Chapter 6
Episode six: The Challenge
Nidai har ga Allah wannan hukuncin baiyi min dadi ba, saboda haka kawai naji raina baya son copper dinnan, he is too young to teach us a ganina. Hafsat kuwa sai na lura babu abinda ya dame ta. Da nayi mata magana sai cewa tayi "laa ni ban wani damu bafa, musamman akan geography, wancan teacher din ya fiya bayar da note, kin san ni kuma bana son note" (Yar Hutu). Unlucky for me, washe gari muna da geography. Tun safe naji raina ya baci dan ma bashine first period ba,sai munyi biology sannan zamuyi shi. Tom teacher din biology yana gama yi mana sai ya bamu assignment, yana fita sai na dauko assignment dina na fara sai naji hayaniya a class anata leka window. Na tambayi Amira nace "menene wai ake wannan leken" sai tayi dariya tace " wannan yaron ne ya taho zai koya mana geography" nayi tsaki nace "zai koya musu dai" na ci gaba da zanen da nakeyi na digestive system dan shine assignment din da biology teacher ya bayar. Hafsat naji tace "sabon shiga, ko dan late coming dinnan ma abar mutane su huta baza'ayi ba". Tana gama fada yana shigowa kuma na tabbatar cewa yaji abinda tace, dariya ce ta kubce min ganin yadda Hafsat ta wani maze kamar ba ita ce tayi maganar ba. Ina kallonsa ta gefen ido na. Ya cire uniform din NYSC ya saka personal shirt da wando amma ya dora p-cap din NYSC din a kansa. Ban wani kalleshi sosai ba na maida hankali na akan zanen da nake yi. Ya jima a tsaye yana kallon mu daya bayan daya sannan a hankali yace "don't u guys know how to greet? Duk class din muka mike a tare, tare da cewa " good morning sir" ya jima yana binmu da kallo sannan yace "sit down" inajin Hafsat a hankali tace "finally" Nayi murmushi na zauna tare da ci gaba da zane na. Takowa yayi a hankali yazo gabana ya tsaya yace "why are u laughing?" Na dago kaina na kalle shi ido cikin ido nace " I am not laughing sir, I was smiling". "Hmm" shine abinda yace sannan ya kunna board, da yake smart board muke amfani dashi. Ya saka flash drive dinsa na nemo slides din da zai yi mana ranar ya kunna. Ni kuma ina ganin haka na cigaba da zane na. Inajinsa yace "our topic for today is rocks and their origin". Sannan yayi tambaya "who knows what this is?" Ban dago kaina ba ballantana inga abinda yake tambaya akai saboda ina expecting wani a ajin ya bada amsa, amma ga mamaki na sai naji shiru babu wanda yayi magana. Jikina ne ya bani ana kallona, na daga kai sai na ganshi a tsaye a kaina "miss smiler, we are trying to have a class here" yace min " can you please, out of the goodness of your heart, tell me what this is?". Ya fada yana nuna board, araina nace lallai wannan mutumin ya raina min hankali. Ya dan bude ido yace "the picture is displayed on the board, miss smiler, not here" ya sake fada yana nuna kansa. Dariya najiyo kasa-kasa daga bayana sannan na fahinci cewa kallonsa nake tayi. A hankali na janye idona daga kansa. Kallo daya nayi wa hoton black shiny stone din da yayi displaying a board, na dauke kaina. Na mai da dubana kan assignment dina tare da daukan pencil dina na cigaba da zanen da nake yi. A hankali nayi magana nace " that's obsidian sir". Shi kansa da yake kusa dani baiji abinda nace ba, dan haka ya sunkuyo da kansa yace "can you PLEASE, raise your voice a little bit?" Take naji raina na sake baci. "PLEASE" Ya sake cewa da muryar challenge. Dariya na sake ji saga baya na. Ni kuma har lokacin zane na nakeyi. Har ya juya zai koma gurin board sai na daga murya ta nace " That is Obsidian " Chak naga ya tsaya sannan a hankali ya dawo inda nake zaune ina zane na yace. "Tell me more" murmushi nayi sannnan na fara kwararo masa bayani tun daga kan yadda earth core take da yadda rocks suke melting su zama lava, yadda mantle da crust suke budewa har lava din ta fito earth surface. Daga nan na koma kan bayanin different types of cooling and solidification na lava din yadda yake producing different kinds of rocks. Sannan na dawo kan shi obsidian din, cooling process din da yake forming dinshi, dalilin da yasa yake black and shiny, composition dinsa, life span dinsa da amfanin sa a gurin mutane. Nafi 30minutes ina magana kuma at the same time ina cigaba da drawing dina. Tunda na fara magana ajin yayi tsit babu wanda yayi magana har na gama. Gamawa ta yayi dai dai da gama drawing dina. Sai da na karewa drawing dina kallo na tabbatar na gama sannan na dago kaina na kalle shi ido cikin ido tare da cewa " Is there anything more you want to know, SIR?" Na fadi kalmar sir din nima cikin challenge. Sai da wajen 30sec ta wuce sannan ya iya magana yace "wow, that is very correct. No, there is nothing more. U have said it all".
