Chapter 5
Chapter 5
*page 9* Zahrau ta taso cikin tsana da tsangwama irinna kishiyar Uwa Sumaye ganamata azaba takeyi tun tana karama aka fara sata zuwa kiwo zuwa yanzu taiya sosai dama ga aladar gidan insun fita kiwo dare yamusu to acan suke kwana ingari yawaye su cigaba da kiwon sede laasar nayi zasu komo gida Shiyasa inzasu tafi suke tafiya da kanzo Wanda aka daka da gishiri da yaji da man shanu da tukunya sabida koda dare yamusu acan sugirka suci Kokadan zahrau batajin dadin zaman gidan inde mahaifinta bayanan sabida inyananan bame dukanta sosai yake jida ita kuma gata sunan mahaifiyarshi yasamata shiyasa ake kiranta da surbajo Yauma kamar kullum surbajo tafita kiwo ita da ya'u yayantane Suna zuwa rafi suka hadu da arera yar gidan alhaji jume itama tafito kiwon itada yaynta saidu Suna ganin juna suka rungume juna ita da areran sabida murnar ganin juna guri suka samu suka zauna suna hira surbajo ayko inada wani albishir dazan miki inji arera dagaske wanne irin albishir ne wannan kekuwa arera inji surbajo Aradu dama jae ne dan gidan alhaji Babba jiya yazo gurin yayana zubairu danaganshi muka gaisa shine yace wai ince miki yana gaisheki ihu surbajo tasa sannan tarungume arera tace kai madallah aradun Allah naji dadin wannan albishir Aydama nasan zakiji dadin shiyasa nafadamiki Ranar agurin kiwo wuni surbajo tayi tanajin dadi Dan harga Allah sakon gaisuwar da jae ya ayko mata ta sanyaya zuciyarta *JA'E* dane agurin alhaji babbah Dan kimanin shekara ashirin kyakkyawane naajin farko dan duk mazan garin bawanda yakaishi kyau shiyasa kowacce mace take kaunarsa gashida da kyauta dan inde yace yanasonki to ko zakici soyayyar gyada da burodi kimore gashi ranar kasuwa kullin kosanki da yar yau na musammanne Shiyasa kowacce mace burinta yace yana sonta to surbajo ma Tana cikin jerin masu sonnasa yau akwai biki agidan alhaji babba inda yake aurar da yarsa Safiyya yar kimanin shekaru goma shadaya Su surbajo sune kawayen Amarya sabida suma shekarunsu sha dayanne ga alada ta Fulani akwai wani wasa dasukeyi bayan shadi inda maza da yanmatane zasu taru suyi layi layin maza dabam haka namatama zasu fuskanci juna suna wakar Wayyohoro hirobe gadaibe jadu jande wayyo horo hirobe gadaibe jadu jande. Seme kalangu yasa kida to matanne daya bayan daya zasu dunga fitowa su tsaya a tsakiyar filin se tagama kallon samarin Wanda yamata acikinsu shi zataje ta yalo da kafarta yin hakan nanufin tanason yafito suyi rawa kenan kuma yawanci daga wannan rawarne soyayya take shiga tsakani hartakai ga aure to wannan bikinma anshirya irin wannan wasan Danhaka surbajo taruga kowa zuwa gurin sabida tanada gaba sabida basa son arugasu zaban jae sabida a alada irinta wasan duk Wanda kika zaba fita zakuyi tsakiyar filin kuchase sosai to inkuma yaji yanasonki zece kufita afili kusami guri kuyi mgn fili yacika bamazanba ba yanmatanba su kuma mazan kowa burinshi Allah yasa surbajo tazabe shi Dan itama duk yanmatan garin tafi kowa kyau anfara waka inda surbajo ce farkon fitowa tashigo filin tafara rawar Fulani irin wacce ake daga kafa dayannan ana saukewa sannan takarewa mazan kallo can idonta yasauka akan jae yanamata murmushi ayko batayi kasa agwuiwaba ta yaloshi ihu yayi sannan yashigo filin da kwambe suka fara rawa tare inda me kalangu yadunga wasasu dacewa kyakkyawa se kyakkyawa bayan sungamane jae yacewa surbajo Sudan fita afilin ay sauran yanmatan naganin sunfita kowacce haushi yakamata inda sukasha alwashin se summa surbajo dukan tsiya akan yaloshin datayi hakade yanmata da samarin suka ci gaba dawasansu har suka gama itako surbajo tunda jae yace sukebe farinciki yabi yacikata dantasan yau tafi kowa saa a duniya koda suka keben juya mishi baya tayi alamun jin kunya shimade kunyar yakeji Danhaka shima