Chapter 31
Chapter 31
dannasan aranka sokake katafin gulma ce kawai irin taku ta maza masu bakin ganga Kaga kawuce ni na rufe k'ofata". Murmushin taka'ici yayi,yajuya yafice daga gidan,hotel yakama yakwana washe gari yawuce kaduna,shi abunma dariya yake bashi wato da gaske ne kenan zancan da maza sukeyi nacewa in matanka suka had'a kai to wlh ubanka zasuci, shide ko ba haka bane shi yayarda tunda gashi sanadin had'in kannasu kowa batason shiga hakkin kowa shi Kuma sun maidashi kamar ball wannan ta buga ta ba wannan. Maman Yusuf ππππππππ *SURBAJO* ππππππ π Zahra Muhammad Mahmud *this page is dedicated to Muhammad indimi family more especially Presido Adama,maryam,hauwa,Allah yakareku a duk inda kuka shiga nagode* *pure moment of life writers* *p.m.l* *page 85-86* Ya iso kaduna lfy a kitchen yasamu Aisha tana wanke wanke,tabaya yaje ya rungumeta yace, "Ta honey me ake tanadarmana ne haka",da sauri tajuyo tana kallonshi cike da mamakin ganinshi zatayi mgn yarigata, "wlh koroni tayi ko gidan bata bari nakwana ba wai dole sena dawo gurinki nasan cewa zakiyi Meya dawo Dani yanzu to koroni akayi kuma wlh bawacce zata K'ara korata na koru,nadawo nan bayan Sati biyu zantafi laifin damuka yimata ta yafe, so banason wani dogon turanci,"yafad'a yana d'aure fuska gudun kartaga k'ofar rainashi. Abun dariya yaba Aisha ganin yadda yake kumbura, janshi tayi suka koma d'akinshi taimakamasa tayi yayi wanka yashirya suka sakko suka ci abinci sannan yakira Surbajo awaya bayan sungaisa yaba Aisha nan fa suka shiga hira bame cewa kishiyoyine, seda kud'in wayar yak'are suka hak'ura. Rayuwar su taci gaba da tafiya Cikin so da k'aunar juna babu meson ganin bacin ran d'an uwansa.babban fili Al-ameen yasiya a Kaduna a anguwar governor road yasa aka gina masa gini nagani na fad'a gidan samane akayi part uku amman anyi babban falo tsakiyar sannan se step Kowanne b'angaren danashi anyi kuma k'ofofi ta waje wanda kowa zefita yashigo batare da wani yaganshiba. Dukiya yazuba agidan bata wasaba ba abinda babu harda garden da swimming pool da filin ball madaidaici kai komai de yaji, cikin Surbajo na wata tara suka tare a gidan ita da Aisha yayinda shima yanemi transfer zuwa Kaduna da ayki, gidan inka shiga kaga yadda kowa ke tattalin kowa abun seya burgeka babu kishi na fili agidan sede na b'oye wanda a ko'ina akwaishi, Yanzu Yusuf yakoma hannun Aisha Itace keyimasa duk abinda yakeso,hakan bak'aramin dad'i yakewa Surbajo ba haka shima uban tafiyar, Wata safiyar laraba Surbajo ta tashi da ciwon nak'uda Wayyo Jama'a zokuga Aisha zaka rantse da Allah Itace take nak'udar dan Surbajo ma tafita dauriya, ko a asibiti dasukaje haka taita rusa kuka harse da Allah yasauki Surbajo lfy inda tasake haifar namiji zokuga murna gurin Al-ameen jiyake kamar ya goya Surbajo dan dad'i. Ranar suna yaron yaci sunan baban Aisha suna kiranshi da hanif,kukan da Aisha tayi na godiya ga Surbajo baya fad'uwa rasa inda zata sa hanif tayi sonshi take fiye da kanta jitake tafi Surbajo sonshi har tausayinta Surbajo tadunga Ji, yayinda taci gaba da addu'ar Allah yaba Aisha haihuwa Itama taga d'anta . Duk wata kulawa da dawainiyar yaran Aisha ce keyi kullum yayinda Surbajo itake ke yimusu girki kullum gami da gyaran gida sam ta hana Aisha yin komai d'akinta kawai take gyarawa se kuma na Al-ameen ranar datake da girki,kai dole Rayuwar gidan ta burgeka, ko ruga Surbajo zataje tare suke zuwa haka Itama in zata gidansu.wani lokacin har mantawa suke waye me girki acikinsu se shine ke tuna musu wacce keda girkin.duk abinnan Al-ameen jin surbajo yake tazama shi yazama ita dan yasan zaman lafiyar gidanshi yasamune ta dalilinta son dayake mata ko da wasa baza'a had'ashi dana Aisha ba ji yake in yarasa Surbajo shima yagama ayki. Maman Yusuf π?