Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 57

Episode Fifty Seven : What You Sow 2

Maimoon Book 1 Complete Hausa Novel 2,783 words 0 views Progress saved
Download Book

A 'yalleman kuwa tunda Munir yayi wa Hajja waya da sassafe ya hada mata karya da gaskiya ya gaya mata. Suna gama wayar ta fita daga part dinta ta tsaya a compound ta rafka wani uban salati "na shiga uku ni zuwaira yau wanne mugun labari zanji haka" a tare da baffa da inna suka fito daga part dinsa suna tambayarta "lfy? Me ya faru? Waye ya mutu?" Ita kuwa kuka take tana fyace majina da bakin zanin ta, "dama babu abinda ban fada ba aka ki daukan magana ta saboda bani na haifi muhammadu ba kuma shine dan gatan gidan nan, dama gata ai mugun abu ne, babu abinda yake haifarwa sai nadama. Wanda duk baiji bari ba ko ai zai ji oh'oh" inna tana jin zancen muhammadu ta ja da baya ta tsaya tana jiran taji alkaba'in da zai biyo baya. Baffa ma bari yayi sai da hajja ta gama sambatun ta sannan ya kuma tambayarta "me ya faru da muhammad din" Hajja ta duba taga duk yaran gida sun taru a compound suna sauraren abinda ake yi sannan tace "yaran nan babu yadda banyi ba akan ayi musu aure akaki, aka nuna min ban isa ba, to yanzu gashi nan abinda ake gudu ya faru. Manniru ne yayo min waya dazu hankalinsa a tashe, yace tunda yarinyar nan ta dawo kasar nan ta juya masa baya, in yaje gidan nasu sam ba'a barin shi ya ganta, in ya kira ta a waya bata dauka, to jiya da daddare wajan karfe daya ya fita neman abinci saboda yaje gidan sun hana shi abinci shi kuma yunwa ta dame shi, kawai yaga yarinyar nan a titin Allah tana yawo da dan skirt, ta sha giya tayi mankas ko tafiya bata iyayi sai wadansu maza ne suka rirriketa, shima kansa da kyar ya gane ta, kuma ya kira walid ya gaya masa, ashe sun riga sun san halin da yarinyar take ciki shi yasa basa barin ya ganta. Daya bisu gidan ya na tada maganar saboda ayi wa tubkar hanci sai walid da habibu suka taru suka yi masa dukan tsiya suka ce in dai ya sake ya fada wa mutane sai sun nakasa shi" wani irin jiri inna taji yana neman daukan ta, wannan wanne irin sharri ne munir ya shirya wa maimunatu? Palon ta ta koma ta zauna kanta yana bala'in sara mata, yaran gidan kuwa tunda suka gama jin abinda hajja tace suka fara fita daya bayan daya suna shiga makota kai rahoto, baffa kasa cewa komai yayi dan shima jirin ne yake dibansa, Ma'aruf dan autan hajja wanda kuma shi kadai ne ya rage a gidan ne yayi saurin dauko kujera ya zaunar da baffa. Sai da baffa ya mayar da numfashin sa sannan yace "hajja kin tabbatar munir ba karya yayi miki ba?" Hajja ta matso kusa dashi tace "yaya zaiyiwa yarinyar da yake so karya? Ita fa ya zaba ta zama uwar 'ya'yansa ta yaya zai yi mata sharri kuma? Ban taba ganin so na gaskiya irin wanda yaron nan yake yiwa yarinyar nan ba, duk da abinda ya gani da idanuwansa fa cewa yayi shi so yake ma a gaggauta auren ko Allah zai sa auren ya gyara ta" still zuciyar baffa taki yarda da maganganun hajja, yana kallon fuskar maimunatu a zuciyarsa, duk acikin jikokinsa yana son 'ya'yan muhammadu, kuma duk a 'ya'yan muhammadu