Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Budurwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tafiyar Tata seta karamata kyau dan wasu dauka sukayi yanga takeyi harsuka karasa gurin cake din alameen besaketaba koda suka tsaya zagayo da hannunsa yayi ta kugunta yariketa ahaka suka yanka cake din aka tafa musu MC yace Amarya taba ango abaki cikin harshen turanci surbajo batajiba alameen ne yaradamata akunne waigowa tayi tana harararsa akan yace tabashi abaki shikuma yana murmushi wayyo jamaa zokuga yadda wannan kallo da surbajo tayi yakoma na so da kauna ga alameen yanata murmushi yanko cake din surbajo tayi tanufi bakin alameen kara rungumeta alameen yayi ta kwantar da kanta a kirjinshi ahaka tasa mishi cake din abaki huuuuu kawai mutane ke fadi dan wasu liki suka fara zuwa suna musu agurin dankoni Sun burgeni shima alameen ahakan yabata cake din tana kwance ajikinshi bayan sunkoma gurin zamansune aka bukaci ango yayi Godiya ga jamaar dasuka taru dominsu nan alameen yayi jawabin cikin harshen turanci bayan yagama aka bukaci Amarya tayi itama alameen ne yafada mata abinda MC yace yakara dacewa tayi da hausa kuma don Allah karta dunga sako aradu Γ  maganar murmushi tamasa Wanda yadauki hankalinsa sannan taamshi loudspeaker tafara magana cikin harshen filatanci wow bakaramin burge mutane tayiba danko babu Wanda yayi zaton batajin turanci bayan tagama ne akabukaci ango da Amarya su fito fili su taka alameen ne yarukota suka fito filin yana rungume da ita aka samusu wakar da Sani slowly yamusu ta auransu suka fara takawa a hankali nanfa kowa yamike yafara yiwa ango da Amarya liki aisha kuka take harda majina n'a bakinciki da sauri aminanta suka fitar da ita daga cikin hall din gudun karsuyi abin kunya kai tsaye gida suka nufa da ita suna bata hakuri itako fadi take wayyo Allah alameen yakasheni yacuceni yarasa wacce ze auromin amatsayin kishiya se wannan gogaggiyar Yar bokon😜 nabani ni aisha sude hakuri suke ta bata acanko ango da Amarya ne keta cashewa baa tashi ataronba se goma nadare suna dawowa aka sa surbajo tayi wanka aka shiryata cikin shigar alfarma aka nufi gidan mijinta da ita maman yusuf πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *SURBAJO* πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ Zahra Muhammad mahmud Zahramuhammadmahmud.blogspot.com *page 31-32* Ankai amarya Lfy inda dangin mahaifiyarta suka kara yimata nasiha game da zaman gidan miji itade surbajo se kuka takeyi Kamin goma nadare kowa yawatse anbarta ita kadai Bilkisu ce tace mata takulle kofarta karta bude se intaji alameen ne ayko haka tayi kulle kofar tayi duk da bata iyaba seda bilkisun takoyamata Gefen gado tasamu tazauna tadunga bin dakin da kallo irinna kauyanci komai yamata kyau sede ita wasu abunma batasan menene shiba Siket da rigane ajikinta nawani material purple colour semayafin data rufa dashi fari takalmin kafarta ma farine kanta ba dankwali sede farin ribom daaka kama mata gashi dashi Mikewa tayi tacire mayafin dan tagaji tunda aka fara bikinta take rufa mayafi to itade yau tagaji shiyasa tacire Falonta tadawo tazauna akan two sitter sanyin AC naratsata komai na falon yaburgeta zamanta bajimawa taji ana nurking din kofar mikewa tayi taleka ta ramin da Bilkisu tace tadunga lekawa Alameen tagani tsaye shikadai bude kofar tayi takoma gurin zamanta tazauna Da sallamarsa yashigo Suman tsaye yayi lokacin dayayi arba da surbajo tamasa kyau sosai musamman gashinta daya zuba har gadon bayanta bakikkirin se shining yakeyi Ledar daya shigo da ita yaajiye sannan yasami daya daga cikin kujerun yazauna surbajo amare kallonshi kawai takeyi ba um ba umum shima itadin yake kallo murmushi yayi yace baby na babu ko gaisuwa irin wannan shan kamshi haka konayi laifi ne murguda baki tayi tace yoto shikenan sokake insaki baki inta zuba agabanka kaidin daba kunyace gareka ishashshiyaba yanzu kace zaka daukeni kamar wata yarka to