Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 58

Episode Fifty Eight : I Missed You

Maimoon Book 1 Complete Hausa Novel 3,447 words 0 views Progress saved
Download Book

Na lumshe idona ina addu'ar Allah yasa shi dinne ya gani ba wai gizo yake yi min ba, dan ganin nasa ya taba min wani guri a zuciya ta wanda bansan yadda zanyi ba idan ba shi bane. Muna zuwa airport muka fito, mommy ce ta fara shigewa jirgi, daddy ya tsaya suna sallama da mutane, sai lokacin na samu damar ganawa da yaya Walid dan a mota tsoron mommy ya hana ni magana, na rungume shi tsam a jikina ina ajjiyar zuciya "I missed you" ya rabani da jikinsa yace "I missed you too sweetie pie" ta gefen idona na hango sultan yana tahowa gurin da muke, kara kankame yaya Walid nayi ina runtse idona, 'Oh Allah, give me the strength kar inje inji kunya a gaban mutane' na kasa kallon inda yake dan nasan zan iya loosing control, muryarsa naji yana cewa "to cika ta haka, ai an gama oyoyon" shi dinne dai, dan muryar sa ce wannan. Ya walid ya dafa kafaduna da hannayensa duk biyun yace "anki din, sai ka bari in an daura muku auren sai kayi min iko akanta amma yanzu tawa ce. Ni ban taba ganin ma suruki marar kunya irin kaba sultan, babban wa ai uba ne, ni ne fa madaurin auren ta, inna ga dama sai ince bazan bayar ba" yaushe Sultan suka fara wasa da Ya Walid? Last time I check ya Walid ya mari sultan. Wata dariya sultan yayi yace "kayi kadan yaro, ni iya kacin sanina na girme ka, dan haka kai ya kamata ka ke yi min biyayya" ya walid ya kama hannuna muka tafi jirgi, har yanzu na kasa kallon sultan, sai da muka fara hawa steps din sannan na juyo ina tunanin kar mu tafi mu barshi, ina juyo wa muka hada ido, nayi sauri na dauke kaina.

Chamber biyu ne da jirgin sai gurin pilots, daddy da mommy suna chamber din farko, mu kuma mu uku muna chamber ta biyu. Tunda na zauna har jirgin ya tashi ban daga kaina ba, duk jina nake a takure saboda idanuwan da sultan ya dora a kaina ko kiftawa baya yi. Ji nayi kallon yayi yawa na dan daga kaina kadan sai naga ashe ido hudu ne a kaina ba biyu ba, yau naga ta kaina zasu chinye ni danya. Ya walid yace "kin ganki kuwa? Wannan ai kece ifritu minal jinni. Wannan irin rama haka? Me Aunty Zaliha take miki?" Ni dai bance komai ba na rufe fuskata da hijab dina. Ina jin Sultan yana ce masa ya tashi ya koma gurin su Daddy, ya Walid yace "saboda me? Duk abinda zaka gaya mata ka gaya mata a gabana. Suma wadancan din couple ne, gwara ma ku ba aure ne da ku ba, babu wani abu da zakuyi wanda ba zan iya gani ba" su kayi ta maganganun su ina jinsu bance musu komai ba, shi Sultan yana ta insisting sai Walid ya tashi ya bamu guri shi kuma yaki. Nadan bude fuskata kadan na kallesu naga basa kallona sai na gyara zamana na bude fuskata sosai. A hankali nace ina kallon sultan "how is your leg?" Duk suka jiyo suna kallona da mamaki Sultan yace "What?" Na sake maimaitawa ina kallon kafarsa. Still bai gane mai nake nufi ba, nace "kafarka da kaji ciwo rannan, how is it?" Dariya yayi sosai, da alama yama manta da cewa yaji ciwon, yace "ta warke ai, tun tuni. Abinda ya kamata ki tambayeni shine how is my heart" ya Walid ya harare shi, ni kuma nayi murmushi ina sunkuyar da kai na kasa. Har muka sauka a Nigeria bamu samu munyi wata magana da Sultan ba, muna sauka muka tarar da motoci suna jiran mu, muka shiga sai gida. Tunda da na fito daga mota nake jin idanuwan sultan a kaina amma baki kallon inda yake da sauri na shige cikin gida. Ina shiga palo na tarar da yaran gida kowa sai murnar dawowa ta suke, nan na sha runguma har sai da jikina ya fara ciwo, da wayo na gudu na hau sama na shiga dakina, a gyare na tarar da dakin sai kamshi yake yi, na fada