maimunatu ta daban ce, ga tarbiyya, ga ladabi, ga fara'a, ga shiga ran mutane sannan uwa uba ga son 'yan'uwanta. Sam bata da girman kan wai babanta wani ne, duk sanda tazo sai ta zaga 'yan'uwa kai hatta 'yan aikin gidan nan kawayenta ne dan wani lokacin a cikin su zai ganta tana wasa. Hajja ta tankwashe kafar ta ta cigaba da zuba zance "ya gayamin ai ba laifin ta bane, wani yaro ta hadu dashi lalatacce shine ya bata ta, su kuma iyayen sun dauki son duniya sun dora mata shi yasa suka kasa raba su, dan ce musu tayi ko yanka ta za suyi ba zata rabu da yaron ba. Ni dai shawara ta shine, ka kira muhammadu ka gaya masa zama maza ya kawo mana yarinyar nan gurin mu, tana zuwa sai mu sata a lalle ayi auren nan kowa ya huta. Shi kuma wannan yaron da yace yaji ya gani zai aure ta a haka Allah yayi masa albarka" baffa da har yanzu kansa bai gama juya masa ba ya aika ma'aruf ya dauko masa wayarsa, amma maimakon ya kira muhammadu kamar yadda hajja tace, sai ya kira Aliyu, aliyu yana dauka ko gaisawa basu yi ba yace "Aliyu kaga abinda ka jawo mana ko? Taurin kanka ne ya hana ayi auren nan da yanzu duk wannan abin bai faru ba, to kasani ni babu ruwana, tunda kai ka jawo sai kasan yadda zakayi ka warware" yana kaiwa nan ya kashe wayar ya mike ya shige dakinsa, hajja ba haka taso ba dan tasan Aliyu sam ba zai taba goyon bayan munir ba, saboda kamar yadda take fada tace ya tsane shi saboda ba uwarsu daya da wanda ya haife shi ba. A bangaren inna kuwa tana shiga dakinta ta dauko wayarta ta kira mommy, sai da ta katse ta sake kira sannan mommy n ta dauka, itama ba tare da sun gaisa ba tace "Fatima me ya faru tsakanin manniru da maimunatu?" Cikin inda inda mommy tace "inna babu komai wani abu akace ya faru?" Inna ta bata rai sosai tace "Fatima dani fa kike magana ba da wani ba, cewa nayi me ya faru tsakanin munir da moon?" Mommy kuma sai kuka, sai da tayi me isarta sannan ta bawa inna labarin duk abinda ya faru a lokacin. Inna salati ta saka tace "amma fatima ya za'ayi ace yarinya tana tare da saurayi har tsahon shekara guda amma ke a matsayinki na mahaifiyarta baki sani ba?"Mommy tace "inna wallahi nasan tana tare da wani, amma bansan ko waye shi ba, da nasan yaron nan ne wallahi da tuni na raba su. Ita yarinyar nan kinsan halinta, har cikin zuciyarta gani take taimaka masa take yi" nan inna ta gaya mata duk abinda hajja take fada, mommy sai da ta sake wani kukan sannan tace "wallahi inna ba haka akai ba" kafin ta cigaba da magana inna ta katseta tace "na sani ai, ni nasan maimunatu, nasan abinda zata aikata da wanda ba zata yi ba. Yanzu dai zamu jira muji abinda baffa zai ce" Suna gama wayar uncle Aliyu yana kiran inna, saboda kiran da baffa yayi masa, tambayarta ya shiga yi akan menene ya faru, nan inna tayi masa bayani, nan take ransa ya baci yace sai ya babballa munir, da kyar inna ta lallabashi, maganar yaron da akace suna tare da moon kuma yace zaije har abujan yayi bincike yaji me ake ciki, saboda yasan da maganar yaron da moon tace masa tana so, tace masa dan sarki ne, kuma yasan akwai dan sarkin abuja tantiri. Da kadan da kadan magana take watsuwa ya a garin yalleman, amma ga mamakin hajja duk wanda aka gayawa maganar tun kafin a karasa ma yake cewa karya munir yake yi, da yawa daga cikin 'yanuwa cewa suke yi dan yaga har yanzu bata sonsa ne shi yasa zai yi mata sharri dan ayi mata dole, kowa yasan halin maimunatu kuma kowa yasan halin munir, shi halinka kuma shine jarinka, mutane kuma sune rahamarka. Shi yasa bature yake cewa 'it is good to be good' ni kuma nace 'it pays to be good'

