Chapter 31
Episode Thirty Two : Munnir
Daddy yana gama fadin haka ya mike yayi musu sallama ya fita. Gurin kowa yayi shiru banda Hajja dake ta sambatun ta ita kadai. "Yauwa, yanzu na ji magana, amma abar yara suna so sufi karfin mutane? Yanzu kuwa zan kira 'yan samarin nan duk abinda suke yi su bari su taho gida, azo ayi ta ta kare" tsam mommy ta mike ta shige dakin da muke sauka in munzo, Hafsat ta tashi ta bita a baya, nan Hajja ta sake daukan magana "zasu je suyi kulle kullen yadda za'a fasa, ai kuwa wannan maganar kamar anyi ta an gama ne, yo gida bai koshi ba a bawa jeji?" Duk abinda take yi inna bata tanka ta ba, aikin gabanta kawai take yi. Sai da na gama taya inna juye furar da ta dama a jug na kai kitchen na saka a fridge sannan na shiga dakin mu. Dariya naji tana neman kubucemin saboda ganin yadda akayi upside down da dakin, duk su biyun sun dage suna ta loda kayan mu a akwatinan mu, wadansu kayan ma ba'a ninke suke ba haka ake watsa su. Mommy idonta ya kada yayi jawur, Hafsat kuma fuskarta kamar an aiko mata da mutuwa. Bance musu komai ba suma haka, na samu guri na zauna na zuba wa sarautar Allah ido, nan da nan mommy ta bani aikin kwashe kayan kwalliyar mu da underwears din mu. Muna cikin aikin da bansan na menene ba sai ga inna ta shigo, da mamaki take bin mu da kallo "yanzu Bintou shine kika tisa 'ya'ya a gaba kuke hada kaya zaku gudu?" Maganar guduwar da inna tayi shi ya saka dariyar da nake kunshewa ta fito, Hafsat ta bini da uwar harara hamkar idanunta zasu fado. Mommy ta yar da rigar da take ninkewa ta zauna dabas a bakin gado tace "inna yanzu zama zanyi a yiwa yaran nan auren dole, dududu nawa suke? Girman jiki ne fa kawai dasu amma ba wani shekarun kirki ne dasu ba ballantana ace sunyi kwantai za'a raba wa 'yan'uwa, wai Nuraddeen, har da Mannirun da baya ganin kowa da gashi" inna tace "ke waya ce miki za'ayi musu auren dole? Ya kike abu ne kamar ba kisan halin mijin kiba? Ni dai abinda kunne na ya jiye min yace shine 'za'ayi auren in dai har yaran sun amince a junansu' to menene kuma abin tashin hankali a ciki. Ke kinsan waye Muhammadu, kinsan babu yadda za'ayi yayi wa 'ya'yansa auren dole, amma yanzu kina diban su kuka gudu cewa zai yi ba kya son 'yan'uwansa. Ki zauna kiyi musu addu'ar zabin alkhairi shi yafi miki" tana fadin haka ta juya ta fice daga dakin.
In matsala irin wannan ta samu mutun, musamman harkar ta aure, rigima, koke-koke da tuburewa iyaye ba shine zai samar da maslaha ba, abinyi shine ka bisu a yadda suka zo maka sannan daga baya sai ka same su, ko ka samu wani wanda suke jin maganar sa kayi masa bayanin cewa kaifa baka son hadin nan. Sannan abu mafi muhimman ci shine ka yawaita addu'ah, wani baya taba auren matar wani kamar yadda wani baya taba haihuwar dan wani, rayuwar mu gaba daya a rubuce take duk abinda Allah ya rubuta sai ya faru da kai to babu tsimi babu dabara, addu'ah kadai ita ce maganin masifa. In Allah ya rubuta something bad zai faru da kai in kana yawaita addu'ar neman mafi alkhairi sai Allah ya goge ya rubuta maka something better.
