Chapter 5
Episode five: The Strangers
Bayan shekara uku
Haka rayuwa ta cigaba da kasance mana cikin jindadi da gata. Daddy yana ta samun ci gaba, yana ci gaba da harkar ambassadorship dinsa kuma yana visiting lecturer a Oxford. Ya Walid ya kammala sec sch dinsa inda Daddy ya tura shi Oxford yake karatun degree dinsa a fannin engineering. Ya Habeeb yana ss3, Hafsat dani kuma muna ss2.
Yaune second day of resumption kuma kamar yadda al'adar school din take, yaune ake gabatar da speech and prize giving. Mommy, ya Habeeb, daada da Faruk duk sunzo mana, suna zaune a gurinsu na musamman a side din parents. Ni da Hafsat da babbar kawata Amira munyi kwalliyar mu dai dai misali, muka fito gurin taron. Abinda ya bamu mamaki shine ganin wadansu mutane su biyar da kayan NYSC a jikinsu a zaune a bakin hall din taron. Tsayawa nayi ina kallonsu da mamaki saboda tunda muke a school din ba'a taba daukan coppers sunyi service anan ba, ko teachers din ma ba kowa ake turowa ba, sai very qualified teachers wadanda suka san me sukeyi. A hankali na furta " this doesn't look good " amma ga mamaki na sai naga duk sun juyo suna kallon mu alamar sunji abinda na fada. Kunya ce ta kamani, yayinda Hafsat ta tabe baki tace" I guess there is a first time for everything " tana fadin haka tayi gaba tare da fizgar hannuna, babu shiri ni da Amira muka bita a baya.
A yanzu kam Hafsat zan iya cewa ta zama budurwa, dan inka ganta ba zaka ce she is just fifteen years ba, ni kuma lokacin ina fourteen amma still bani da girman jiki sai tsaho shima ba sosai ba. Hafsat kuwa masha Allah, dan koni da nake mace wani lokacin tsayawa nakeyi inyi ta kallonta. Fatarta bata kai tawa haske ba amma fa a murje take tana daukan ido, ga laushi. Hancinta yafi nawa tsaho kamar yadda fuskarta ma tafi tawa tsawo. Idanuwanta dara dara farare tas, bakinta mai dan fadi wanda yake dauke da full lips shi kansa abin kallo ne. Kirjinta a chike yake taf haka hips dinta wanda yasa dole mommy ta dinka mata dogayen hijabs saboda in tana tafiya gaba daya jikin ta rawa yake yi. Hafsat mai class ce sosai, ba kowa take yiwa magana ba ballantana kaga dariyarta, amma in tayi dariya wani one sided dimple ne da ita ga kuma jerarrun hakora farare tas abin sha'awa. Ni kuwa mostly English wears nake Takawa saboda nafi feeling comfortable a cikin su. Kuma babu mai yi min magana saboda bani da komai a jiki na sai kyan fuska, wannan kuwa mutane da yawa sukance nafi Hafsat amma ni kam ban yarda ba, a ganina yawan murmushi na ne yasa ake ganin kyau na. Saboda shi murmushi ado ne musamman a gurin mace.