Uncle Aliyu bai samu zuwa abuja ba saboda aiyuka da suka yi masa yawa sai bayan sati biyu, yana zuwa baije gidan ba ya sauka a hotel, yaje unguwar a wayance yake tambayar mutane abinda suka sani tsakanin sultan da moon, amsoshin da yake samu sam basu yi masa dadi ba. A karshe dai ya kira ambassador inda shi kuma ya gaya masa ai yana gari ma. Da yamma yaje gidan, a compound ya tarar da ambassador tare da walid da kuma wani kyakykyawan yaro sun saka kaya iri daya shi da walid, har ya zauna yana kallon yaron dan sam bai san shi ba, suka gaishe shi tare shi da walid, uncle Aliyu ya dan tsokani walid sannan suka shiga gida. Sai a lokacin ya gaishe da yayan nasa, sannan yace "wannan yaron kuma fa yaya a ina ka samo shi?" Fuskar ambassador dauke da murmushi yace "Sultan sunan sa, shine babban dan mai martaba sarkin Abuja" da mamaki uncle Aliyu ya kalleshi yace "Sultan? Sultan din moon?" Daddy shima da mamaki yace "kasan shi ne?" Uncle aliyu yace "a'a bansan shi ba. Amma maganar sa ce ta kawo ni abuja. Sai dai kuma yadda ake gaya min labarinsa ba haka na ganshi ba" daddy ya gyada kai cikin gamsuwa yace "ai ba haka din yake ba, yanzu ne ya zama haka" nan ya fara bashi labarin sultan dalla dalla, a karshe yace "labarin yaron ne ya saka naji tausayinsa kuma nayi alkawarin gyara masa yaruwarsa" uncle Aliyu yanu tausayin rayuwar sultan sosai, amma duk da haka sai yace "gaskiya yaron abin tausayi ne, amma duk da haka yaya kana ganin ya dace mu dauki maimunati mu bawa yaron da yake da past kamar nashi?" Daddy ya gyara zama yace "shi aure wannan nufin Allah ne, yanzu ba maganar auren su ake ba tukunna, maganar chanzawa yaron yaruwa ake yi. Kuma ni sam ba domin maimunatu nake yi ba, ko da ace a yanzu sultan zai ce ya fasa auren moon to ba zan fasa ko daya daga cikin abubuwan da nayi niyyar yi masa ba". Suna cikin maganar sai ga sultan ya fito daga part dinsu, ya chanza wanka, yazo kusa da daddy ya durkusa yana shafa kansa yace "daddy zan dan fita" daddy yace "OK, Allah ya tsare. Make sure ka dawo kafin dinner" sultan yayi dariya yace "I won't miss it for the world" shima daddyn dariya yayi sanin halin sultan akan abinci, Sultan yayi wa uncle Aliyu sallama sannan ya fita. Har lokacin dinner uncle Aliyu yana nan, sosai yaji yana missing moon amma daddy yace kar ya kula mommy akan maganar ta, a dinner din duk su Habeeb har daddy suka saka sultan a gaba da tsokana shi kuwa ko a jikinsa sai zuba lomarsa yake yana kuma zuba surutu, sai dai in sun hada ido da uncle Aliyu ya dan sunkuyar da kai alamar kunya. Nan take uncle Aliyu yaji sultan ya shiga ransa saboda Sultan yana da shiga rai kamar Moon.

