Chapter 13
Chapter 13
jiran abude motar tsawon minti goma baa budeba yasa Momy tambayar daya daga cikin sojojin Kai wai amaren basu isobane ko bawannan bace motar amaryar Cike da girmamawa yace madam Amarya taiso amma oga shima yana cikin motar bande san abinda yahanasu fitowaba sede ko zakije ki gani Murmushi Momy tayi sannan aranta tace dakyau aminullahi wato mu zenunawa yayi Amarya ko zeci uwashi ne dawannan shegen rawar kan munauwara takira tace taje gurin motar tace injita tace aminullahi yafito da Amaryar haka kota sabamasa dagudu munauwara tanufi motar abinnema yasamu Dan ita akwai son Amata irin wannan ayken nurking glass din motar tayi seda tadan jima tana nurking din sannan yasauke glass din motar ganin munauwarace Yana saukewa idonta yasauka kan surbajo dake ta faman bacci kwance ajikinshi Dariya tayi sannan tace Bross kana hutawafa to mommy tace Wlh ranka ze baci inbaka fito da amaryaba tafadi Tana dariya takara dacewa su Bross ko kunya juyawa tayi da gudu zata bar gurin dasauri yarukota yace zaki sani wato ninema mara kunyan ko kwacewa tayi taruga gurin mommy Tana dariya tace mommy Wlh amaryar ma bacci takeyi maybe shine abinda yahanashi fitowa daga motar bata rufe bakiba taga daya daga cikin sojojin yanufi motar yabude kofar Alameen ne yafito sannan yamika hannu yadauko surbajo dake bacci Yanufi su mommy nanfa abokanan wasa suka shiga tsokanarshi masu dauka awaya suna dauka Dan abun koni yaburgeni jin hayaniya da surbajo tayine yasata farkawa ganin abinda kefaruwane yasata Fara kiciniyar kwace kanta Dan gaskiya kunyace takamata sosai Ganin tanason saukane yasa alameen sauketa Lafayar dake jikinta takara ja tarufe fuskarta jikinta se rawa yake sabida kunya mommy ce takarasa ta rungumota tana fadin barka da zuwa cikin zuriata Allah yasadamu da alkhairin dake tattare dake yakawar da sharrin Ameen sauran jamaar suka amsa daganan aka shige da ita cikin gidan falon daddy aka kaita alameen ma yabi bayansu nasiha sosai daddy yamusu inda akarshe yagargadi alameen akan yarike amanar yar mutane kuma yayi adalci atsakaninsu daganan akawuce da surbajo part din mommy domin shiryata zuwa gurin dinner shima part dinshi na gidan yanufa Usman yatarar da wasu abokansa su biyu suna hira dashigarshi suka juyo kanshi suna tsokanarshi babu kamarma Usman harda cewa shi ko alabari betaba jin ango Mara kunya kamar alameenba dariya alameen yayi sannan yace Kai alhdllh nagodewa Allah dayasa nazama nafarko atarihi duka suka kaimasa dukansu suna dariya daganan suka shiga shirin zuwa gurin dinner wacce zaayi a bafra international hotel dake no11b yakubu avenue off alkali road unguwar rimi kaduna Sosai suke shiri inda Amarya mommy tadauko me kwalliya tashiga yimata sosai tayi kyau wedding gown akasamata light blue gaskiya bame kallonta yayi zaton wai shekarunta sha hudune sabida surbajo akwai Kira kuma bame zaton tasan hanyar wani abu waishi kauye bare aje ga ruga ita kanta data Kalli kanta a mirror tantama tashigayi akan anya itace kuwa alameen ma shadda yasa light blue shima yayi kyau sosai yayinda sauran abokansa suka sa farar shadda kawayen munauwara sune suka zama yanmatan Amarya dangama surbajo baazo da kawarta kodayaba suma yanmatan Amarya fararan dogayen riguna sukasa yayinda Suka daura head ja takalmi ja gaskiya sunyi kyau takwas nadare motoci suka fara dibar mutane zuwa gurin taron yayinda uwargida Aisha ma tagama shiryawa cikin wani yellow din material doguwar riga takalminta red head dinta ma red Jakarta ma red ce se mayafin Data Dan yafa shima red itama ba laifi tayi kyau aminanta kuma pink din material suka sa da duk wani Wanda yazo ta bangarenta duk pink sukasa muje zuwa maman Yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *page 29-30* Gabadaya