Muna shiga hall din gurin su mommy muka je muka gaishesu sannan muka je muka gaida Maman Amira muka tafi seats dinmu muka zazzauna, saboda an kusa fara taron. Kamar yadda aka saba, bayan bude taro da addu'ah sai aka fara gabatar da jawabai. Hafsat ta dauko novel dinta ta dora akan chinyarta ta fara karantawa ni kuma nayi tagumi da hannu bibbiyu ina sauraren speeches din daki daki. Sai da aka gama sannan aka kirawo passing head girl ta gabatar da farewell speech on behalf of the graduands. Lokacin har kuka nayi saboda tunanin shi kenan bazan sake ganin suba. Hafsat kuwa bama tasan me akeyi ba, sai da taji ina sheshahekar kuka sannan ta dago kanta ta kalleni ta kalli stage sai kuma tayi tsaki ta cigaba da karatun ta. Sai da aka fara rabon gifts sannan ta dago kanta ta rufe littafin da take karantawa ta mayar da hankalinta kan stage. A kayi ta kiran mutane ana basu gifts sannan aka zo kan set din mu. Kamar duk shekara, ni aka bawa overall san nan Hafsat second. Sai da aka gama rabon gifts sannan senior master ya hau kan stage ya fara announcement " I know all of u notice some strangers wearing strange clothes here" akayi dariya gaba daya, yaci gaba da cewa" they are NYSC members, they are sent here because the are the best in their various fields. The NYSC board wants this school to start participating in the scheme, that is why they sent this coppers to work with us. I hope you students will give them your maximum cooperation " daga nan sai ya fara kiran su daya bayan daya suna gabatar da kansu tare da fadin subjects din da zasu ke dauka da kuma classes din da zasu dauka. Tunda suka fara naji gabana yana faduwa, haka kawai naji jikina yana bani cewa something not so good is going to happen. Ina cikin haka naji wani daga cikinsu yace" my name is Ibrahim Adeniran Oluwaseun, from Ibadan. I will be taking SS2 mathematics and geography.
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine abinda nayi ta maimaitawa a zuciyata. Ji nayi tamkar an juya min dukkan plans dina na rayuwa ta. Mathematics is my best subject, maths teacher din mu is my best teacher, yaya za'ayi a chanja min teacher a hada ni da inexperienced copper? Ji nayi tamkar inbi su mommy mu koma gida saboda ji nayi gaba daya makarantar ta fita daga kaina. Ban kuma fahimtar me ake ciki ba saiji nayi ana hayaniya alamar an tashi daga taron. Cikin sanyin jiki na dauki gifts dina na tafi gurin mommy na kai mata, haka ma Hafsat. Mommy tana gani na tasan something is wrong, tana tambaya ta kuwa na fara yi mata bayani. Mommy akwai daukan zafi dan haka nan da nan ta jamu sai office din senior master ta fara yi masa bayani akan cewa tun da muna senior class bai kamata a dauki subject as important as mathematics a bawa copper ba, kamata yayi ace an bar coppers a junior classes. Murmushi yayi tare da cewa " na fahimci complaints dinki Ma, kuma insha Allah in ya fara daukan su in har sunga akwai problem, ina encouraging dinsu su zo su yi complaining. But first they need to give him a chance. We will all need a chance one day in our lives, one way or another". Da haka muka fito daga office din, mommy tana encouraging din mu akan as soon as muka ga bama gane teaching dinsa mu zo muyi complain. In ba'a dau mataki ba in tazo mana visiting mu gaya mata, in yaso sai tayi wa daddy magana yazo da kansa yayi solving issue din.
Table of Contents
Chapters
- 1 Episode One : The Beginning of the Beginning
- 2 Episode Two: Meet my Family
- 3 Episode Three: Loved by All
- 4 Episode Four: Moon's Sister
- 5 Episode five: The Strangers
- 6 Episode six: The Challenge
- 7 Episode Seven: The Thin Tall Man
- 8 Episode Eight: The New Imam
- 9 Episode Nine: Give Me a Chance
- 10 Episode Ten: I Don't Know
- 11 Episode Eleven : The Protector
- 12 Episode Twelve : This is Me
- 13 Episode Thirteen : This is Me 2
- 14 Episode Fourteen : The Limit
- 15 Episode fifteen: blood is Thicker than Water.
- 16 Episode Sixteen : The Letter
- 17 Episode seventeen: Reply
- 18 Episode eighteen: what's Next?
