Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 9

Chapter 9

Budurwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nono dahar zata ce yasiya motarshi yashige yana shirin tadawa dagudu surbajo tasha gaban motor tana kuka tace cikin kuka haba bawan Allah Allah fa nahadaka dashi kaji tausayinamana Don Allah hankalin daddy ne yakai gurunta mamakine yakamashi Dan haka dakatar da alameen yayi sannan yabude kofar motor yakirata karasowa tayi jikinta har rawa yakeyi mommy ce tafara mgn dacewa yanmata Lfy cikin harshen fulatanci kasancewarta mommyn bafulatanace cikin Yaren fulatancin surbajo tabata amsa dacewa taimako nake nema akan asiyi nono da fura Dan inna koma gida yankani zatayi inbansiyarba inkuma najima agurin tallan Baffa dukana zeyi Don Allah kutaimakamin tausayintane yakama mommy bayani tayiwa daddy game da abinda surbajo tace tambayarta yayi da Hausa yace yarinya meyasa kika ga muyadace damu taimakeki share hawaye tayi sannan tace sabida naga kuna da kudi Dan wancam tanuna alameen da haushi duk yagama cikashi sabida batamusu lkcn datayi taci gaba naga yabiya kudin sa iska naira dubu guda amaimakon naira talatin shiyasa dariya sukayi harda sumunauwara daddy yace to tundaga ina kikazo nan tallan tundaga rugar yalli tabashi amsa jinjina Kai daddy yayi Dan yasan rugar duk sallah anan ake siyo shanun dayake rabawa mutane kuma agurin shi yallin wato ardon ke yar wanne gidace a rugar daddy yatambaya ni yar gidan ardoce mamakine yakamashi yace nasan shi yanzu ke yarsace washe baki tayi jin ance ansan baffanta tace eh Amman innata ta rasu no wonder inji mommy shiyasa ake doramata talla inbata siyarba adoketa shigo mota inji daddy yayinda yace munauwara dake gaban motor tadawo baya surbajo tashiga gaban arude alameen yawaigo yace haba daddy time is going fa inakuma zamu da ita gidansu zamu daddy yabashi amsa dakyar surbajo tayarda tashiga motar Dan gani take guduwa daita zasuyi seda sukasha fama da ita tayarda tashiga utone alameen yayi sannan yadauki haryar makarfin daddy kemasa kwatance dan surbajo tunda tashiga tarungume kwaryar nononta sanyin ac yafara dukanta tafara bacci yin baccinnata seda yabasu daddy dariya ita me gudun asaceta gata Tana bacci harsukazo makarfi surbajo baccinta take sha maman yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *page 17-18* Alameen tunda yadawo gida ko Aisha tabata masa rai baya damuwa sabida yanashiga damuwar surbajo take fadomasa arai yayita dariya shikadai Naira gomanta ko duk inda zashi da ita sabida inya Kalli kudin suna sashi nishadi yanason komawa rugar Dan yaga irin bidirin da zaayi in suka hadu da ita Dan yasan tabbas akwai artabu Anyi sallah da sati guda alameen yakoma bakin ayki Sosai wannan Karon yakejin dadin aykinnasa sabida baya tare da damuwa ko kadan Dan daya tuno surbajo yake samun natsuwa yauma tafe suke a mota shida amininsa Usman tambayarshi yayi yace yadai mutumin naga tunda kadawo daga pass gaba daya kasauwa dariya bata maka wiya kode madamce tasamu twins ne Murmushi alameen yayi Sannan yace hmm Usman kenan wanne irin twins Aisha zata samu abinda ranar dazan dawo naje mata sallama naga wasu tablet a kan mirror dinta a time din tana toilet nadauka nakaranta naga nahana daukar cikine abun yadauremin kai banmata maganaba sabida nasan kanta ta cuta Danni Wlh aure zan kara kwanannan Kai haba mutumina Usman yatambaya cike da murna Wallahi kuwa aure zan kara inji alameen tokodai soyayyace take saka yawan nishadi dariya sukayi gabadaya sannan alameen yaba Usman labarin surbajo Usman harda hawaye Dan dariya Alameen yaci gaba Usman Wlh bawai sonta nakeba sabida yarinyace gaba dayanta kawai drama dinta nakeso shiyasa nake ganin auranta kawai zanyi tazo gidana amatsayin cartoon inkalla inyi dariya Kokuma takalleka tayi dariya ba darabon kaine zaka zama cartoon din agurinta inji Usman yafadi yana dariya Haba Usman