ππππππππ *SURBAJO* πππππππ Zahra Muhammad Mahmud *this page is dedicated to my fans on facebook thanks for the care and support* *pure moment of life writers* *p.m.l* *page 87-88* Waiwaye adon tafiya Ruky tunda ta auri baballe bata tab'a sanin meye sana'ar saba.kullum cikin cin dad'i suke hankalinsu akwance kwatsam wani dare y'an sanda suka dira agidan su abin yabata mamaki dataji suna zargin baballe da laifin fashi da makami har sunshiga gidan wani Alhaji sunyiwa y'arsa fyad'e,shine aka kama sauran suka tonashi tanaji tana gani aka tafi dashi police station. Kotu aka shigar dasu K'ara inda aka yanke musu hukuncin Kisa ta hanyar harbi da bindinga bayan Kotu ta kwace duk wata kadara dasuka mallaka, Ruky haukane kawai batayiba tana gani aka harbe mijinta wanda tafiso fiye da rayuwarta,tashiga halin k'unci da bakinciki dole takoma gidan iyayenta da zama domin yin takaba. Zuly kuwa taci gajiyar soyayya domin cutar zamani musa yad'ebo ya shafa mata tana cikin mawuyacin hali gashi yak'i dena halinnashi yace seya shafa ma mutane da yawa shima, Zuly Itama fatanta kenan tashafawa Jama'a acikin burinnata shine aminanta yadace tafara sawa,wato Ruky da Aisha. Yau gidan su Ruky Zuly taje da niyar yimata gaisuwa, bayan sungaisa suka shiga hirar duniya,Ruky tamik'e zata fita,carab Zuly tace," ina zuwa kuma muna hira?" "Kinga wallahi yaro zankira na aykeshi yasiyomin reza Zan yanke farce na sun taru," Murmushi najin dad'i Zuly tayi,sannan tace, "lah karki bata kudinki Inde reza ce inada ita ajaka sabuwa zauna ma na yanke miki farcen",Abun yayiwa Ruky dad'i bamusu ta zauna Zuly tafara yankemata farcen da rezar data yanke hannunta jininta yashafa dama tayine dan tayi amfani da ita gurin aykata manufarta,tana Cikin yanke mata ta yanke ta da gangan nanko jini yasoma tsartuwa agigice tasaki hannunta kamar gaske tafara kuka wai bata sani bane,murmushi Ruky tayi tace,"haba kawas dan tsautsayi yafaru shine kike kuka Wlh karki damu kanki bari nasa kalanzir." Ranar wuni Zuly tayi agidan su Ruky inda a karshe suka tsaida shawarar Sati biyu masu zuwa Lokacin Ruky tafita takaba zasuje gidan Aisha subata hak'uri amman zuciyar Zuly ba haka bane manufarta dabam. Aji dad'i Yaude Aji dad'i tasha alwashin sake kiran Al-ameen, Lokacin data kira Surbajo ce Kusa da wayar Al-ameen yafita training, da kamar karta d'auka cande ta d'aga muryar mace taji tana fad'in, "Haba namijin duniya don Allah Kadena wulak'antani wlh sonka nakeyi ni ko bazaka yimin komaiba don Allah Ka kusanceni ko so d'ayane wlh na kwad'aita dakaine Shiyasa." Hankalin Surbajo ne yay mugun tashi kashe wayar tayi, dabara ta fado mata ta tura text da cewa, "Tunda kin takuramin kizo kisameni agidana nikad'aine agidan kizo yanzu kuma namiki so d'aya bazan sakeba," tatura mata gami da Address. Lokacin da sak'on yashiga wayar Aji dad'i jitayi kamar tazuba ruwa ak'asa tasha fad'i take,"wato nid'in mesa'ace ashe rabon sake ganinshine yakawoni Kaduna gaskiya nagode wa Allah,"tashi tayi tashirya cikin wasu tsinannun kaya tasha magungunan tsumi harda na matsi sabida aji komai zam zam. Kai tsaye gidanshi ta nufa. Surbajo ko tana gama tura text d'in d'akin Aisha taje da gudu ta sanar da ita zasuyi bak'uwa da manufar zuwanta ,nanfa suka ruga da gudu zuwa kitchen domin tarbar bak'uwar tasuπ Maman Yusuf ?πππππππ *SURBAJO* πππππππππ Zahra Muhammad mahmud *INA KUKE MARASA AYKIN YI SENA GULMA?KUZO GA AYKI NA SAMAR MUKU, TUNDA NAGA RASHIN SHINE YASA KUKA TASA NAMANA D'ANYE KUNA CI.NAYIWA INDIMI FAMILY DEDICATION YASA KUNKASA ZAUNE KUN KASA TSAYE TSOHON BASIR YA MOTSA TO GAWANI SABO* *THIS PAGE IS DEDICATED
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34