Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Budurwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fuska se raini yanemi yashigo to contract ne kuma yakare bukatar maje hajji sallah Dan haka karka nemi ka takuramin amfaninka nawannan lokacin agurina yawuce sewani jikon tawuce tabarshi agurin jiri ne yafara daukar alameen dasauri yazauna yadafe kanshi yana karanta adduar datazo bakinsa wato Aisha tayaudareshine da duk abinda tayi Dan yabiyamata bukata badan Allah ba wannan wanne irin balaine dakyar yasamu zuciyarshi tadena zafi yana zaune agurin tazo tawuceshi tafita yawonta mikewa yayi jiki bakwari yanufi gidan iyayensa sosai sukayi murna dazuwanshi daddy ne TaiwanYauwa aminullahi dama Kabir nake jira yazo na aykeshi tunda gaka kazo sekai kaje cikin ladabi da biyayya yace to daddy ina zanje rugar yalli inda muka taba zuwa muka Kai wata yarinya gidansu can Zan aykeka kasiyo shanu dazaa rabawa mutane carab munauwara taamshe daddy cewa zakayi gidansu me kiranshi kado budurwar jae zaka aykeshi gabadaya falon sukasa dariya duka alameen yakaimata ta gudu kudi daddyn Tamiko Yamiko masa a ledar viva yace gasu miliyan ukune kasiyo yadda yakama murmushi alameen yayi sannan yaajiyewa daddy kudinsa yace ze siyomasa danashi kudin inda sabo daddy sunsaba da kyautatawa daga alameen din albarka sukai tasamasa yamusu sallama yatafi bayan daddy yatambayeshi zegane gidan yace eh zegane har munauwara nacewa kode tazo tarakashine yamata banza yawuce da azahar ya iso garin yana faking surbajo nafitowa zata tafi kitso tsayawa tayi Tana kallonshi yayinda shima tsayawar yayi yana kallonta cike da TaiwanTsiwa tace aradu wannan kadon bayan bakin halin har maita gareka yoto inba mayeba taya zaka tsaya kana kallona kamar nacimaka bashi nagade kudin daaka bani kyauta aka bani kuma bakai kabaniba baffankane bare kace sukazo ansa sede idan bakin halin nakane zaka gwadamin aradu ko dakasha sanda Danni bani daukar raini tafadi harda murguda baki alameen dariyace takwacemasa tabbas ya yarda da zancan mutane dasuke cewa yanfulani Nada katobara surbajo ganin yanamata dariyane yasa takwance dankwalin kanta tasake Damara dashi dama akwai wata damarar daure akugunta karasowa tayi gabanshi tatsaya taruke kugu ita ala dole zatayi maganinsa tunda yake mata dariya wata dariyarce tasake kamashi yace ikon Allah yau nahadu da gamona inba hakaba taya daga zuwana bancimikiba ban shamikiba kitareni da balai surbajo tsayawa tayi Tana kallonshi tunda yafara dariya dimples dinshi suka lotsa hankalinta yakoma kanshi aranta tace Ashe akwai Wanda yafi jae kyau dama bansaniba hannunta takai dede setin dimples din ta taba dariyar dayakeyine tatsaya sakamakon jin antabashi afusace yajuyo zekaimata duka dagudu takwasa Tana cewa woo nacuceshi nataba ramin nacuceshi nataba ramin harta kule yadena ganota haba alameen mezeyi inba dariyaba shi tunda yake betaba nishadi irinnayauba yana dariyar ne ardo yafito yasameshi ganinshine yasa yadena dariyar da faraa yanufeshi suka gaisa ardo yamasa iso zuwa cikin gidan anan alameen yafadamasa abinda yakawosa zagayawa dashi ardo yayi gardengarken shanun yagama zaba yabiyashi kudinsa inda harda ihsani yamasa sannan yabaShi kudin daze dauko motor dazaa zuba shanun akawo musu kaduna Dan dama inaka siya ardonne yake kaimusu sallama yamasa yatafi bayadda ardo beyi dashiba yatsaya yatafi da nono amma yaki yafara rakiyatafiya kenan yahadu da surbajo tadawo daga kitson tsayawa yayi Dan yaga tanufoshi soyake tasake bashi dariya Dan duk wani bacin ran da Aishaaisha tasashi dariya da surbajo tabashi dazu yakawar masa dashi karasowa tayi tace kado zaka tafine kai yadagamata yana murmushi tace to Dan Allah kabarni nasake taba ramin fuskarka aradu bazan fadawa kowaba inma bazaka Bari nataba Dan Allah ba togashi kabarni nataba a naira goma tafadi tana kwance habar zaninta tadauko naira goman dariya