Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 73

Episode Seventy Three : His Father's Son

Maimoon Book 1 Complete Hausa Novel 3,376 words 0 views Progress saved
Download Book

Washe gari bamuyi missing sallar assuba ba kaman jiya, Sultan ne ya fara tashi, sai da yayi alwala sannan ya tashe ni shi kuma ya fita masjid, ya jima bai dawo ba har nayi sallah na dan taba karatun al'qurani sannan nayi morning azkar dina, ji nayi duk na gaji da kwanciya, I want to do some work, na tashi na gyara dakin na wanke toilet, na dawo palo ina cikin gyarawa ya shigo, ya tsaya yana kallona "wato matar nan kin warke ko? Shine zaki kama aikin da assubar nan ko?" Nace "na gaji da kwanciya ne kawai, I want to do something" ya fara tahowa yana min murmushin mugunta yace "You want to do something? I have got something for you" na ajiye duster din hannuna na fara ja da baya ina jin tsoro har cikin raina dan na warke amma ban manta azabar da nasha ba. Nace "Sultan Allah ban gama warkewa ba, dan Allah kayi hakuri wallahi na daina aikin zan koma in kwanta" ya karaso in da nake yace "really baki warke ba? Can I see?" Nayi saurin girgiza kaina nace "you are not a doctor how will you know if a wound is healed or not?" Yace "am not a doctor but ni mijin doctor ne, dan haka believe me I will know" idonsa kawai na kalla nasan kona roke shi it will be to no avail, jikina har karkarwa yake yi saboda tsoro, me yasa nayi aure ne wai? A kunne na ya rada min "believe me, it will not hurt". And it didn't, at least not as I expected. Yana cikin bacci na zare jikina na tashi, a hankali na lallaba na saka kayana na fice, da sauri na karasa dakina ina shiga nayi locking kofar, finally nazo dakina after two days, da sauri sauri na gyara dakin duk da ba wani datti yayi ba, na shiga toilet na shiga shower ina wanka, at last zanyi wanka without sultan standing and watching. Na fito na zauna na shirya a tsanake cikin atamfa ruwan hoda, nayi 'yar kwalliya kadan na fesa turare na fito. Ina fita palo na tarar da wata tsohuwa a zaune a kan carpet da wadansu 'yammata su biyar daga can bakin kofa, ina fitowa duk suka mike tsaye kansu a kasa, 'yammatan kamar harda tsoro a fuskarsu, sai da na zauna sannan suka durkusa suka fara gaisheni daya bayan daya, na saki fuskata sosai na amsa musu. Babbar matar ce ta matso tace "ranki ya dade, Allah ya taya miki, Allah ya dora ki akan makiyanki duniya da lahira, Allah yaji kan magabata, Allah kuma yasa albarka a zuriya" nace "Ameen" ta cigaba da magana "ranki ya dade ai jiya ma munzo, muna nan har magriba bamu samu ganin ki ba. Dama mai babban daki (yaya) ce ta turo mu, tace tana gaishe ki sosai, kuma tace duk mu shidan nan mu dawo nan gurinki mu zauna muke yi miki hidima. Ni sunana Gaji, tun asalin kakanni na bayi ne a wannan gidan, anan aka haifeni anan na girma nayi aure na hayayyafa, 'ya'yana ma suka yi aure suka haihu duk acikin gidan nan, guda biyu daga cikin 'yammatan nan jikokina ne. Kamar yadda aka kawo 'yammatan nan gurinki yanzu haka aka kaini gurin mai babban daki sanda tana amarya, wannan shi yasa nake daga cikin amintattun bayinta, kuma wannan