aradu kakiyayeni kajide nafadamaka tafadi Tana Kara daure fuska ita ala dole batason raini dariya zancannata yabashi babu abinda yake burgeshi da ita irin son girmanta mikewa yayi yakoma kujerar datake kai dasauri tamike tana shirin barin gurin cikin zafin nama yarikota tafado kanshi Riketa yayi tayadda bazata kwaceba sannan yace baby na Wlh bakida kunya ke kodan irin kukannan da amare keyi in antafi anbarsu bakiyiba Dan mayafin dasuke rufe fuskarsu dashi shima bakiyiba kin yiwa ango magana dawuri se ansiyi baki shima duka bakiyiba se rashin kunya kikemin to ki kiyayeni ko yanxu nayi Maganin rashin kunyar taki yafadi yana shafo gashin kanta Surbajo kokarin mikewa takeyi Amman yahanata ayko budar bakinta se cewa tayi hddijan amma aradu kado akwai raini yo inbanda abunka ko kukan nakeyi aka kawoni gidannan me shegen kyau ay aradu nadena kukan kuma wannan kayan kyalekyalen duniyar inna rufe idona ay bazan gansu da kyauba kuma dakake cewa nayi magana da wuri badole inmaka magana da wuriba gudun kar kace zaka lashemin bakina kamar tsohon Maye ni wallah narasa mekakeji acikin lashewa mutane baki kallonshi tayi sannan tace Don Allah kado mekakeji inkana tsotsewa mutane baki batagama fadin mezata fadaba yahada bakinta danashi yashiga kissing besaketaba seda yaji dakyar take numfashi kallonta yayi yaga jikinta yamutu murmushi yayi yace baby to kinji abinda nakeji inna lashewa mutane bakin surbajo baki yamutu mikar da ita yayi suka shiga kitchen dinta dake falonta yadauko plate da cup suka dawo falon ledar daya shigo da ita yadauko yajuye naman kaza a plate din sannan ya tsiyayamusu fresh milk a cup yamatso dasu gabanta wayyo surbajo idonki idon nama ay tuni ta watsake daga kasalar da yasamata takai hannu zata dauki naman caraf yarike hannunta yace au ci zakiyi batare danamiki tayiba wani kallon banza tawatsamasa sannan tace aa kallonshi zanyi kamar yadda kaima naga kanayi murmushi yayi yace inde zakici namannan to akwai sharadi inde kikaci sekin biyani ko ajikinta tace inde biyane me saukine zanbiya koma menene bani naci murmushi yayi sannan yamikamata seda taji takoshi over sannan tahakura da naman sannan tashanye cup biyu na fresh milk din mikewa alameen yayi sannan yamika mata hannu takama yadagata toilet suka nufa brush yadauko yamiko mata bayan yasa maclean kallonshi tatsayayi danbatasan amfaninshiba mamakine yakama alameen ganin surbajo batasan brush ba Amman bakinta baya wari kwatantamata yadda zatayi yayi wayyo shazumamu aytana gogawa taji zakin maclean tas tashanye kumfan hankalinta kwance tamika masa brush din yakaro mata wani Kobe tambayaba yasan shanyewa tayi dariya yashiga Yi sannan yasamata wani yacemata inde tasake hadiyewa mutuwa zatayi Dan yaganota mutuwace kawai kebata tsoro ayko bata sha dinba duk da ranta naso haka tadunga zubarwa har suka gama suka dauro alwala suka fito shiyajasu sallah rakaa biyu ta nafila bayan sun idar yamata tambayoyi gameda addini ga mamakinsa duk tabashi amsa dede sabanin Aisha mayafinta yabata tarufa yaja hannunta zuwa falonshi zaunar da ita yayi sannan yanufi dakin Aisha sallama yayi yashiga tanajinshi tamasa banza karasawa yayi yasamu guri yazauna bata gaisheshiba shiya gaisheta sannan yace tazo falonshi ο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώ?????????????????? *SURBAJO* ?????????????????? Zahra Muhammad mahmud *page 33-34* Yace tazo falonshi yanason yayi magana dasu yana gama fadamata bejira amsartaba yabar dakin yakoma falonshi inda surbajo kezaman jiranshi Bejima ba Aishan tashigo ko sallama babu. Surbajo seda ta tsorata da ganinta Dan ita bata dauka yanada wata matarba Guri Aisha tasamu tazauna Tana girgiza kafa Tana cika Tana batsewa Alameen ne yafara magana bayan yabude taro da addua sannan yafara yimusu nasiha akan su zauna lafiya bayason rigima da tashin hankali agidanshi Bayan yagama jamusu kunne sannan

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});