Chapter 15
Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
Da kyar na samu na lallaba hafsat ta koma seat dinta ta zauna. Har aka tashi muka koma Hostel bata yiwa kowa magana ba. Tunda taje hostel ta kwanta take kuka har lokacin islamiyya bata fito daga daki ba, ni kuma ban zauna bata hakuri ba amma sam ranar ban fita gurin Ibrahim ba. Da dare yayi saina samu kaina da kin zuwa islamiyya. Nasan ba Ibrahim ne ya daki Hafsat ba amma still ina ganin duk a sanadin alakata da shi ne komai ya faru.
Sai da na gama shiri zan kwanta sannan nazo kan gadon Hafsat na zauna na fara yi mata magana da harshen fulatanci. "Hafsat nasan yadda kike ji a ranki yanzu, kina jin tamkar duniya duka ta juya miki baya amma ina so ki sani ba haka bane. Ita duniya tana zuwa maka ne a yanda ka dauke ta, inka dauke ta da zafi to babu shakka zata zo maka da zafi. Ina so ki san cewa ni bani da komai a raina a game dake sai alkhairi, bana miki fatan komai sai na alkhairi, ban taba rukon ki a raina ba kuma kema ina rokon yafiyar ki idan na taba yi miki wani abu. Please Hafsat tunda muke ban taba neman alfarma a gurinki ba, dan Allah wata alfarma nake nema as a sister, idan kika yi min wannan nayi alkawarin bazan sake rokon wani abu a gurinki ba, please ina so komai ya wuce dan Allah kiyi abinda mommy tace, kizo muke yin karatu tare da Ibrahim, I assure you you will like him. Please sister just give us a chance" duk maganganun da nake bata cemin komai ba amma ni na tabbatar tana jina. Na tashi naje na kwanta nayi adduoi nayi bacci. Washegari ma duk mu biyun bamu je islamiyya ba, nayi wanka ina saka uniform sai ga Hafsat ta fito daga wanka ta bude fridge ta dauko fresh milk tana sha sai ta miko min tace "do you want some?" Nayi murmushi na karba nace mata "thank you" daga nan muka shirya muka fita class tare. Tun daga lokacin muka daidaita da Hafsat, muka koma yin alamuran mu kamar da. Hafsat ta fara zuwa gurin karatun mu da Ibrahim sai dai ba kullum ba, in taje su kan danyi magana kadan ba sosai ba.
Shakuwa ce sosai take shiga tsakanina da Ibrahim. Kullum muna tare tun daga 3pm har magrib. Kofar library ya zama permanent gurin zaman mu. Abin mamaki shine, kusan duk interest din mu daya; a duk subject nafi son maths shima haka, sport din da nake yi shi ne basketball kawai ranar sport shima sai na ganshi a gurin basketball, duk kanin mu muna da fara'a da surutu kuma bamu da fada. Kullum in aka tashi daga class Ibrahim sai ya rakani har bakin hostel, haka zalika in aka tashi daga islamiyya ta dare ko ta assuba sai ya rakoni har sai na shiga hostel sannan zai koma. Tun ana min surutu ina damuwa har na saba. Zan iya cewa kusan komai na Ibrahim na sani, duk wani abu da yayi idan bama tare in muka hadu sai ya bani labari. Rannan muna zaune a gurin zaman mu sai sister dinsa ta kira shi a waya, ya dauka suka fara hira da yarabanci, ni sai abin ya bani dariya saboda ban taba jin yana yarabanci ba dan har manta wa nake yi shi yaroba ne, daga dukkan alama fada yake mata. Sai da suka gama sannan ya miko min yace mu gaisa, na karba tare da yi mata sallama ta amsa min da accent din yaroba. Muka gaisa babu yabo babu fallasa na mika masa wayar sukayi sallama ya kashe. Nace masa "what is her name?" Yace "Maryam" na sake tambaya "how old is she?" Yace "23" sai a lokacin na sake realising age gap din da yake tsakanina da Ibrahim. Nan yake bani labarin cewa maganar auren ta ne ya taso, ta kawo miji step father dinsu baiyi approving ba shine take so shi Ibrahim din ya shiga cikin maganar shi kuma yaki. Anan na fahimci cewa Ibrahim yana mugun yiwa step father dinsa biyayya like shi yake da final say a duk abinda ya shafesu.