shi yasa ta zabe ni akan in zo in zauna a gurinki, saboda tasan zan rike mata amana. Suma wadannan duka yaran da kika gani zababbu ne dan ni ta saka in zabo mata masu tarbiyya da rikon amana kuma na zabo su. Insha Allah zamu rike ki da amana Allah kema ya baki ikon rike mu da amana." Kawai naji matar ta kwanta min araina, na tambayi yaran duk sunayensu suka fada min, naga duk sunki sakin jikinsu sai na fara yi musu wasa, ba'a jima ba suka fara dariya. Da kaina na tashi na kaisu har bq din mata na nuna musu komai sannan muka dawo tare. Nace "Ku dauke ni a matsayin yayar ku kunji, dama ni bani da kanne mata kunga shikenan na samu, duk abinda kuke so kuyi min magana in dai ina dashi zan baku, abinda bana so shine kazanta, ku kula da tsaftar gidan nan ku kuma kula da tsaftar jikin ku, ku kame kanku banda shiririta. Allah ya bamu ikon zama lafiya". Sunji dadin yadda na karbe su, kuma daga dukkan alamu sunji dadin bq din dai sai murna suke sunzo gurin 'yan gayu. Nan take baba Gaji ta raba mudu kowa aikinsa, jikokinta guda biyu su ta bawa part dina, sauran kuma sauran parts din gidan. Banda part din Sultan. A take suka tashi suka fara aikin su. Ina zaune sai ga abinci daga cikin gida, suka je suka ajiye a dining room sannan suka zo suka gaishe ni, wai hajiya tace ayi min sannu da jiki, na amsa musu, naga suna ta kallon 'yammatana da Baba Gaji da naga ta hade rai. Na tashi na koma part din Sultan na tarar ya tashi yana wanka, na zauna na jira shi ya fito, yana kallona yace "shine kika gudu ko?" Bance komai ba, ya tsaya yana goge jikinsa, ya juyo ya kalleni muka hada ido nayi sauri ya sunkuyar da kaina, yayi dariya yace "ana so ana kaiwa kasuwa. You are welcome to watch" nace "an kawo abinci, nan za'a kawo ko kuma zaka fito dining?" Yana kokarin shiga closet yace "bara kawai in fito, dama zan dan fita" har ya kai bakin kofa kuma ya tsaya ya juyo "bazaki zo ki tayani shiryawa ba?" Na rufe fuskata da hannuna, yayi dariya "wannan kunyar naga har yanzu da akwai saura, zanyi maganin ta ne" ina nan zaune inda ya bar ni har ya sake fitowa, kananan kaya ne a jikinsa yayi stocking rigar ya saka belt, da comb a hannunsa yana taje kansa, na tashi na karasa inda yake na karbi comb din na cigaba da taje masa, nace "ina zaka je?" Yace "orphanage. Yanzu zan dawo. Tunda aka fara bikin nan banje na gansu ba" na gama gyara masa gashin nace "let's go eat then".
Sai bayan ya tafi sannan na dawo palo gurin baba gaji, ina zama tazo ta fara yi min tausa a kafa ta, naji dadin tausar saboda dama kafar ba dadin ta nake ji ba, cikin girmamawa ta fara yi min magana "ranki ya dade ni kam wadannan masu kawo abincin nan ina ma za'a ce musu su daina kawowa? Mu sai mu ringa yi anan" ban amsa mata ba na lumshe ido na inajin dadin tausar. Ta cigaba da magana "Ranki ya dade sai kinyi a hankali sosai da Hajiya. Mutanen da suke waje kullum suna maganar irin yadda take nuna wa karamin sarki soyayya amma mu da muke cikin gidan nan mun san ba haka abin yake ba" na bude ido na nace "waye karamin sarki?" Tace "maigidanki ranki ya dade, haka mai babban daki take ce masa muma kuma duk haka muke ce masa" na