsahonsa, dan gabaki daya na a kirjinsa na tsaya. "See u tomorrow" na fada bayan mun fita daga libraryn. "See u in CLASS tomorrow" yace yana jaddada Kalmar class din. Da sauri nayi gaba dan bana so ya cigaba da bata min lokaci tunda already nayi latti a class din English. Ina shiga Aunty grace ta fara tuhumata akan daga ina nake, inda ni kuma na bata amsa da cewa ina library ina assignment ban san cewa har lokaci ya wuce da yawa ba.
Saida aka fita break sannan na tambayi Hafsat ya akayi a lokacin maths. Ta be baki tayi tace "ina ruwanki, ke da kikayi tafiyarki kika barmu da wannan dogon mutumin" nace "sorry tare da langwabar dakai, ta harare ni ta dauke kai alamar har yanzu fushi takeyi. " is he good? " na tambayeta. Kamar ba zatayi magana ba sai kuma tace "you will find out tomorrow, we have him double period da safe" " oh my God Moon, he is so good, ban taba enjoying mathematics irin na yau ba, I really did enjoy it. Wato dalla-dalla yake bin komai kuma sai ya tabbatar kowa ya gane sannan zai yi gaba. Gaskiya Moon kinyi missing " inji Hasiya wacce ta dawo kusa da desk dina fuskar ta kamar gonar auduga. Na mike tsaye na dubi sauran 'yan class nace "OK people, tomorrow, I will give the Thin Tall Man a chance" "Thin Tall Man?" suka kusan hada baki. Nace "yes" matter of factly, "baku ga yadda yake bane? I think the name fits him perfectly". Dariya ajin ya dauka gaba daya, inda ni kuma na bawa Hafsat hannu muka kashe muna kyalkyala dariya. Amira na hango ta gefen idona fuskarta dauke da bacin rai.

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Episode One : The Beginning of the Beginning
  2. 2 Episode Two: Meet my Family
  3. 3 Episode Three: Loved by All
  4. 4 Episode Four: Moon's Sister
  5. 5 Episode five: The Strangers
  6. 6 Episode six: The Challenge
  7. 7 Episode Seven: The Thin Tall Man
  8. 8 Episode Eight: The New Imam
  9. 9 Episode Nine: Give Me a Chance
  10. 10 Episode Ten: I Don't Know
  11. 11 Episode Eleven : The Protector
  12. 12 Episode Twelve : This is Me
  13. 13 Episode Thirteen : This is Me 2
  14. 14 Episode Fourteen : The Limit
  15. 15 Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
  16. 16 Episode Sixteen : The Letter
  17. 17 Episode seventeen: Reply
  18. 18 Episode eighteen: what's Next?
  19. 19 Episode Nineteen: The Goodbye
  20. 20 Episode Twenty: The New Job
  21. 21 Episode Twenty one: Amira
  22. 22 Episode Twenty Two: Efisowa
  23. 23 Episode Twenty three: The Break up 💔
  24. 24 Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
  25. 25 Episode Twenty five: The Eclipse
  26. 26 Episode Twenty Six: A Step Further Away
  27. 27 Episode Twenty Eight : University of Oxford
  28. 28 Episode Twenty Nine: The Message
  29. 29 Episode Thirty : The Final Blow
  30. 30 Episode Thirty One: Let it go
  31. 31 Episode Thirty Two : Munnir
  32. 32 Episode Thirty Two : Mahdi
  33. 33 Episode Thirty Three: Zayed
  34. 34 Episode Thirty Four : Back to Square One
  35. 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
  36. 36 EpisodeThirtySix: Interesting
  37. 37 Episode Thirty Seven : The Dinner
  38. 38 Episode Thirty Eight : The Shadow
  39. 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2
  40. 40 Episode Forty :TheShadow 3
  41. 41 Episode Forty One : Born for This.
  42. 42 Episode Forty Two : Born for This
  43. 43 Episode Forty Three: America
  44. 44 Episode forty four : America 2
  45. 45 Episode Forty Five : The Rush
  46. 46 Episode Forty Six : The Repentance
  47. 47 Episode Forty Seven : Amir
  48. 48 Episode Forty Eight : Awkward
  49. 49 Episode Forty Nine : Ya Habeeb
  50. 50 Episode Fifty : Munir 2
  51. 51 Episode Fifty one : Mommy
  52. 52 Episode Fifty Two : The Journey
  53. 53 Episode Fifty Three : Daddy
  54. 54 Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
  55. 55 Episode fifty five : Her Father's Daughter 2
  56. 56 Episode Fifty Six : What You Sow
  57. 57 Episode Fifty Seven : What You Sow 2
  58. 58 Episode Fifty Eight : I Missed You
  59. 59 Episode Fifty Eight : For You, Only You
  60. 60 Episode Sixty : The Prince
  61. 61 Episode Sixty One : Save the Date
  62. 62 Episode Sixty Two : The Manager
  63. 63 Episode Sixty Three : Amira 3
  64. 64 Episode Sixty Four : The Past and the Future
  65. 65 Episode Sixty Four : The Visitors
  66. 66 Episode Sixty Six : The Wedding
  67. 67 Episode Sixty Seven : The Wedding 2
  68. 68 Episode Sixty Eight : The Wedding Night
  69. 69 Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
  70. 70 Episode Seventy : The Wedding Night 3
  71. 71 Episode Seventy One : The Honeymoon
  72. 72 Episode Seventy Two : My Everything
  73. 73 Episode Seventy Three : His Father's Son
  74. 74 Episode Seventy Four : The Cook
  75. 75 Episode Seventy Five : The Emir
  76. 76 Episode Seventy Six : The Visitors
  77. 77 Episode Seventy Seven : Amina
  78. 78 Episode Seventy Eight : The Storm
  79. 79 Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
  80. 80 Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
  81. 81 Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
  82. 82 Episode Eighty Two : The Light
  83. 83 Episode Eighty Three : The News
  84. 84 Episode Eighty Four : Little Love
  85. 85 Episode Eighty Five : Ibrahim
  86. 86 Episode Eighty Six : The Phone Call
  87. 87 Episode Eighty Seven : Riyadh
  88. 88 Episode Eighty eight :Khairat
  89. 89 Episode Eighty Nine : Khairat 2
  90. 90 Episode Ninety : His Mother's Son
  91. 91 Episode Ninety One : His Mother's Son 2
  92. 92 Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
  93. 93 Episode Ninety Four : RIP
  94. 94 Episode Ninety Five : The Light
  95. 95 Episode Ninety Six : The New Bride
  96. 96 Episode Ninety Seven : The Real Prince
  97. 97 Episode Ninety Eight: My Baby
  98. 98 Episode Ninety Nine : New Little Love
  99. 99 Episode Hundred : Not The End.