Daga Abuja direct yalleman uncle Aliyu ya koma, ya samu baffa ya tabbatar masa da cewa duk maganganun Munir karya ne, yace masa kawai yayi mata sharri ne dan yana so a tirsasa ta ta aure shi. Ai kuwa da baffa ya tisa munir a gaba da fada kamar zai dake shi da kansa, dan har hajja sai da fadan ya shafe ta. Shi dai munir yasan ba duk maganar sa ce karya ba, akwai 'yar gaskiya a ciki, amma fur kowa yaki sauraronsa. Yana fita waje kuwa suka kwashi 'yan kallo da nuraddeen wanda tun da yaji maganar yace wallahi duk sanda munir ya shigo gari sai jikinsa ya gaya masa tunda yayi wa Moon sharri irin wannan. Kaikayi ya koma kan mashekiya.

Wannan kenan;

Sultan yana kwance a daki daddy ya kira shi, ya daga da sallama, daddy yace masa "Maza ka shirya ka fito zamu tafi Niger mu dauko Moon" rasa masar da zai bayar yayi dan ji yayi komai ya tsaya masa, sai da daddy yace "kaji abinda nace kuwa?" Da sauri yace "yes, daddy" ya mike yana tunanin anya yaji abinda yace din kuwa? Ya daiji kamar ance Niger kuma ance Moon, sai a lokacin tunanin shi ya dawo, Moon zadu je su dauko a Niger, what? It means yau zai ganta kenan? Wani tsalle yayi ya sauko daga kan gado ya fito palo yana neman walid dan yayi confirming maganar, yana fitowa walid yana shigowa da sauri, ya kalle shi yace "a haka zaka je dauko amaryar taka" Sultan ji yayi kamar kafafuwan sa ba zasu dauke shi ba, da gudu ya koma daki, sai kuma gashi ya sake fitowa da gudu yace wa walid "yau zamu dawo ko kwana zamu yi?" Walid ya duba agogonsa yace "sai dai mu kwana ai, it is already late, dan dai daddy ya matsa tafiyar nan ne amma da mun bari kawai sai da safe" Sultan bai ji karashen maganar ba ya koma dakin, ba'afi minti biyar ba sai gashi ya fito ya shirya da jaka a hannunsa, babu walid a palon dan haka ya fita waje ya saka kayansa a motar da zata kai su airport, ji yake kamar yaje ya chichchibo duk wanda za'ayi tafiyar dasu suzo su tafi, gani yake kamar duk suna sane suke lakaki. It seems like eternity kafin su mommy su fito, yana ganin ta yaji jikinsa yayi sanyi, bata taba yi masa magana ba kuma ko sun hadu a compound in ya gaishe ta bata amsawa, bai kuma taba ganin ta a palo ba shi kuma bai taba tambayar dalili ba. Yaji dadi da ba mota daya zasu shiga ba, shi da daddy, ita kuma da Walid. Sai gab da magrib suka je airport, private jet din daddy suka hau, kafin isha suka sauka a Niamey, aka kai su wani gida shi da walid suka sauka, shi dai kawai jira yake yi suje gurin moon, sai da zasu kwanta walid yake masa bayanin moon fa ba'a nan take ba, tana agadaz amma sun taho suna hanya, goben ma sai wajen azahar zasu karaso. Ranar sultan yadda yaga rana haka yaga dare, wani irin farin ciki yake ji da wani irin son Moon a ransa, sannan kuma da fargaba, what if yanzu kuma tace bata son shi? Tunda shi ya jawo mata duk wannan wahalar da ta sha, yasan tana cewa bata son shi kuma daddy zai kore shi daga gidansa. He will then be back to square one. Washegari tunda yayi breakfast yake zaune, gabansa ne kawai yake ta faduwa, sai