koma na kwanta na sake rufe idona, ta cigaba "bata sonsa ko kadan, kema kuma dole nasan kiyayyarsa zata shafe ki. Kar ki yarda da duk wata magana da zata gaya miki musamman akansa, mu mun san komai" maganar ta ta karshe ce ta saka na bude ido na, 'mu munsan komai' na tashi zaune ina kallonta nace "Baba Gaji, kin san mahaifiyar Sultan?" A hankali naga yanayin fuskarta yana komawa alamar tsoro, ta sunkuyar da kanta kasa, na sake magana "baba gaji kince anan gidan aka haife ki, kince kuma kina tare da Yaya tun tana amarya, haka yana nuffin kinsan mai martaba sarki tun haihuwarsa har girman sa har auren sa, hakan yana nufin kinsan haihuwar Sultan, abinda na tambayeki shine; kin san mahaifiyar sultan?" Gani nayi jikinta ya fara rawa, kanta har yanzu yana kasa ta kasa kallona, tace "ki yi min afuwa ranki ya dade, an hana mu yin magana akan ta, an hana mu ko da ambatar sunan tane" cikin mamaki nace "waye ya hanaku maganar ta? Kuma saboda me?" Ta dago ta kalleni tace "mai martaba sarki, marigayi, mahaifin wannan sarkin" wani mamakin na sake yi nace "kina nufin ba wannan sarkin ba, wancan" ta gyada kai, nace "to saboda me?" Ta girgiza kanta tace "Allah masani" nayi shiru ina tunani, Sultan ya taba ce min "no body talk about her, it is as if she didn't exist" na gyara zamana nace "amma baba gaji shi wanda kike magana akansa shekarar sa ashirin da rasuwa, in kin gaya min taya za'a yi yasan kin gaya min?" Ta girgiza kai, tace "ranki ya dade mu bayi ne, muna biyayya ga iyayen gidan mu koda kuwa bayan mutuwar su ne, bama cin amanarsu, bama ha'intarsu" na mike tsaye na fara zagaye a palon sannan na dawo na zauna nace "sanda wancan sarkin yana nan kina a matsayin baiwar sa, bayan ya mutu kika zama baiwar Yaya, yanzu kuma yaya ta bani ke, in dai har zaki yi masa biyayya har bayan ransa to hakan yana nufin zaki yi min biyayya nima. Ina umartarki daki bani labarin duk da kika sani dangane da mahaifin sultan da kuma mahaifiyarsa" ina kallon yadda duk ta rude, na dan dafa kafadarta nace "nayi miki alkawarin duk maganar da mukayi zata tsaya a tsakanin mu".
Sai da ta nutsu ta daidaita numfashinta sannan ta fara magana " ina nan aka haifi mai martaba sarki na yanzu, ina nan kuma aka haifi dukkannin kannensa. Duk a cikin su shine yafi dauko halin mahaifinsa; zafin zuciya, taurin rai da kuma tausayi. Yadda kika ga karamin sarki haka yake, kuma shima kakansa haka yake. An gaya mana cewa wannan shine abinda yasa suke zama sarakuna, dan shi mulki sai mutum yana da karfin jiki dana zuciya, sai mutum yana da zafi kuma yana da sanyi. Sanda ya girma ya zama saurayi mu dai munsan yana kasar waje karatu, duk sanda yayi hutu yazo gidan nan haka zai cika gidan nan da abokanan sa har sai ya koma tukunna, wadansu abokan ma daga makarantar suke biyo shi su zo nan suyi hutun tare su koma. Rannan ya dawo gida tare da abokanan sa da yawa, aka shirya musu party ana ta murna, aka gaya mana cewa ai murnar kammala karatunsa akeyi, muma mukayi ta murna muna taya shi farinciki. Bai dade da dawowa ba sai suka samu sabani da mahaifinsa, rana daya muka neme shi muka rasa a gidan nan, ba karamin