Ibrahim sam ba mai yawan abokai bane dan ban taba ganinsa ko jin sa yana waya da wani aboki ba. Rannan mun tashi daga islamiyya. Nace " why aren't you going into town? Yace "I have nothing to do in town, ni ban san kowa a garin nan ba, school din nan ta bani gurin zama a cikin quarters, tana bani abinci kullum" ya tsaya da tafiya ya juyo yana kallona "and you are here also, so mai zai kaini cikin gari?" Nayi murmushi naji dadi har cikin raina nace "amma tunda har kazo Abuja, why not baza kayi using this chance ba ka ga gari, it is a very nice town, besides, u never know wa zaka hadu dashi a cikin garin. Ka sani ko kayi budurwa. Dariya yayi sosai yana kallona da lumsassun idanuwansa, ya langwabe kai gefe kamar mai shirin yin shagwaba yace "ni nayi kankanta da yin budurwa. Baki ganin ni yaro ne" yadda yayi maganar ne ya bani dariya nima nace "yaro a ina? I thought 25years kake? To in bakayi budurwa ba sai ka fara furfura tukunna? Ya kalleni da serious look yace "Allah da gaske nake bani da budurwa, sai later, da nace sai na gama service amma yanzu ina tunanin anya zan iya jira kuwa? In na tsaya wasa zuciya ta zata iya fitowa daga kirjina" yadda yake maganar a hankali da yanayin da yake kallona yasa naji tsigar jikina tana tashi. Banyi aune ba sai ji nayi Amira ta kama hannuna tana jana gefe tare da cewa "to love birds, times up, goodnight sir, sleep tight " da sauri da sauri take jana muna tafiya hostel ni kuwa har yanzu ido na a kansa suke shima kuma ni yake kallo, sai da muka je bakin gate din hostel sannan naga yayi min alamun 😘 nayi sauri na dauke kaina ban kuma kallon inda yake ba. Muna shiga hostel Amira ta jani gefe "what are you doing Moon? Kinga kallon da yake miki kuwa? Shaidan fa is real komai iliminsa kema kuma komai kame kanki da saka hijabin ki ba guarantee bane na cewa shaidan ba zai yi nasara akan ku ba" raina ya baci da accusation din Amira nace mata "Amira mutumin nan fa ba saurayina bane, we are just friends, sannan kuma bama kebewa mu kadai ni dashi, kullum a waje muke inda kowa zai gan mu" tace "ni ban taba ganin inda saurayi da budurwa za'a keyin friendship ba, you are deceiving yourselves, ko makaho ya shafa fuskokin ku yasan cewa something is there" nace "saurayi da budurwa kika ce. He maybe saurayi amma ni ba budurwa bace" tayi min kallon sama da kasa tace "oh ke 'yar jaririyace kenan ko? Ji nake yanzu haka ma period kike yi? Wanne girma kuma zakiyi nan gaba bayan already hormones din adolescent sun fara aiki a jikin ki. You are a woman now whether you are full breasted or not, dole akwai attraction tsakanin ki da shi" nayi sauri nace mata "am not attracted to him" tace "really? " tayi tafiyarta ta barni.
Table of Contents
Chapters
- 1 Episode One : The Beginning of the Beginning
- 2 Episode Two: Meet my Family
- 3 Episode Three: Loved by All
- 4 Episode Four: Moon's Sister
- 5 Episode five: The Strangers
- 6 Episode six: The Challenge
- 7 Episode Seven: The Thin Tall Man
- 8 Episode Eight: The New Imam
- 9 Episode Nine: Give Me a Chance
- 10 Episode Ten: I Don't Know
- 11 Episode Eleven : The Protector
- 12 Episode Twelve : This is Me
- 13 Episode Thirteen : This is Me 2
- 14 Episode Fourteen : The Limit
- 15 Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
- 16 Episode Sixteen : The Letter
- 17 Episode seventeen: Reply
- 18 Episode eighteen: what's Next?