Kamar hadin baki, yana gama fadin haka aka buga bell din break. Books din mu duk muka rufe muka fice daga class din. Sai da mukayi nisa sannan na juyo na kallo class din mu naga yana nan a tsaye a inda muka barshi ya saka hannayensa cikin aljihun wandon sa yana kallon kasa. "He must be feeling like an idiot" na fada ina murmushi. Amira tace " Ai kin wanke mana shi tas, I wonder ta yaya zai yi facing din mu tomorrow morning for maths" Hafsat tace "and they said I am the cruel one". Dariya muka yi muka tafa ni da ita, nace "ai ba cruelty bane, he asked me a question and I answered him. He then asked me to tell him more, so I told him more" wata kawarmu Hasiya tayi joining din mu tace "baki da kirki Moon. You told him more and more. By the way, how do u know so much? Ni dai nasan ba'ayi mana duk wannan a aji ba" Nayi murmushi nace mata a cikin holiday na karanta, nasan za muyi shi a wannan term din. Nayi forming note a kan shi, in kina so kizo ki karba ki copying " tayi min godiya ta wuce. Amira tace "Tabdi ai ni babu abinda zai saka inyi karatu a cikin hutu, hutu fa akace, we are suppose to huta a cikin hutu"
Table of Contents
Chapters
- 1 Episode One : The Beginning of the Beginning
- 2 Episode Two: Meet my Family
- 3 Episode Three: Loved by All
- 4 Episode Four: Moon's Sister
- 5 Episode five: The Strangers
- 6 Episode six: The Challenge
- 7 Episode Seven: The Thin Tall Man
- 8 Episode Eight: The New Imam
- 9 Episode Nine: Give Me a Chance
- 10 Episode Ten: I Don't Know
- 11 Episode Eleven : The Protector
- 12 Episode Twelve : This is Me
- 13 Episode Thirteen : This is Me 2
- 14 Episode Fourteen : The Limit
- 15 Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
- 16 Episode Sixteen : The Letter
- 17 Episode seventeen: Reply
- 18 Episode eighteen: what's Next?
- 19 Episode Nineteen: The Goodbye
- 20 Episode Twenty: The New Job
- 21 Episode Twenty one: Amira
- 22 Episode Twenty Two: Efisowa
- 23 Episode Twenty three: The Break up 💔
- 24 Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
- 25 Episode Twenty five: The Eclipse
- 26 Episode Twenty Six: A Step Further Away
- 27 Episode Twenty Eight : University of Oxford
- 28 Episode Twenty Nine: The Message
- 29 Episode Thirty : The Final Blow
- 30 Episode Thirty One: Let it go
- 31 Episode Thirty Two : Munnir
- 32 Episode Thirty Two : Mahdi
- 33 Episode Thirty Three: Zayed
- 34 Episode Thirty Four : Back to Square One
- 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
- 36 EpisodeThirtySix: Interesting
- 37 Episode Thirty Seven : The Dinner
- 38 Episode Thirty Eight : The Shadow
- 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2
- 40 Episode Forty :TheShadow 3
- 41 Episode Forty One : Born for This.
- 42 Episode Forty Two : Born for This
- 43 Episode Forty Three: America
- 44 Episode forty four : America 2
- 45 Episode Forty Five : The Rush
- 46 Episode Forty Six : The Repentance
- 47 Episode Forty Seven : Amir
- 48 Episode Forty Eight : Awkward
- 49 Episode Forty Nine : Ya Habeeb
- 50 Episode Fifty : Munir 2
- 51 Episode Fifty one : Mommy
- 52 Episode Fifty Two : The Journey
- 53 Episode Fifty Three : Daddy
- 54 Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
- 55 Episode fifty five : Her Father's Daughter 2
- 56 Episode Fifty Six : What You Sow
- 57 Episode Fifty Seven : What You Sow 2
- 58 Episode Fifty Eight : I Missed You
- 59 Episode Fifty Eight : For You, Only You
- 60 Episode Sixty : The Prince
- 61 Episode Sixty One : Save the Date
- 62 Episode Sixty Two : The Manager
- 63 Episode Sixty Three : Amira 3
- 64 Episode Sixty Four : The Past and the Future
- 65 Episode Sixty Four : The Visitors
- 66 Episode Sixty Six : The Wedding
- 67 Episode Sixty Seven : The Wedding 2
- 68 Episode Sixty Eight : The Wedding Night
- 69 Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
- 70 Episode Seventy : The Wedding Night 3
- 71 Episode Seventy One : The Honeymoon
- 72 Episode Seventy Two : My Everything
- 73 Episode Seventy Three : His Father's Son
- 74 Episode Seventy Four : The Cook
- 75 Episode Seventy Five : The Emir
- 76 Episode Seventy Six : The Visitors
- 77 Episode Seventy Seven : Amina
- 78 Episode Seventy Eight : The Storm
- 79 Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
- 80 Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
- 81 Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
- 82 Episode Eighty Two : The Light
- 83 Episode Eighty Three : The News
- 84 Episode Eighty Four : Little Love
- 85 Episode Eighty Five : Ibrahim
- 86 Episode Eighty Six : The Phone Call
- 87 Episode Eighty Seven : Riyadh
- 88 Episode Eighty eight :Khairat
- 89 Episode Eighty Nine : Khairat 2
- 90 Episode Ninety : His Mother's Son
- 91 Episode Ninety One : His Mother's Son 2
- 92 Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
- 93 Episode Ninety Four : RIP
- 94 Episode Ninety Five : The Light
- 95 Episode Ninety Six : The New Bride
- 96 Episode Ninety Seven : The Real Prince
- 97 Episode Ninety Eight: My Baby
- 98 Episode Ninety Nine : New Little Love
- 99 Episode Hundred : Not The End.