tayar da hankali mahaifinsa yayi ba saboda kowa ya san duk cikin 'ya'yansa babu wanda yake so kamarsa. Yaya ta tada hankalinta, kullum ana cikin tara malamai da addu'ar Allah ya bayyana shi. Rannan muna zaune da daddare tare da Yaya kawai sai gashi ya shigo palon, hannunsa rike da hannun wata yarinya, balarabiya. Muka tashi da murna amma sai muka ga yaya sam bata murna sai ma tashin hankali da muka gani a tare da ita, aka aika aka gayawa sarki sai gashi ya taho da kansa, mu dai duk muka fita muka basu guri, basu fi awa daya ba sai gashi ya fito rike da hannunta ya bude motarsa ya shiga ya fice daga gidan. Sai daga baya muka samu labarin ainahin abin da ya faru, yarinya ce yake so balarabiya, ya nemi babansa ya nema masa auren ta amma baban yaki, wannan shine dalilin da yasa ya tsallake yayi tafiyarsa yaje ya nemi auren nata da kansa, aka bashi ita aka daura musu aure sannan ya dauko ta ya taho da ita, a tunaninsa tunda ya riga ya aure ta ai dole uban ya karba. Amma da suka zo maimakon uban ya karba sai ya kara tunzura yana ganin kamar ya nuna masa bai isa dashi ba tunda yayi aure ba da sanin sa ba. Hakan ne yasa shi kuma ya dauki matarsa suka yi tafiyarsu. Ba'a kuma jin labarin sa ba sai bayan shekara daya. Shima wannan karon muna zaune sai gashi ya shigo gidan, hannunsa daya rike da wannan balarabiyar, daya hannun kuma yana rungume da dan jariri. Wato tunda ya kawo musu suruka sunki karba shine yanzu ya kawo musu jika. Ai kuwa wannan karon yaci nasara, dan kallo daya kakan yayi wa jikan ya tattara son duniya ya dora masa. Tun daga nan Khairat ta tare a gidan nan. Yarinya ce nutsatstsiya sosai, tana da hankali da girmama mutane. Farkon zuwanta sam bata iya hausa ba, amma a hankali ta fara koya. Duk gidan nan, 'ya'yan gida da mu bayi, dama wadanda suke shigowa su fita, babu wanda baya son khairat, babu kuma wanda bai san irin son da mijinta yake mata ba dan baya boyewa ko a gaban waye kuwa. Shi kuwa wannan dan jaririn wanda daga baya muka fahimci babansa ya saka masa sunan sa saboda tsananin son da yake masa, sai ya zama an kasa ban bance waye yafi sonsa tsakanin iyayensa da kuma kakansa. Tun yana jariri muka fahimci cewa ba sunan babansa kadai yaci ba harda halayensa, duk duk kiriniyar da babansa yayi yana jariri shima ita yake yi, kamar copy dinsa ne aka ajiye, sai dai yafi kama da mahaifiyarsa. Karamin Sarki yana da shekara biyu a duniya rannan kawai muka tashi babu khairat babu alamunta, babu abinda ta dauka a kayanta, ko danta bata dauka ba, kuma babu wanda yace yaga sanda ta fita. Abinda kuma ya fi bamu mamaki a tafiyar tata shine, babu wanda ya neme ta" nayi sauri na katse ta nace "ban gane me kike nufi babu wanda ya neme taba, mijinta fa wanda kika ce yana yi mata soyayya kamar rai?" Tace "shine abin mamakin Allah ya taimakeki, duk zafin ransa, duk, duk taurin zuciyarsa. Mun dauka zai bita amma ko kofar gida bai je ba. Komawa yayi tamkar wanda aka chanza shi da wani, tamkar ba shi ba gaba daya yayi sanyi duk karfin sa babu. Kamar an zare masa ruhinsa an bar gangar jikin. A rana daya aka saka aka kwashe duk kayanta aka rufe dakinta. A ranar aka