Mommy ta fasa tafiya amma daga ganinta kasan ranta a bace yake, Hafsat ta kara hade gida, ni kuwa harkar gaba na nake yi saboda na yarda cewa daddy ba zai taba aura min wanda bana so ba, duk wanda yazo yace yana sona all what I have to do is in ce bana son sa, kalas.
Nuraddeen ne ya fara zuwa, very cheerful and nice guy. A falon inna ya same mu, kallo daya Hafsat tayi masa ta tashi ta shige daki, ni kuwa harda durkusawa ta ina gaishe shi, ya amsa min da fara'arsa yana tambayata labarin England da rayuwar makaranta, nan na zauna na tankwashe kafata na ringa kwararo masa labari yana dariya, shima ya fara bani labarin BUK da irin wahalar da suka sha ina ta mamakin banbancin makarantun mu na gida da kuma na waje. Sai da muka gama hirar mu ya tashi ya daga labulen cikin daki yace "Hafsat ke kuwa ko gaisawa ai kya fito muyi, ni ba cewa zanyi ina son ki ba dan kin fi karfina, in ma zaban zanyi sai dai Moon ita ce mutuniyar kirki, to amma ita kuma na dauke ta kamar kanwa ta" ina jiyo inna tana yi mata fada sannan ta fito ta gaishe shi tana kirkiro murmushin karya. Har ya juya zai fita sai yace "kun taba zuwa hadejia kuwa?" Muka girgiza kai a tare, yace "ku shirya to gobe tunda ina gari sai muje yawo ku gano fadar sarkin mu, kuga river hadejia" da murna ta nace "Allah ya kaimu, mungode Allah ya bar zumunci" daga haka ya juya ya fita, Hafsat tabi bayansa da harara. Yana fita ta kama kunnena ta rike "maza ki zauna kiyi ta wangale musu baki, in aka aura miki daya ni ko gidanki bazan ke zuwa ba" . Washegari kuwa mukaje hadejia da yaya Walid, nuraddeen da kuma mu uku har Amina. Munyi yawo sosai a garin, ya nuna mana duk guraren tarihi, hatta Hafsat ta ware muna ta hirar mu ta zumunci, a hanyar dawowa ne yake bamu labarin budurwarsa 'yar kano, tana karatu a BUK, bai kai maganar gurin iyaye ba saboda yana so sai ta kammala tukun. Hafsat tana jin haka ta sake warewa tana yi masa hira. Da zamu dawo gida ya sayo mana balangu mai uban yawa. Har zamu shiga gida sai ya kirani na dawo, seriousness na gani a fuskar sa nima na nutsu, yace "naji Hajja tace ta kira munnir shima, in yazo kar ki yadda ki sakar, masa fuska, bashi da kirki ko kadan kuma bashi da kunya" na gyada masa kai da sauri alamar na fahimta, daga haka na shige gida. Balarabe bai zo ba, sai yayo waya ta wayar inna wai shi ba zai samu damar zuwa 'yalleman ba sai dai a turo masa hotunan mu ta waya ya zaba. Nan inna ta haushi da bala'i "an gaya maka su atamfofi ne da zaka wani ce a turo maka hotuna ka zaba, aikin banza, ai ba neman kai muke yi dasu ba" ta inda take shiga bata nan take fita ba. Mommy tace "good riddance" nima kaina sai da maganar tasa ta bani haushi, lallai ma wannan mutumin, me ya dauke mune? Duk hajja ce ta jawo mana wannan wulakancin.