- 19 Episode Nineteen: The Goodbye
- 20 Episode Twenty: The New Job
- 21 Episode Twenty one: Amira
- 22 Episode Twenty Two: Efisowa
- 23 Episode Twenty three: The Break up 💔
- 24 Episode Twenty Four: The Heartbreak 💔
- 25 Episode Twenty five: The Eclipse
- 26 Episode Twenty Six: A Step Further Away
- 27 Episode Twenty Eight : University of Oxford
- 28 Episode Twenty Nine: The Message
- 29 Episode Thirty : The Final Blow
- 30 Episode Thirty One: Let it go
- 31 Episode Thirty Two : Munnir
- 32 Episode Thirty Two : Mahdi
- 33 Episode Thirty Three: Zayed
- 34 Episode Thirty Four : Back to Square One
- 35 Episode Thirty Five : When Destiny Calls.
- 36 EpisodeThirtySix: Interesting
- 37 Episode Thirty Seven : The Dinner
- 38 Episode Thirty Eight : The Shadow
- 39 Episode Thirty Nine : The Shadow 2
- 40 Episode Forty :TheShadow 3
- 41 Episode Forty One : Born for This.
- 42 Episode Forty Two : Born for This
- 43 Episode Forty Three: America
- 44 Episode forty four : America 2
- 45 Episode Forty Five : The Rush
- 46 Episode Forty Six : The Repentance
- 47 Episode Forty Seven : Amir
- 48 Episode Forty Eight : Awkward
- 49 Episode Forty Nine : Ya Habeeb
- 50 Episode Fifty : Munir 2
- 51 Episode Fifty one : Mommy
- 52 Episode Fifty Two : The Journey
- 53 Episode Fifty Three : Daddy
- 54 Episode Fifty Four : Her Father's Daughter
- 55 Episode fifty five : Her Father's Daughter 2
- 56 Episode Fifty Six : What You Sow
- 57 Episode Fifty Seven : What You Sow 2
- 58 Episode Fifty Eight : I Missed You
- 59 Episode Fifty Eight : For You, Only You
- 60 Episode Sixty : The Prince
- 61 Episode Sixty One : Save the Date
- 62 Episode Sixty Two : The Manager
- 63 Episode Sixty Three : Amira 3
- 64 Episode Sixty Four : The Past and the Future
- 65 Episode Sixty Four : The Visitors
- 66 Episode Sixty Six : The Wedding
- 67 Episode Sixty Seven : The Wedding 2
- 68 Episode Sixty Eight : The Wedding Night
- 69 Episode Sixty Nine: The Wedding Night 2
- 70 Episode Seventy : The Wedding Night 3
- 71 Episode Seventy One : The Honeymoon
- 72 Episode Seventy Two : My Everything
- 73 Episode Seventy Three : His Father's Son
- 74 Episode Seventy Four : The Cook
- 75 Episode Seventy Five : The Emir
- 76 Episode Seventy Six : The Visitors
- 77 Episode Seventy Seven : Amina
- 78 Episode Seventy Eight : The Storm
- 79 Episode Seventy Nine : The Lightening and The Thunder
- 80 Episode Eighty : The Skeleton in The Closet
- 81 Episode Eighty one : The Skeleton in the Closet 2
- 82 Episode Eighty Two : The Light
- 83 Episode Eighty Three : The News
- 84 Episode Eighty Four : Little Love
- 85 Episode Eighty Five : Ibrahim
- 86 Episode Eighty Six : The Phone Call
- 87 Episode Eighty Seven : Riyadh
- 88 Episode Eighty eight :Khairat
- 89 Episode Eighty Nine : Khairat 2
- 90 Episode Ninety : His Mother's Son
- 91 Episode Ninety One : His Mother's Son 2
- 92 Episode Ninety Two and Three : Maldives 1 and 2
- 93 Episode Ninety Four : RIP
- 94 Episode Ninety Five : The Light
- 95 Episode Ninety Six : The New Bride
- 96 Episode Ninety Seven : The Real Prince
- 97 Episode Ninety Eight: My Baby
- 98 Episode Ninety Nine : New Little Love
- 99 Episode Hundred : Not The End.