taramu aka umarcemu da ko sunan ta kada wanda ya sake ambata a gidan. Bamu tambayi dalili ba kawai dai munyi biyayya. Kwana biyu da tafiyar ta karamin sarki ya galabaita da kukan neman ummin sa da daddyn sa, har zazzabi yayi, ranar da safe ina gurin yaya ina ta faman rarrashin karamin sarki sai ga babansa ya shigo, yana shigowa yaron ya fara zamewa daga hannuna yana kokarin tafiya gurinsa amma abin mamaki ko kallon inda yake bai yi ba, tamkar bai san shi ba, ya shiga ya gaishe da mahaifiyarsa ya juya ya fice, yaron yana ta kiran daddy daddy yana kuka. Tun daga ranar abinda ya cigaba da faruwa kenan, kamar yadda aka goge duk wani abu daya shafi mahaifiyar karamin sarki a gidan nan haka ya zamo tamkar an goge duk wani digo na soyayya tsakanin karamin sarki da mahaifinsa" tasa mayafinta tana goge hawayen idonta, nace "amma hajiya fa, an auro ta lokacin?" Ta girgiza kai tace "ai Hajiya sam basu zauna da mahaifiyar karamin sarki ba, sai bayan da suka rabu da shekara biyu ma sannan aka yi aurenta" ji nayi kaina ya daure, saboda all this while abinda nake tunani shine Hajiya ce ta raba maman sultan da babansa, ita ce kuma ta raba tsakanin su ta saka kiyayya a tsakanin su, things are not always what they seem, na sake tambaya "to daga baya kenan Takawa ya hadu davita har suka fara soyayya suka yi aure?" Tace "Ranki ya dade ai babu soyayya, auren hadi ne, 'yar 'uwarsa ce ai, kakansu daya. Kawai kiransa akayi akace masa an hada shi aure da wance yace to, daga nan akayi auren, anayin auren suka tafi kasar waje tare wai itama zata yi karatu, shekarar su daya suka dawo da yarima Abbas yana karami" na danyi digesting maganar kadan, wanne karatu ne akeyinsa a shekara daya?. Taci gaba da labarin Sultan tace "daga nan sai kakansa ya dauke shi, ya mayar dashi dakinsa, hatta kayan sakawarsa a can suke, gata da soyayya sosai ya nuna masa, a haka har yaron ya saki jikinsa ya daina kuka, amma kuma duk da kankantarsa bai manta da mahaifinsa ba, dan duk inda ya ganshi zai tafi gurinsa da gudu, amma ko kallon inda yake baya yi, in yazo ya rike kafarsa sai ya ture shi ya fadi yayi tafiyarsa. A gurin sarkin lokacin kuma babu tamkar karamin sarki, dan har bacci akan gado daya suke yi, ko taba shi babu wanda ya isa yayi hatta su Yaya da Nani, abin ya dami yaya kwarai amma duk sanda tayi magana to ranar kuwa zata ga bacin rai. A haka har yaron ya shekara goma, ya sangarce sosai babu mai saka shi babu mai hana shi, ko tafiya zuwa kasashen waje tare yake tafiya dashi, a fada suna tare, in taro zaije tare zasu tafi. Rannan kawai da safe aka ga basu fito sallar asuba ba, aka shiga za'a tashe su amma sai jikan ne kawai ya tashi, kakan Allah ya karbi ransa a cikin bacci. Wannan mutuwar ta tayar da hankalin kowa a masarautar nan amma babban abin tausayi shine karamin sarki, bai saba da kowa ba sai shi bai san kowa ba sai shi, dan haka rasa wanda zai rarrashe shi akayi, kwata kwata ya hana a yi wa gawar sutura, sanda mahaifinsa yazo muka ji dadi cewa an samu mai rarrashinsa amma yana zuwa sai ya dauke shi chak ya tafi dashi wani tsohon store ya daure masa bakin sa, ya daure masa hannayensa