kan gado tare da lumshe idona, home sweet home, da sauri kuma na mike naje na bude window ina leken waje ko zan ganshi amma naga bayanan, to ko ya tafi gidan su? Toilet na shiga na kunna ruwa a tub na hada kumfa sosai, when was the last time I had a real bath? Na cire kayana na shiga ina sauke ajjiyar zuciya. Na lissafo irin wahalar da nasha, kuma duk akan Sultan amma yanzu wai gani gashi na kasa yi masa kwakwkwarar magana. Sai kuma na fara yiwa kaina tambayoyin me ya faru da bana nan? Ya akayi har su daddy suka karbi sultan har ya saba dasu sosai? Jin ana kiran sallar isha yasa na tuna ko magrib banyi ba, na dauraye jikina na fito, na bude kayana naga sunanan yadda na tafi na barsu sai dai daga alama an dan karkade su an sake gyaramin, na saka wasu riga da skirt ga mamaki na sai naga wuyan rigar yayi min yawa skirt din kuma yana zamewa, chafdi, gaskiya na rame da yawa, dole na saka doguwar riga nayi rolling mayafi na fita. Ina saukowa daga sama na tsaya da mamaki, Sultan again, dare dare a kan kujera a palo suna ta zabga musu da ya Habeeb, a tare suka juyo suka kalle ni, dif sultan ya dauke wuta ya daina magana, ya Habeeb kuma ya taso da sauri gurina yana cewa "welcome home, my parrot" nayi murmushi na karasa gurinsa, sai kuma ya rike hannuna yana kallon fuskata, dariya yayi yace "kinga yadda kika yi baki kuwa?" Na juya idona nace "tubarkallah, wannan yace da rame wannan yace nayi baki in ba so kuke ku chinye ni ba ai ya kamata ku kyaleni haka" daddy ne ya shigo Walid yana biye dashi a baya, duk muka gaishe da daddy ya hau sama, har lokacin sultan bai ce min komai ba sai kallo kamar zai chinye ni, dole na tashi na tafi kitchen na zauna ina kallon ana ta fita da kayan abinci, sai da naji daddy ya kuma saukowa sannan na kuma palon, still Sultan yana nan, muka tafi dining har dashi, sai kawai naga ya tashi yana serving din mu, what is happening ne ni maimunatu? Someone should start explaining. Har ya zuba min abincin kuma sai ya dauke ya sake karo min ba tare da ya kalleni ba yace "ki chinye wannan a karo miki wani" ji nayi duk suna dariya ni bansan dariyar me suke yi ba, daddy yace "yes, kina bukatar alot of food da kuma bacci ko kya yi kyan gani" a raina nace Daddy kaima harda kai ko? Allah ne kadai yasan shi kuma Sultan me zai ce min. Na dan fara cin abincin kamar bana so kuma sai naji taste din abincin ba zan iya resisting ba, nayi missing home da duk wani abu na home din, ya Habeeb yace "to 'yar agadaz, bamu labarin agadaz" na yi murmushi nace "sai dai in baka labarin anty Zaliha da samarin 'ya'yanta, dan su kadai na gani tunda naje agadaz din, ko kofar gate ban taba zuwa ba" nan aka koma hirar Niger da zafin garin, suna cewa zafin ne ya sakani baki. Tunda muke hirar Sultan baice mana komai ba abincinsa kawai yake ci, har ya gama yasha lemo ya mike tsaye, ina kallonsa muka hada ido nayi sauri na dauke kaina. Yace da Daddy "Daddy sai da safe" Daddy yace "Allah ya bamu alkhairi" ya dan jima a tsaye kuma sai ya tafi, naji bude kofar palo amma banji rufewa ba. Yaya habeeb ne ya fara taba ni yana nuna min hanyar waje, nayi kamar ban ganshi ba, ina jin yaya Walid yana yin dariya kasa kasa, sai kuma ya dan daga murya yace "na'am? Tana zuwa" sai ya ce a hankali "kamar naji sultan yana kiranki ko?" Shima yi nayi kamar bansan me yake yi ba amma fa ta ciki na ciki, a hankali Daddy yace "tashi kije" nace "yes Daddy" na mike a hankali kamar bana so nayi hanyar waje, amma fa a xuciya ta ji nake kamar in kwasa a guje. Ina zuwa kofar falon na ganta a bude, na fita na mayar da ita na rufe. Kafin inyi taku daya naji ni a jikin sa, duk da banga fuskarsaba amma nasan shine, na danyi kokarin raba jiki na da nashi amma ya rike