jamaa sungama tafiya gurin dinner se Amarya da ango yarage Motar dazasu tafi aciki ta iso dan haka alameen dakanshi yanufi falon Momy inda surbajo kezaman jira dan babu kowa agidan duk Sun tafi harda su mommyn Dasallamarsa yashiga falon dakyar surbajo ta amsa gamida dago fuskarta Wow itace kalmar alameen tafarko jikinshi narawa yakarasa gurinta hannunta yakamo yamikar da ita tsaye yayi hugging dinta kissing dinta yake kokarinyi dasauri surbajo takwace jikinta gamida ballamasa harara tace hoddijan aradu baka isaba yau inma wani asirin akabaka kadunga samin abaki da bakinka to yau takare danni yau KO abinci banajin zanci sabida gudun kar jambakina yagoge shine kai godaigodai dake kawani zo zaka lashe minshi da bakinka ko to Wlh a hir dinka takarasa maganar tana murgudamasa dan bakin dayasha makeup Dariya abun yaba alameen yadda tayi maganar gunta yanufa da niyar kamata nanfa surbajo tasa gudu shima yana binta sunata zagaya dakin wedding gown dinta taja yakamata sabida Jan kasar datakeyi rungumota yayi jikinsa yana kokarin yimata Kiss wayarsa tashiga ruri dasauri yaciro wayar a aljihunsa mommy ce ke kira dasauri yadaga tunkafin yayi mgn mommy tafara fada Aminu baka da hankaline kuntara jamaa a guri amma har yanzu baku isoba banason shashancin banza fa Hakuri yashiga bata sannan yakashe wayar danshi ganin surbajo dayayine yasa yamanta akwai dinner da zasuje Be tsaya bata lokaciba ya dauketa cak bayan yadauko mata fos dinta kai tsaye motar yanufa da ita tun kamin yakaraso wani soja yabude masa murfin bayan zaunar da ita yayi sannan shima yazagaya yashiga direba yaja suka dau hanya yayinda sauran motocin excode dinshi suka sa motar a tsakiya ana jiniya Dayake ba nisa tsakanin gidan da hotel din so basu wani dauki lokaciba suka iso Isowarsu keda wuya abokan ango da kawayen Amarya suka fito daga hall din danyima ango da Amarya rakiya zuwa ciki Fitowa yayi sannan yakamo hannun surbajo itama tafito nanfa masu hoto da video camera suka shiga aykinsu Kawayen Amarya da abokan ango ne suka sasu atsakiya Sun fara tafiya surbajo se kokarin faduwa takeyi sabida takalmin kafarta me uban tudune ganin hakan da alameen yayi ne yasa be Bata lokaciba yadauketa kamar jaririya itakuma tasakalo hannunta ta wuyansa Ihu da tafi kawayen suka sa dan gaskiya koni sunburgeni Daganan suka fara takowa zuwa cikin hall din yayinda MC yashaida shigowarsu Nanfa kallo yadawo kofar dazasu shigo aisha ko wuyanta kamar ze tsinke dan tsawon datake karamasa nason hango ango da Amarya shigowarsu seda numfashinta ya dauke yadawo bakaramin razana tayiba da ganin alameen dauke da amaryarsa suko sauran jamaar dake gurin tafi kawai suke musu masu daukarsu hoto nayi har suka karasa gurin zamansu zaunar da surbajo yafarayi sannan shima yazauna surbajo kara rufe fuskarta tayi da mayafinta sabida tasha kunya daukota da alameen yayi daurewa kawai tayi tabarshi yadaukota dan tasan intace dakanta zata tafi faduwa zatayi nanfa aka shiga gabatar da abinda yakaisu gurin inda MC yabukaci da ango yabude fuskar amarya batare da Bata lokaciba yabude fuskar surbajo innalillahi wainna ilaihirrajuun itace kalmar da aisha ke furtawa dan ta gigice da ganin kyau irinna surbajo hawayene suka fara biyo fuskarta na bakin ciki dasauri Zuly tasharemata gudun kar wasu sugani rarrashinta suka shigayi amma kosu Sun jinjina dakyau irinna surbajo hankalinta besake tashiba seda taji ana Kiran ango da Amarya sufito su yanka cake duk abinda ake fadi da turanci akeyi kuma surbajo batajin turancin alameen ne yamike sannan yakamo hannu surbajo yamikar da ita suka nufi gurin cake din dakyar surbajo take tafiya sabida gudun karta sha kasa duk da de rabin jikinta na jikin alameen
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34