da kafafuwansa ya rufe shi a dakin yayi tafiyarsa. Babu wanda bai tausayawa yaron nan ba, kuka biyu muka yi a lokacin, har yanzu ina iya tuno wani irin gunjin kuka daya ringa yi babu baki, kamar ransa zai fita, wallahi ban dauka yaron nan zai yi rai ba, na dauka zuciyarsa zata buga ya mutu, amma zuciyarsa mai karfi ce. Haka ya kwana anan sai da safe sannan ya fito dashi kuma ya gaya masa in ya kuma yin kuka sai ya kuma daure shi. Bayan anyi sarauta su Hajiya suka dawo nan mu kuma muka koma sabon guri tare dasu Yaya, nan Hajiya tace abar mata Karamin Sarki, Yaya sam bata so hakan ba amma sai ta barshi din wai ko hakan zai sa ya saba da mahaifanan. Mu dai daga nan bamu kuma jin labarin da yake ciki ba sai kawai muka ji labarin wai an kai shi Lagos gidan kangararru, Yaya ta tayar da hankalinta sosai, amma ko ta kira Takawa ta yi masa magana sai ya nuna mata kamar zai aika a dawo dashi amma shiru, sai da ya shekara biyu acan sannan Yaya ta aika galadima ya dauko shi, tace masa ya mayar dashi gidansa ya zauna acan, ai kuwa nan rigima ta tashi dan har saida Yaya tayi sharia tsakanin sarki da galadima akan me yasa galadima ya dauko karamin sarki daga Lagos, wannan shi yasa duk 'yan uwa kowa ya dauke hannunsa daga kan maganar karamin sarki har aka turashi kasar waje karatu babu wanda yayi magana, amma ni nice shaida, duk watan duniyar nan sai Yaya ta saka an sauke masa alqur'ani da niyyar ya zama kariya a gare shi a duk inda yake".
Jin tayi shiru yasa na gyara zamana nace "to yanzu baba gaji, duk gidan nan babu wanda yasan ina ne garin su mahaifiyar Sultan?" Tayi shiru tana tunani, sannan tace "to mu bayi dai kam bana jin akwai wanda ya sani, amma Yaya ba zata kasa sani ba, amma kuma ranki shi dade bana jin zata gaya miki, dan da zata fada da duk tsahon shekarun nan da ta gayawa karamin sarki". Na koma na kwanta na lumshe ido na ina juya maganganun a raina, na samu wasu amsoshin, amma kuma amsoshin sun kuma tayar da wasu tambayoyin. Menene gaskiya dalilin rabuwar iyayen sultan? Menene dalilin da yasa soyayyar mahaifinsa ta koma kiyayya a lokaci daya? Menene kuma dalilin da yasa ake boye labarin mahaifiyar Sultan ba'a so kowa ya sani? Na tuna da labarin da Sultan ya bani na amsar da Yaya ta bashi sanda yayi mata irin wannan tambayar 'to protect the family name' but what kind of protection?
Follow me on wattpad @maman_Maimoon

Table of Contents

Chapters

99 chapters
  1. 1 Episode One : The Beginning of the Beginning
  2. 2 Episode Two: Meet my Family
  3. 3 Episode Three: Loved by All
  4. 4 Episode Four: Moon's Sister
  5. 5 Episode five: The Strangers
  6. 6 Episode six: The Challenge
  7. 7 Episode Seven: The Thin Tall Man
  8. 8 Episode Eight: The New Imam
  9. 9 Episode Nine: Give Me a Chance
  10. 10 Episode Ten: I Don't Know
  11. 11 Episode Eleven : The Protector
  12. 12 Episode Twelve : This is Me
  13. 13 Episode Thirteen : This is Me 2
  14. 14 Episode Fourteen : The Limit
  15. 15 Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
  16. 16 Episode Sixteen : The Letter
  17. 17 Episode seventeen: Reply
  18. 18 Episode eighteen: what's Next?