ni tsam, nima kuma I need the hug, dan haka na kwantar da kaina, a tare muka sauke ajjiyar zuciya, ina jin bugawar zuciyar sa kamar a kirjina take bugawa, mun jima a haka sannan ya kawo bakinsa dai dai kunne na yace "I missed you" na kara narkewa a jikinsa dan ni inajin ba zan iya cewa ma i missed you din ba. Sai da hankali na ya fara dawowa jikina na tuna anytime wani, ko kuma ma Daddy da kansa zai iya bude kofar palon ya fito. Na dan zame daga jikinsa amma ina jin kamar na bar wani part of me a tare da shi. Yana kallona yace "come, let me show you something" yayi gaba na bishi a baya da sauri, naga yayi hanyar part din su ya Habeeb, ni dai binsa nake, ya bude kofar yayi min alama da in shiga, ina shiga naga gurin gaba daya ya chanza min, wani kamshi mai dadi yana tashi, kamshin Sultan, irin kamshin da kullum motarsa take yi kuma irin kamshin da naji a apartment dinsa na newyork, ya tsaya a bayana yace "welcome to my humble home" na juyo ina kallonsa da mamaki, ya jawo ni ya zaunar dani akan kujera shi kuma ya zauna a gaba na ya harde kafafuwansa yace 'I have a story to tell you" nan fa ya fara bani labarin abubuwan da sula faru tun tafiya ta, duk irin abubuwan da Daddy yayi masa, dawowarsa gidan mu hatta zancen sabon kamfaninsa daya bude sai da ya gayamin, nayi mamakin yadda al'amarin ya kasance sannan na jinjinawa Daddy na, na kuma gode wa Allah da samun uba na gari da nayi, dan iyaye na gari sune ginshikin rayuwar 'ya'ya, sannan kuma na kara imani da kuma godiya ga Allah, dan nasan duk abinda ya faru ya faru ne saboda karfin addu'ah. Ni kam babu abinda zance sai Alhamdulillah. Nan ni kuma na zauna na fara bashi labarin nima abinda ya faru dani tun sanda ya Walid ya dauko ni daga gurinsa, tafiyar mu niger da duk abinda ya faru acan har taimakon da musbahu yayi min na samu na kira daddy na. Nace "yanzu Mommy ce kadai matsala, ita ma kuma insha Allah zata sauko" na sauko daga kan kujerar nima nayi irin zaman da yayi na cigaba da bashi shawarwari akan sabon companyn sa, na bashi shawarar ya bude branch a New York tunda yana da mutane sosai acan, naga alamar yaji dadin shawarar, nan yace in zabarwa companyn suna wai dama ni yake ta jira in dawo in fadi sunan da nake so, nace zan zaba amma ba yanzu ba sai nayi tunani. Nan kuma na sake bashi shawarar yake zuwa palace yana gaishe da babanshi, ya dan bata fuska yace "why?" Nace "because he is your father" Ya Habeeb ne ya shigo palon, ya tsaya yana kallon mu da mamaki yace "wai ke har yanzu kina nan? Mu duk mun dauka kinyi bacci by now?" Na kalli wall clock din palon 12:49, da sauri na mike ina rufe bakina da hannu, na shiga uku, duk dariya suke min, Allah yasa Mommy bata shiga dakina ba, dan tunda muka dawo gidan ban kuma ganinta ba, kar in kara wani laifin akan wani. Ya Habeeb yace "soyayya dadi, wayo ku baku ma san lokacin ya tafi ba ko?" Da sauri nayi hanyar waje ina jin Sultan ya biyo bayana yana kirana, a bakin kofa na tsaya ya karaso ya miko min wani abu a leda, na kalle shi da alamar tambaya yace "it is a phone, ba zan iya hakura da jin muryar ki ba, dazu na siyo na yi miki charge dinta na saka miki sabon sim" na dan yi shiru amma kuma nima ina son muke wayar ai. Na karba nace "thank you" bai ce komai ba, na juya na cigaba da tafiya ya sake biyoni ya sha gabana yana tafiya da baya da baya yana kallona kamar wacce zan gudu, har muka je kofar palon mu, na kama handle din kofar yace a hankali "love" na juyo na kalleshi, a hankali ya sake cewa "thank you for loving me" bance komai ba sai murmushi da nayi, shima murmushin yayi min, and in that moment ji nayi duk hawalar da nasha is nothing, for him, I can do it all over again, ko da wacce tafi ta baya ce ma.