can bayan azahar Walid ya shigo yana dariya, sultan yasan me zai ce masa "sun zo, baka je kayi mata oyoyo ba" Sultan ya zauna akan kujera yana rikr kansa, Walid yayi dariya yace "jarumtar kenan? Kar ka bani kunya mana, ni da na saka ran zaka fita a guje kaje ka ture daddy ka rungumeta?" Hararar sa kawai Sultan yayi dan shi kadai yasan me yake ji a ransa. Walid ya sake cewa "kaga ni na fita yawo, in ga kama ragwantar ka fita driver zai kaika inda suke, zan same ku a can" Sultan bai iya fita ba har sai da daddy ya kira shi a waya yace sun kusa gama wa fa, su zo su same su. Da sauri ya dan watsa ruwa ko zaiji garau, ya chanja kaya yana kallon kansa a mudubi, maybe ma cewa zata yi bai yi kyau ba, ya chire hular ya ajiye sai kuma ya sake dauka ya dora. Sai kuma yaji haushin kansa, me yasa yake nin tsoron wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ne. Koma me zata ce ta fada din. Ya fita aka kai shi can gidan, ya fito ya jingina da jikin mota yana jiran fitowar su, wayarsa ya dauko yana daddan nawa amma sam ba wai yasan abinda yake yi bane, ji yayi ana kallon sa, kuma har cikin jinin jikin sa yasan cewa itace kuma yasan daga wanne side take, a hankali ya daga kansa, cikin idonta ya tsinci nasa. Ya Allah. He had no idea how much he missed her sai da ya ganta. Karfin zuciya ne kawai ya saka ya tsaya a inda yake, ji yayi kamar yayi abinda walid yace, yaje ya rungume ta, amma kuma anya rungume budurwa a gidan surukai dai dai ne? Ta rame, sosai, Allah ne kadai yasan abinda zai yiwa wanda duk ya takura mata da zai ganshi. Sama sama yaji daddy yana magana amma bai fahimci me yake cewa ba, sai da ya sake maimaitawa sannan ya fahimta, wayarsa ya dauko ya kira walid ya gaya masa sakon daddy sannan ya bude wa daddyn kofa ya shiga ya rufe da sauri ya juyo inda take tsaye, Allah yasa bata bace ba, tana nan kuwa tamkar wadda aka dasa, cikin kwayar idonta ya kalla ya fahimci cewa he have nothing to fear, kujerar mulkinsa tana nan daram a zuciyarta. Da sauri ta bar gurin ta tafi daya motar ta shiga, sai bayan data shiga sannan ya lura daddy ya sauke glass din window dinsa yana kallon shi, ya shafa kansa da sauri yana sunkuyar da kai kamar munafiki sannan ya shiga gaban motar ya zauna. Walid ya karaso suka hau hanyar airport.

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Episode One : The Beginning of the Beginning
  2. 2 Episode Two: Meet my Family
  3. 3 Episode Three: Loved by All
  4. 4 Episode Four: Moon's Sister
  5. 5 Episode five: The Strangers
  6. 6 Episode six: The Challenge
  7. 7 Episode Seven: The Thin Tall Man
  8. 8 Episode Eight: The New Imam
  9. 9 Episode Nine: Give Me a Chance
  10. 10 Episode Ten: I Don't Know
  11. 11 Episode Eleven : The Protector
  12. 12 Episode Twelve : This is Me
  13. 13 Episode Thirteen : This is Me 2
  14. 14 Episode Fourteen : The Limit
  15. 15 Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
  16. 16 Episode Sixteen : The Letter
  17. 17 Episode seventeen: Reply
  18. 18 Episode eighteen: what's Next?