nidin yarone dazan tsaya ina shirme kawai nafadamaka for personal use zan ajiyeta dariya usman yakeyi sosai sannan yace Allah yabada saa amma Wlh zakace nafadamaka kaine zaka koma cartoon din at the end of the day Dariya alameen yayi yace zanko baka labari ni dannayi dariya kawai Zan auri yarinyarnan Wanda kaima intayi wani shirmen agabanka seka dara ********** Seda alameen yakwashe wata uku sannan yazo hutu wannan Karon besamu tarba daga gimbiyarsa ba shima bedamuba sabida badan ita yazo hutunba Dan madam surbajo yazo Iyayensa sunyi murna dazuwansa dama kuma sungaji da ganin shi a halin dayake sunason subashi shawara agameda rayuwar gidanshi Bayan yagaishesu mahaifinsa yace yanzu aminullahi haka kazabawa kanka rayuwa da macen dabatasan ciwon kantaba bazaka iya daukar matakiba duk Inda nafita labarinka Akeyi mace tamallakeka ko haka kaga Dan uwanka nayi anasa gidan haba aminullahi kasanifa mace itace mutum amma Kai ga irin wacce kazabowa kanka kayi tunani kagyara rayuwarka mahaifiyarsama fadan Tamasa dama kuma sunbarshine badan komaiba sedan kar ace suncika sa ido arayuwar yayansu godiya alameen yayi sosai sannan yashaida musu aure yakeson karawa sosai sukai farinciki dajin zancan dansuma abinda ke ransu kenan mahaifinshine yace aina kasamo matar aminullahi murmushi yayi yana sosa keya yace daddy kumma santafa faraace takaru afuskokinsu inda daddy yace Kai alhdllh wacece surbajo yabasu amsa gabadaya sukasamasa dariya mommy tace ikon Allah tagida ma kana fama ina zaka iya da shirmen surbajo ban hanakaba amma Allah yasanya alkhairi Kai kaji kagani daddy da tun dazu dariya yake seyanzu yace aminullahi na yar fillo to iyayenta sunsan dazancan aa yabasu amsa inade so daddy kaje kanemarmin aurannata badamuwa aminullahi daddy yafadi yana dariya sallama yamusu yatafi Dan dama yakosa sugama magana yatafi Dan surbajo yakeson gani yana fitowa yadauki hanyar makarfi shikadai dan bako inane yakeson excode Dinshi subishiba bare irin wannan tafiyar tazuwa yada manufa 😜 da azahar yaiso garin makarfi lokacin surbajo taje yo icce parking yayi akofar gidan dayake yau larabace mazan gidan suntafi cin kasuwa Dan kasuwar makarfi ranar laraba take ci surbajo ce tashawo kwana da iccen datayo akanta kamar amafarki taganshi atsaye ajikin motarshi habawa xubar da iccen tayi ta runtuma da gudu gurinshi Tana zuwa rigarshi takama Tana fadin yauwa wana Kama ay dama nafadi aradu nakamaka sekaji jiki gashiko yau kaida kanka ka kawo kanka har gida tabadi Tana kokarin gyara damararta da hannunta daya daya kuma Tana rike dashi Dan kar yagudu shiko alameen dariya abun yabashi Dan yasan zaa rina surbajo dataga yana dariya naushi ta dirka masa aciki sannan tacigaba da kaimishi duka takoina ba abinda keba alameen dariya seganin itace ke dukan Amman itace ke kuka Tana aradu Seka bani kudina bazan yardaba gashi dukan datakeyi ko zafi babu kamar badukannasa takeyiba be hanataba seda tagaji Dan kanta sannan takyaleshi Tana haki sannu alameen yamata yana dariya yace ammafa kinsha ayki dagowa tayi da jajayen idanuwanta datasha kuka tace jiki kamar karfe dukanka nakeyi amma ninakejin zafi aradu senamaka abinda koda wasa akace ka kuma yimin rashin kunya bazaka kumaba tafadi harda nunashi da hannu shide binta kawai yake da ido yayinda gefe daya kuma yana daukarta awayarshi shigewa gida tayi Takai iccen sannan tadawo ga mamakinsa tsugunnawa tayi agabanshi tanacewa Dan Allah kado kayi hakuri kabani kudina aradu nasha kuka sabida kudina daka gudu dashi danhaka seka karamin akan nera gomata kaji kado murmushi yayi sannan yace naji zanbaki kuma zan karamiki akan nakin tonikuma dukan dakikamin anawa dannima biyana zakiyi inba hakaba inje inkiramiki sojoji sukamaki akidime surbajo tamike Tana shirin guduwa jin yaambaci sojoji rukota yayi dasauri yace ina zaki muna magana kuma

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});