A bangaren Mommy kuwa tunda suka dawo ta shiga dakinta ta rufe kofa, ta kwanta a kan gado zuciyarta tana yi mata zafi, mai yasa wai kowa ba zai fahimce ta ba? Wannan yaron ba yaron kirki bane, bai dace da Moon dinta ba, her perfect daughter deserves someone like her. Wannan yaron is too strong for her daughter, in anyi auren ma cin zalinta zai tayi yana lallabata ita kuma da raguwar zuciya tayi ta yafe masa. That's is ko da ace ya gyaru ma, in kuma bai shiryu ba yaje ya sha giyarsa yazo ya lakada mata dukan tsiya. Ta runtse idonta, bama zata iya tunanin 'yarta wani katon gardi yana dukanta ba. Ta tashi ta dan daga labule ta leka waje, shi ta fara gani akan mota tare da habibin ta, ta rasa wanne irin charm yayi using akan 'ya'yanta da mijinta, ita yanzu abin kunya ne ma kawayenta su shigo su ganshi a gidanta bayan duk irin maganganun da suke yi a office akansa, da akwai cases dinsa da yawa da ake kawo musu amma sai kuma azo a janye saboda iyayensa sun bata shi, ita ta kasa gane wanne irin so iyayensa suke masa da har suka barshi ya lalace haka, wannan ai ba soyayya bace. Ta shiga toilet tayi wanka ta fito tana shiryawa, wai har ita yau dear ya zauna ya wanke ta agaban iyayenta, abinda bai taba yi mata ba kuma duk akan wancan shegen ruwa biyun. Ta saka kayanta ta fita ta leka dakin Moon ta jita a bandaki tana wanka, ita kunyar 'yar tata ma take ji, me zata ce mata bayan tayi failing, yanzu ga yaron nan an kawo shi har gida yadda zaiji dadin lalata mata 'ya a gidan ubanta. Ta sauka kasa tana bada order abincin da za'a dafa, a kitchen din ta zauna kamar yadda ta saba akayi aikin abincin tare da ita, sai da ta tabbatar komai ya kammala sannan ta koma sama tace akawo mata nata sama, bata son wannan tsageran yaron ya shigo ya same ta a kasa, da wasu idanunsa a tsatstsaye irin na marasa kunya. Ta koma dakinta tayi sallolinta sannan ta jawo abincinta taci, duk abincin ma babu dadi, sam yanzu bata iya cin wani abin kirki, she is suppose to be downstairs with her family, kamata yayi ace tana can ta tabbatar Moon taci abinci ta ko shi. Amma sam dear yaki sauraronta, ita ba zata iya zama da yaron nan ba, shi kuma direct ya gaya mata shi fa ba zai kore shi daga gidan saba sai ranar da shi da kansa yace zai tafi. Kuma yaran ma babu wanda ya hawo yayi mata magana, irin Mommy mai yasa ba kya saukowa mu ci abinci tare? Ji tayi wani hawaye ya zu bo mata, ta goge tare da jawo wayarta ta duba time, safiya ce yanzu a England, tayi dialing number din Hafsat.