  19. 19 Episode Nineteen: The Goodbye
  20. 20 Episode Twenty: The New Job
  21. 21 Episode Twenty one: Amira
  22. 22 Episode Twenty Two: Efisowa
  23. 23 Episode Twenty three: The Break up 💔
  24. 24 Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
  25. 25 Episode Twenty five: The Eclipse
  26. 26 Episode Twenty Six: A Step Further Away
  27. 27 Episode Twenty Eight : University of Oxford
  28. 28 Episode Twenty Nine: The Message
  29. 29 Episode Thirty : The Final Blow
  30. 30 Episode Thirty One: Let it go
  31. 31 Episode Thirty Two : Munnir
  32. 32 Episode Thirty Two : Mahdi
  33. 33 Episode Thirty Three: Zayed
  34. 34 Episode Thirty Four : Back to Square One
  35. 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
  36. 36 EpisodeThirtySix: Interesting
  37. 37 Episode Thirty Seven : The Dinner
  38. 38 Episode Thirty Eight : The Shadow
  39. 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2
  40. 40 Episode Forty :TheShadow 3
  41. 41 Episode Forty One : Born for This.
  42. 42 Episode Forty Two : Born for This
  43. 43 Episode Forty Three: America
  44. 44 Episode forty four : America 2
  45. 45 Episode Forty Five : The Rush
  46. 46 Episode Forty Six : The Repentance
  47. 47 Episode Forty Seven : Amir
  48. 48 Episode Forty Eight : Awkward
  49. 49 Episode Forty Nine : Ya Habeeb
  50. 50 Episode Fifty : Munir 2
  51. 51 Episode Fifty one : Mommy
  52. 52 Episode Fifty Two : The Journey
  53. 53 Episode Fifty Three : Daddy
  54. 54 Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
  55. 55 Episode fifty five : Her Father's Daughter 2
  56. 56 Episode Fifty Six : What You Sow
  57. 57 Episode Fifty Seven : What You Sow 2
  58. 58 Episode Fifty Eight : I Missed You
  59. 59 Episode Fifty Eight : For You, Only You
  60. 60 Episode Sixty : The Prince
  61. 61 Episode Sixty One : Save the Date
  62. 62 Episode Sixty Two : The Manager
  63. 63 Episode Sixty Three : Amira 3
  64. 64 Episode Sixty Four : The Past and the Future
  65. 65 Episode Sixty Four : The Visitors
  66. 66 Episode Sixty Six : The Wedding
  67. 67 Episode Sixty Seven : The Wedding 2
  68. 68 Episode Sixty Eight : The Wedding Night
  69. 69 Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
  70. 70 Episode Seventy : The Wedding Night 3
  71. 71 Episode Seventy One : The Honeymoon
  72. 72 Episode Seventy Two : My Everything
  73. 73 Episode Seventy Three : His Father's Son
  74. 74 Episode Seventy Four : The Cook
  75. 75 Episode Seventy Five : The Emir
  76. 76 Episode Seventy Six : The Visitors
  77. 77 Episode Seventy Seven : Amina
  78. 78 Episode Seventy Eight : The Storm
  79. 79 Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
  80. 80 Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
  81. 81 Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
  82. 82 Episode Eighty Two : The Light
  83. 83 Episode Eighty Three : The News
  84. 84 Episode Eighty Four : Little Love
  85. 85 Episode Eighty Five : Ibrahim
  86. 86 Episode Eighty Six : The Phone Call
  87. 87 Episode Eighty Seven : Riyadh
  88. 88 Episode Eighty eight :Khairat
  89. 89 Episode Eighty Nine : Khairat 2
  90. 90 Episode Ninety : His Mother's Son
  91. 91 Episode Ninety One : His Mother's Son 2
  92. 92 Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
  93. 93 Episode Ninety Four : RIP
  94. 94 Episode Ninety Five : The Light
  95. 95 Episode Ninety Six : The New Bride
  96. 96 Episode Ninety Seven : The Real Prince
  97. 97 Episode Ninety Eight: My Baby
  98. 98 Episode Ninety Nine : New Little Love
  99. 99 Episode Hundred : Not The End.