- 19 Episode Nineteen: The Goodbye
- 20 Episode Twenty: The New Job
- 21 Episode Twenty one: Amira
- 22 Episode Twenty Two: Efisowa
- 23 Episode Twenty three: The Break up 💔
- 24 Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
- 25 Episode Twenty five: The Eclipse
- 26 Episode Twenty Six: A Step Further Away
- 27 Episode Twenty Eight : University of Oxford
- 28 Episode Twenty Nine: The Message
- 29 Episode Thirty : The Final Blow
- 30 Episode Thirty One: Let it go
- 31 Episode Thirty Two : Munnir
- 32 Episode Thirty Two : Mahdi
- 33 Episode Thirty Three: Zayed
- 34 Episode Thirty Four : Back to Square One
- 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
- 36 EpisodeThirtySix: Interesting
- 37 Episode Thirty Seven : The Dinner
- 38 Episode Thirty Eight : The Shadow
- 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2
- 40 Episode Forty :TheShadow 3
- 41 Episode Forty One : Born for This.
- 42 Episode Forty Two : Born for This
- 43 Episode Forty Three: America
- 44 Episode forty four : America 2
- 45 Episode Forty Five : The Rush
- 46 Episode Forty Six : The Repentance
- 47 Episode Forty Seven : Amir
- 48 Episode Forty Eight : Awkward
- 49 Episode Forty Nine : Ya Habeeb
- 50 Episode Fifty : Munir 2
- 51 Episode Fifty one : Mommy
- 52 Episode Fifty Two : The Journey
- 53 Episode Fifty Three : Daddy
- 54 Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
- 55 Episode fifty five : Her Father's Daughter 2
- 56 Episode Fifty Six : What You Sow
- 57 Episode Fifty Seven : What You Sow 2
- 58 Episode Fifty Eight : I Missed You
- 59 Episode Fifty Eight : For You, Only You
- 60 Episode Sixty : The Prince
- 61 Episode Sixty One : Save the Date
- 62 Episode Sixty Two : The Manager
- 63 Episode Sixty Three : Amira 3
- 64 Episode Sixty Four : The Past and the Future
- 65 Episode Sixty Four : The Visitors
- 66 Episode Sixty Six : The Wedding
- 67 Episode Sixty Seven : The Wedding 2
- 68 Episode Sixty Eight : The Wedding Night
- 69 Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
- 70 Episode Seventy : The Wedding Night 3
- 71 Episode Seventy One : The Honeymoon
- 72 Episode Seventy Two : My Everything
- 73 Episode Seventy Three : His Father's Son
- 74 Episode Seventy Four : The Cook
- 75 Episode Seventy Five : The Emir
- 76 Episode Seventy Six : The Visitors
- 77 Episode Seventy Seven : Amina
- 78 Episode Seventy Eight : The Storm
- 79 Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
- 80 Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
- 81 Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
- 82 Episode Eighty Two : The Light
- 83 Episode Eighty Three : The News
- 84 Episode Eighty Four : Little Love
- 85 Episode Eighty Five : Ibrahim
- 86 Episode Eighty Six : The Phone Call
- 87 Episode Eighty Seven : Riyadh
- 88 Episode Eighty eight :Khairat
- 89 Episode Eighty Nine : Khairat 2
- 90 Episode Ninety : His Mother's Son
- 91 Episode Ninety One : His Mother's Son 2
- 92 Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
- 93 Episode Ninety Four : RIP
- 94 Episode Ninety Five : The Light
- 95 Episode Ninety Six : The New Bride
- 96 Episode Ninety Seven : The Real Prince
- 97 Episode Ninety Eight: My Baby
- 98 Episode Ninety Nine : New Little Love
- 99 Episode Hundred : Not The End.