Hafsat ta gama sallamar Zayed tana shirin shiga wanka taji shigar kira daga Mommy, ta zauna da kyar saboda nauyi da ta fara, ta daga da sallama. Mommy ta amsa da daskararriyar murya, suka gaisa sannan mommyn tace "Moon ta dawo gida" da yake tuntuni Hafsat tasan duk abinda yake faruwa, da sauri Hafsat tace "Haba? Tana ina? Dan Allah Mommy bata mu gaisa" Mommy tace "tana kasa tare da daddyn ku da brothers dinku, da kuma wannan yaron" Hafsat ta gane wa take nufi. Sun jima shiru sannan Mommy tace "Hafsat ke kinfi kowa sanin Moon, dan ina ganin kamar hatta ni da na haife ta kinfi ni sanin ta, please tell me, where did I go wrong a tarbiyyar dana bata? Me yasa tayi choosing ta bakantamin ta tozartani a cikin jama'a? Me yasa ta zabi sultan? Me yasa tun farkon ganin ta dashi ba ta fahimci cewa ba sa'an auren ta bane ba?" Hafsat ta danyi shiru sannan tace "Mommy kaddara ce, destiny, Sultan destiny din Moon ne haka itama Moon destiny din Sultan ce. Allah ya riga ya rubuta cewa sai sun hadu kuma sai hakan ta faru a tsakanin su. Mommy babu inda kikai wrong a tarbiyyar mu dan ba mu kadai ba duk wanda ya san mu yana yabawa da irin tarbiyyar da kika bamu, wannan shi yasa ko da yaushe muke kokarin mu zama perfect saboda kar muyi failing dinki, but no body is perfect. Duk abinda Moon tayi tayi shine because she is afraid of failing you Mommy. Sultan ba shine saurayin Moon na farko ba, tayi Ibrahim, she loved him so much amma haka tayi ta kumbiya2 saboda tasan ba lallai ne in ta kawo muku shi ku karbe shi ba, sanda tayi summoning courage kuma ta kawo shi gida shi kuma ya kasa summoning courage yayi facing Daddy. Sai da tayi spending five years kafin ta cire ran dawowarsa. So you understand why she is holding tightly unto Sultan. Shima haka tayi ta hiding dinsa daga gurinku saboda tasan shima ba zaku amince da shi ba. Tsoron da take yi na cewa zaku rabata dashi shi yasa take going behind your back take ganinsa. Na sha bata shawarar ta kai ku gurinsa but she kept saying she is waiting for the right time, she was afraid, afraid of not being the perfect girl you want her to be. So tayi ta dan gyara shi kafin ta kawo muku shi, amma sai gashi kun ganshi in his worst" tunda ta fara magana Mommy bata ce komai ba, sai da taji tayi shiru sannan tace "yanzu me kike ganin ya kamata inyi" Hafsat ta sake cewa "Mommy ni personally i don't like sultan, but tunda har Moon tayi falling for him, kuma Daddy ya dauko shi ya hada shi da 'ya'yansa gudan jininsa, suma kuma a cikin 'yan watanni har suka saba dashi then there must be something Good about him. Ni ina ganin Mommy give him a chance, you might even like him too"

Bayan sun gama wayar Mommy ta jima a zaune tana digesting maganganun Hafsat, tasan Hafsat tsintar kalmomi tayi wajan yi mata bayani amma abinda take so ta gaya mata shine 'she is too strict' kuma tasan haka ne, takurawar ta da son su zama perfect ne ya saka Moon take zuwa gurin Sultan a boye. Yanzu badan Allah ya kare mata yarinyar bama da sai dai ta ganta da ciki ta rasa a ina sa samu. She was wrong before, but now she is going to correct her mistakes. Ta tashi ta kwashe kayan abincin da ta gama ci ta fita dasu kitchen, babu kowa a palon duk sun fita, ta koma daki ta sake wani wankan tayi shiri na musamman, she is going to take back her family. Tana jin Daddy yazo ya wuce ta gaban dakinta amma ko lekowa bai yi ba, sai da ta bari ya dan jima da shiga sannan ta bi bayansa. Tana shiga taga ya fito daga wanka da towel a jikin sa yana kokarin shiryawa, kallo daya yayi mata ya dauke kansa, ta zagayo gabansa ta dauko mansa ta fara kokarin shafa masa, ya ture ta ya matsa, ta ajjiye man ta dauko turarensa ta biyo shi inda yake kokarin saka pajamas dinsa ta karasa saka masa ta fara fesa masa turaren hannunta, ture ta ya sake yi ya tafi kan gado yana shirin kwanciya, ta saka hannayenta ta baya ta rungumo shi, ya chire hannun nata ya matsa. Ta shagwabe fuskar ta kamar zatayi kuka tace "am sorry fa" bai kula taba ya hau kan gadon, ta bi bayansa ta kwanta a kirjinsa tare da sauke ajjiyar zuciya, sun jima a haka sannan a hankali ya dora hannunsa a bayanta yana shafa ta kamar mage, ita kuma ta kara narkewa a jikin sa, can kasan makogwaronsa a furta "I miss you"

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Episode One : The Beginning of the Beginning
  2. 2 Episode Two: Meet my Family
  3. 3 Episode Three: Loved by All
  4. 4 Episode Four: Moon's Sister
  5. 5 Episode five: The Strangers
  6. 6 Episode six: The Challenge
  7. 7 Episode Seven: The Thin Tall Man
  8. 8 Episode Eight: The New Imam
  9. 9 Episode Nine: Give Me a Chance
  10. 10 Episode Ten: I Don't Know
  11. 11 Episode Eleven : The Protector
  12. 12 Episode Twelve : This is Me
  13. 13 Episode Thirteen : This is Me 2
  14. 14 Episode Fourteen : The Limit
  15. 15 Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
  16. 16 Episode Sixteen : The Letter
  17. 17 Episode seventeen: Reply
  18. 18 Episode eighteen: what's Next?