Shi ogan bai zo ba sai ana ya gobe zamu tafi, muna dakin inna Hafsat ta shigo tana bata fuska tace "wannan dan iskan ne yazo, I was hoping ba zai zo ba, ganinsa ma kawai yayi spoiling mood dina ballantana yin magana dashi" mommy tana jin haka tace "wai munnir din ne yazo?" Hafsat tace "eh shi fa, yana dakin hajja" mommy ta watsomin wani kallo tace "behave your self" bata ce da Hafsat komai ba saboda tasan halin abarta. Duk muna bedroom din mu ya shigo palon, tun daga daki muka jiyo kamshin turarensa. Hafsat ta kwanta taja bargo. Ina jinsu suna gaisawa da mommy da inna, yana tsokanar inna wai kullum kara kyau take ko ita zai zaba ne. A raina nace "oh ni 'yar nan, me hajja ta mayar damu ne? Kashin dankali?" Naji inna ta kalla mana kira wai muzo mu gaishe shi. Na dauki mayafi na na yafa na kalli Hafsat naga ta rufe ido. Ina fita palon mommy ta tashi ta shige daki tana harara ta, inna ma tace bara taje kitchen ta duba abinci. Kallo daya nayi masa na fahimci abinda Nuraddeen yake nufi da yace inyi a hankali dashi. Kallo daya nayi masa naji sam bai yi min ba. Tun daga sama yake kallona har kasa. Inna tana rufe kofa yace "damn, wai mafarki nake yi ne ko gaske ne Moon ce ta zama haka? Ni da hajja ta kira ni ina mita za'a hada ni da 'yar tsakuwa ashe kin zama dakwalwar kaza?" Binshi kawai nake da kallo, wannan me yake nufi ne? Sai a lokacin nayi nadamar saka mayafi ba hijab ba. Ya nuna min kan handle din kujerar da yake kai yace "come sit with me" lallai wannan duk inda nake tunanin sa ya wuce nan. Na tafi kujerar da take opposite dinsa na zauna ina gyara lullubi na. Tsam naga ya taso ya dawo handle din kujera ta ya zauna yana cewa "meye kuma na wannan uban lullubin, ni da nazo in ganki kuma in kika rufe me zan gani kenan?" Ya fada yana kokarin sauke min lullubi na. Na mike tsaye ina kallonsa. Kyakykyawa ne ba karya, dan gayu ne na azo a gani, haihuwa da rainon legas. Baban su shine babba a gurin baffa, kuma shi yake kula da business din baffa a lagos. Acan aka haifesu duk, kuma acan suka girma. Bafulatani ne gaba da baya. Ya riko gefen rigata "ina zaki je kuma ko gaisawa ba mu yi ba?" Na kalleshi a raina nace "yau dole in dauki page a cikin littafin Hafsat" na watsa masa wata hararar da bansan na iya taba, nace "don't you dare try to touch me again, in kana so mu gaisa ka koma kujerar da ka taso daga kai, in ba haka ba bazan kara second daya anan ba" ya mike yana wani shagwabe fuska yace "i can't help it wallahi, you are so beautiful" na wuce na zauna tare da hade girar sama da ta kasa irin yadda Hafsat take yi nace "ina wuni" cikin wata irin murya yace min "lafiya lau sweetheart, ya England? Nima nace "lafiya" a ta kaice. Daga nan ya fara min labarin irin kudin da yake samu, sabuwar motar da ya saya, irin yadda yake shanawa a lagos, ni dai duk ina jinsa, sai da na gaji na mike nace "bara in kirawo maka Hafsat", shima ya mike tare da cewa "there is no need, I have already made my choice" daga nan ya ajiye rafar 'yan dubu dubu akan santa table, ya sakar min wani kasalallen murmushi ya fice.
Table of Contents
Chapters
- 1 Episode One : The Beginning of the Beginning
- 2 Episode Two: Meet my Family
- 3 Episode Three: Loved by All
- 4 Episode Four: Moon's Sister
- 5 Episode five: The Strangers
- 6 Episode six: The Challenge
- 7 Episode Seven: The Thin Tall Man
- 8 Episode Eight: The New Imam
- 9 Episode Nine: Give Me a Chance
- 10 Episode Ten: I Don't Know
- 11 Episode Eleven : The Protector
- 12 Episode Twelve : This is Me
- 13 Episode Thirteen : This is Me 2
- 14 Episode Fourteen : The Limit
- 15 Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
- 16 Episode Sixteen : The Letter
- 17 Episode seventeen: Reply
- 18 Episode eighteen: what's Next?