  19. 19 Episode Nineteen: The Goodbye
  20. 20 Episode Twenty: The New Job
  21. 21 Episode Twenty one: Amira
  22. 22 Episode Twenty Two: Efisowa
  23. 23 Episode Twenty three: The Break up 💔
  24. 24 Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
  25. 25 Episode Twenty five: The Eclipse
  26. 26 Episode Twenty Six: A Step Further Away
  27. 27 Episode Twenty Eight : University of Oxford
  28. 28 Episode Twenty Nine: The Message
  29. 29 Episode Thirty : The Final Blow
  30. 30 Episode Thirty One: Let it go
  31. 31 Episode Thirty Two : Munnir
  32. 32 Episode Thirty Two : Mahdi
  33. 33 Episode Thirty Three: Zayed
  34. 34 Episode Thirty Four : Back to Square One
  35. 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
  36. 36 EpisodeThirtySix: Interesting
  37. 37 Episode Thirty Seven : The Dinner
  38. 38 Episode Thirty Eight : The Shadow
  39. 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2
  40. 40 Episode Forty :TheShadow 3
  41. 41 Episode Forty One : Born for This.
  42. 42 Episode Forty Two : Born for This
  43. 43 Episode Forty Three: America
  44. 44 Episode forty four : America 2
  45. 45 Episode Forty Five : The Rush
  46. 46 Episode Forty Six : The Repentance
  47. 47 Episode Forty Seven : Amir
  48. 48 Episode Forty Eight : Awkward
  49. 49 Episode Forty Nine : Ya Habeeb
  50. 50 Episode Fifty : Munir 2
  51. 51 Episode Fifty one : Mommy
  52. 52 Episode Fifty Two : The Journey
  53. 53 Episode Fifty Three : Daddy
  54. 54 Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
  55. 55 Episode fifty five : Her Father's Daughter 2
  56. 56 Episode Fifty Six : What You Sow
  57. 57 Episode Fifty Seven : What You Sow 2
  58. 58 Episode Fifty Eight : I Missed You
  59. 59 Episode Fifty Eight : For You, Only You
  60. 60 Episode Sixty : The Prince
  61. 61 Episode Sixty One : Save the Date
  62. 62 Episode Sixty Two : The Manager
  63. 63 Episode Sixty Three : Amira 3
  64. 64 Episode Sixty Four : The Past and the Future
  65. 65 Episode Sixty Four : The Visitors
  66. 66 Episode Sixty Six : The Wedding
  67. 67 Episode Sixty Seven : The Wedding 2
  68. 68 Episode Sixty Eight : The Wedding Night
  69. 69 Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
  70. 70 Episode Seventy : The Wedding Night 3
  71. 71 Episode Seventy One : The Honeymoon
  72. 72 Episode Seventy Two : My Everything
  73. 73 Episode Seventy Three : His Father's Son
  74. 74 Episode Seventy Four : The Cook
  75. 75 Episode Seventy Five : The Emir
  76. 76 Episode Seventy Six : The Visitors
  77. 77 Episode Seventy Seven : Amina
  78. 78 Episode Seventy Eight : The Storm
  79. 79 Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
  80. 80 Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
  81. 81 Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
  82. 82 Episode Eighty Two : The Light
  83. 83 Episode Eighty Three : The News
  84. 84 Episode Eighty Four : Little Love
  85. 85 Episode Eighty Five : Ibrahim
  86. 86 Episode Eighty Six : The Phone Call
  87. 87 Episode Eighty Seven : Riyadh
  88. 88 Episode Eighty eight :Khairat
  89. 89 Episode Eighty Nine : Khairat 2
  90. 90 Episode Ninety : His Mother's Son
  91. 91 Episode Ninety One : His Mother's Son 2
  92. 92 Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
  93. 93 Episode Ninety Four : RIP
  94. 94 Episode Ninety Five : The Light
  95. 95 Episode Ninety Six : The New Bride
  96. 96 Episode Ninety Seven : The Real Prince
  97. 97 Episode Ninety Eight: My Baby
  98. 98 Episode Ninety Nine : New Little Love
  99. 99 Episode Hundred : Not The End.