  19. 19 Episode Nineteen: The Goodbye
  20. 20 Episode Twenty: The New Job
  21. 21 Episode Twenty one: Amira
  22. 22 Episode Twenty Two: Efisowa
  23. 23 Episode Twenty three: The Break up 💔
  24. 24 Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
  25. 25 Episode Twenty five: The Eclipse
  26. 26 Episode Twenty Six: A Step Further Away
  27. 27 Episode Twenty Eight : University of Oxford
  28. 28 Episode Twenty Nine: The Message
  29. 29 Episode Thirty : The Final Blow
  30. 30 Episode Thirty One: Let it go
  31. 31 Episode Thirty Two : Munnir
  32. 32 Episode Thirty Two : Mahdi
  33. 33 Episode Thirty Three: Zayed
  34. 34 Episode Thirty Four : Back to Square One
  35. 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
  36. 36 EpisodeThirtySix: Interesting
  37. 37 Episode Thirty Seven : The Dinner
  38. 38 Episode Thirty Eight : The Shadow
  39. 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2
  40. 40 Episode Forty :TheShadow 3
  41. 41 Episode Forty One : Born for This.
  42. 42 Episode Forty Two : Born for This
  43. 43 Episode Forty Three: America
  44. 44 Episode forty four : America 2
  45. 45 Episode Forty Five : The Rush
  46. 46 Episode Forty Six : The Repentance
  47. 47 Episode Forty Seven : Amir
  48. 48 Episode Forty Eight : Awkward
  49. 49 Episode Forty Nine : Ya Habeeb
  50. 50 Episode Fifty : Munir 2
  51. 51 Episode Fifty one : Mommy
  52. 52 Episode Fifty Two : The Journey
  53. 53 Episode Fifty Three : Daddy
  54. 54 Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
  55. 55 Episode fifty five : Her Father's Daughter 2
  56. 56 Episode Fifty Six : What You Sow
  57. 57 Episode Fifty Seven : What You Sow 2
  58. 58 Episode Fifty Eight : I Missed You
  59. 59 Episode Fifty Eight : For You, Only You
  60. 60 Episode Sixty : The Prince
  61. 61 Episode Sixty One : Save the Date
  62. 62 Episode Sixty Two : The Manager
  63. 63 Episode Sixty Three : Amira 3
  64. 64 Episode Sixty Four : The Past and the Future
  65. 65 Episode Sixty Four : The Visitors
  66. 66 Episode Sixty Six : The Wedding
  67. 67 Episode Sixty Seven : The Wedding 2
  68. 68 Episode Sixty Eight : The Wedding Night
  69. 69 Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
  70. 70 Episode Seventy : The Wedding Night 3
  71. 71 Episode Seventy One : The Honeymoon
  72. 72 Episode Seventy Two : My Everything
  73. 73 Episode Seventy Three : His Father's Son
  74. 74 Episode Seventy Four : The Cook
  75. 75 Episode Seventy Five : The Emir
  76. 76 Episode Seventy Six : The Visitors
  77. 77 Episode Seventy Seven : Amina
  78. 78 Episode Seventy Eight : The Storm
  79. 79 Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
  80. 80 Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
  81. 81 Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
  82. 82 Episode Eighty Two : The Light
  83. 83 Episode Eighty Three : The News
  84. 84 Episode Eighty Four : Little Love
  85. 85 Episode Eighty Five : Ibrahim
  86. 86 Episode Eighty Six : The Phone Call
  87. 87 Episode Eighty Seven : Riyadh
  88. 88 Episode Eighty eight :Khairat
  89. 89 Episode Eighty Nine : Khairat 2
  90. 90 Episode Ninety : His Mother's Son
  91. 91 Episode Ninety One : His Mother's Son 2
  92. 92 Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
  93. 93 Episode Ninety Four : RIP
  94. 94 Episode Ninety Five : The Light
  95. 95 Episode Ninety Six : The New Bride
  96. 96 Episode Ninety Seven : The Real Prince
  97. 97 Episode Ninety Eight: My Baby
  98. 98 Episode Ninety Nine : New Little Love
  99. 99 Episode Hundred : Not The End.