- 19 Episode Nineteen: The Goodbye
- 20 Episode Twenty: The New Job
- 21 Episode Twenty one: Amira
- 22 Episode Twenty Two: Efisowa
- 23 Episode Twenty three: The Break up 💔
- 24 Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
- 25 Episode Twenty five: The Eclipse
- 26 Episode Twenty Six: A Step Further Away
- 27 Episode Twenty Eight : University of Oxford
- 28 Episode Twenty Nine: The Message
- 29 Episode Thirty : The Final Blow
- 30 Episode Thirty One: Let it go
- 31 Episode Thirty Two : Munnir
- 32 Episode Thirty Two : Mahdi
- 33 Episode Thirty Three: Zayed
- 34 Episode Thirty Four : Back to Square One
- 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
- 36 EpisodeThirtySix: Interesting
- 37 Episode Thirty Seven : The Dinner
- 38 Episode Thirty Eight : The Shadow
- 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2
- 40 Episode Forty :TheShadow 3
- 41 Episode Forty One : Born for This.
- 42 Episode Forty Two : Born for This
- 43 Episode Forty Three: America
- 44 Episode forty four : America 2
- 45 Episode Forty Five : The Rush
- 46 Episode Forty Six : The Repentance
- 47 Episode Forty Seven : Amir
- 48 Episode Forty Eight : Awkward
- 49 Episode Forty Nine : Ya Habeeb
- 50 Episode Fifty : Munir 2
- 51 Episode Fifty one : Mommy
- 52 Episode Fifty Two : The Journey
- 53 Episode Fifty Three : Daddy
- 54 Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
- 55 Episode fifty five : Her Father's Daughter 2
- 56 Episode Fifty Six : What You Sow
- 57 Episode Fifty Seven : What You Sow 2
- 58 Episode Fifty Eight : I Missed You
- 59 Episode Fifty Eight : For You, Only You
- 60 Episode Sixty : The Prince
- 61 Episode Sixty One : Save the Date
- 62 Episode Sixty Two : The Manager
- 63 Episode Sixty Three : Amira 3
- 64 Episode Sixty Four : The Past and the Future
- 65 Episode Sixty Four : The Visitors
- 66 Episode Sixty Six : The Wedding
- 67 Episode Sixty Seven : The Wedding 2
- 68 Episode Sixty Eight : The Wedding Night
- 69 Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
- 70 Episode Seventy : The Wedding Night 3
- 71 Episode Seventy One : The Honeymoon
- 72 Episode Seventy Two : My Everything
- 73 Episode Seventy Three : His Father's Son
- 74 Episode Seventy Four : The Cook
- 75 Episode Seventy Five : The Emir
- 76 Episode Seventy Six : The Visitors
- 77 Episode Seventy Seven : Amina
- 78 Episode Seventy Eight : The Storm
- 79 Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
- 80 Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
- 81 Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
- 82 Episode Eighty Two : The Light
- 83 Episode Eighty Three : The News
- 84 Episode Eighty Four : Little Love
- 85 Episode Eighty Five : Ibrahim
- 86 Episode Eighty Six : The Phone Call
- 87 Episode Eighty Seven : Riyadh
- 88 Episode Eighty eight :Khairat
- 89 Episode Eighty Nine : Khairat 2
- 90 Episode Ninety : His Mother's Son
- 91 Episode Ninety One : His Mother's Son 2
- 92 Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
- 93 Episode Ninety Four : RIP
- 94 Episode Ninety Five : The Light
- 95 Episode Ninety Six : The New Bride
- 96 Episode Ninety Seven : The Real Prince
- 97 Episode Ninety Eight: My Baby
- 98 Episode Ninety Nine : New Little Love
- 99 Episode Hundred : Not The End.