bayan yajuyamata sannan yafara mgn wato surbajo nadade inashonki amma nakasa fadamiki segashi yau Allah yakawo ranar dazan sanar dake danhaka Do Allah do annabijjo kishe kina shona.nide aradu ina shonki kunyace da dadi suka rufeta Dan haka ta ranta anakare takoma gurin arera gudun datayi shiyabashi tabbacin tanasonshi Danhaka agurin yafara rawar cin nasara Dan yasan yama mazan garin nisa maman yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *fans muna barar adduarku yaron da bashida Lafiya Allah yamasa rasuwa to kutayamu da addua Allah yajikansa yasa meceton iyayenshine sukuma iyayenshi Allah yabasu hakurin jure rashin sa ,rest in paradise my baby* *page 10* Tundaga wannan lokaci syy me karfi tashiga tsakanin surbajo da jae ko kadan basa son rabuwa da juna Yauma kamar kullum jae yazo hira gurin surbajo Akan wani ice suka zauna yayinda surbajo tajuyamasa baya sabida kunya Gyada takawomusu da burodi sunaci suna hirar Can jae yace surbajo aradu inna aureki nahaye nasan duk garinnan se andunga hirata saboda na auri sarauniyar mata Dariya tayi tasake rufe fuskarta sannan tace aynima hakanne Dan yanzu haka yanmatan garinnan haushina sukeji Dan rannan munje kiwo nida arera su haulen gidan ku suka tsareni wai sesunmin duka ayko nida arera muka hadu mukaimusu dukan tsiya dariya yayi sannan yace hauka sukeyi nibance inasonkowa acikinsuba shima Baffa cewa yayi inzabi wacce nakeso inde agarinnanne ze auramin nikuma nazabeki Dadine yarufe surbajo harseda sautin dariyarta yafito hakade suka gama hirar wacce yawancinta cin gyadar yafi yawa **************************** Al ameen yanzu yafita harkar Aisha kwatakwata harkar gabanshi kawai yakeyi yayinda mahaifansa zuwa yanzu sunfara bashi shawarar yakara aure kuma yabasu tabbacin ze Kara yana neman wacce yake sone fatan alkhairi suka masa alameen anturashi wani course kasar amurka inda seda yakwashe tsawon shekara guda acan yanzu idonshi yakara budewa ya waye fiye da tunaninku ko maganarshi yanzu tasauya Alameen Kenan Dan kimanin shekaru arbain da haihuwa amma babu me ganinshi yayi zaton yakai hakan Aisha ma yanzu bata da lokacinshi Dan yanzu tazama yar business Dan haka kasuwancinta yafiyemata komai Mahaifiyarta tanasane da irin tsiyar da Aishan take tsulawa agidan miji amma kda wasa bata taba tsawatarmataba sabida gudun kar abin arzikin da Aishan take kawomata tadena Su Ruky suma kullum cikin bata munanan shawara suke inda ahalin yanzu har sata takema alameen din yasan tanamishi satar Amman ko afuska be nunamataba Dan yafuskanci bata da wadataccen hankali *************** surbajo Ankara zama yanmata inda yanzu shekarunta sha biyu da haihuwa Dankaka yanzu sumaye har tallan nono da fura take doramata tabi yanmatan rugar sukai cikin garin makarfin ranar dabata siyarba dukan tsiya take mata shiyasa surbajo bata dawowa gida da wuri matukar tasan bata siyarda nononba Se tara nadare take baro cikin garin kamin tagama keto dajin ta iso rugarsu goma tayi haka baffanta zetamata fada itade sede tai tabashi hkr itakuma sumaye na zugashi da cewa maza tafara bi shiyasa take dare bata dawoba itade surbajo sede kuka wasawasa seda kaiwa dare agurin talla yabi jikin surbajo sabida bata da kan kasuwa Dan wani lokacin setakai laasar baasiya ko na kwaboba gashi nonon yafi Nakowa yawa acikin wainda suke zuwa tallan tare duk sanda ta dawo se baffanta yazaneta sannan yamata fada akan dolene setayi cinikin inbata siyarba ta dawo mana inya tambayi sumaye ko itace take cewa surbajo karta dawo seta siyar munafukar har kuka take sawa tace haba alhaji yazaayi nacemata haka koban haifeta ba ay yatace kuma nasan hatsarin dake tattare da hakan da irin wannan kalaman take Rufe bakinshi insuka koma daki ita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34