alameen yakeyi danshi Wlh yanzu kallonta yake tamkar katoon Mika hannu yayi yaamshi kudin sannan yatada motarshi yatafi yabarta dagudu tabi bayan motor Tana cewa kado katsaya kabani kudina gudu take iya karfinta alameen na kallonta ta mirror yana dariya dataga bazata iya kamoshibane tace kaci wuta balbal ban bakaba tadauki dutse tawurga ma motar dayake surbajo ta iya jifa seda tasamu motor Alameen Allah ne kawai yakaishi gida Lfy Sabida daya tuno surbjo dariya yakeyi lalle ya yarda fillo akwai wowta baabinda kebashi dariya irin nacuceshi nataba ramin wannan Abu nabashi dariya ahaka har yaiso gida itako surbajo Allah yaisa tajata yafi kwando dubu sabida naira gomanta Dan kudin da daddy yabata gona ardo yasiyamata dasu goman data ba alameen ardone kullum yake bata goma takashe toshine tayau alameen yagudu da ita har kuka tayi akan naira goman koda sukaje makarantar dare kasa karatu tayi sabida gomanta yayinda tasha alwashin duk randa taga kado seya sani taku har kullum Maman Yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *page 11-12* Alameen yadawo hutu inda yasamu labarin anyi rasuwa akano zasu tafi gaisuwa duka family dinsu Ayko haka suka rankaya gaba dayansu harda matar kabeer da yaransa gabadaya ran alameen ne yabaci ganin batashi matar acikin ayarin Mota biyu sukayi kabeer ke Jan motar da iyalinshi suke ciki yayinda alameen kejan wacce iyayensa da kannansa suke ciki Dan be tafi da excode dinshiba sabida gaisuwa zasu Sun isa kano Lfy sunyi gaisuwa an karbesu cikin mutunci da karramawa Seda laasar suka kamo hanyar dawowa gida Dan ba kwana zasuyiba ************** Surbajo yau dawuri ta shirya ta tafi tallan nono Dan Tana gudun tayi dare kuma tasha alwashin yau intaje talla rokon mutane zata dungayi akan su siya Tayi kwalliyarta cikin kayansu na Fulani inda fuskarta tacikata da digedige duk asunan kwalliya bakinta tacikeshi da bakin kwalli gaba daya dan Tana tunanin rashin yin Kwalliyar ne yasa baa siyan kayanta sallama tayiwa sumayen tadauki kwaryar nonon ta wuce Koda tazo cikin gari jamaa bame bitakanta bare asiya kota rokesu basa siya Dan haka kuka tasa taci gaba da bin mutane akan su siya haka tadunga bi kwararokwararo akan asiyi nonon mutum Hudu ne kawai suka siya ga nonon da uban yawa haduwa tayi da Mari yar rugarsuce ita har ta siyar tambayarta tayi Don Allah Mari ina kike kai nono da furarki asiye Dan Allah kifadamini Murmushi tamata sannan tace aradu da nisa Dan sekin hau mota naira dari zaa kaiki a akori kura Dasauri surbajo tace fadamini Dan Allah aradun Allah zani Tashar yarine tabata amsa daganan tajata takaita inda zata hau motar Godiya sosai surbajo tayi mata tahaye motor akori kuran suka tafi ************** Alameen tafiya suke suna hira cikin nishadi sabida daddy bayason gudu amota shiyasa ahankali yake tafiya sabanin kabeer Wanda yakusa shiga kaduna Dan cewa yayi baze iya tafiyar wahainiya ba suna zuwa tashar yari tayansu Yay faci dole Al ameen yay parking agefen titi dede wani masallaci gurin akwai jamaa sosai kamarde kasuwa fitowa yayi Dan yanemi Mesa iska yasamusu suwuce agefe yaga Mesa iskar Danhaka yace yazo yasamusu dasauri Mesa iskar yasakamusu sabida ganin dankareriyar motor dasuke ciki 1k alameen yabashi mutumin se godiya yake karaf a kan idon surbajo hakan ta faru Dan haka dasauri takaraso inda alameen keshirin shiga yatada motor dasauri tace sannu bawan Allah Don Allah kataimakeni dasauri alameen yajuyo jin zazzakar murya namishi mgn arba yayi da surbajo dauke da kwaryar nono akanta durkusawa tayi tana kuka tace Don Allah kataimakamin kamar yadda Allah yataimakeka kasiyi nonon nan da fura wlh inna koma dashi bansiyarba yankani zaayi kuma inna Dade agurin tallan Baffa yace seya yankani takara rushewa da kuka alameen mamakine yakamashi to inbanda haukar fillo shi mezeyi da fura da

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});