Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 1

Chapter 1

Budurwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ο»ΏπŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *SURBAJO* πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ Zahra Muhammad mahmud Bismillahi rahmanir raheem Allah yanufa nagama Allah gatan bawa Lfy Seku sake sabon zama domin ga sabon darasi nakawomuku Innayi kuskure pls kutunasar dani *page 1* Sauri yake ya isa gida sabida yaga bakwai na safiya tayi. Tunda yaje sallar asuba bedawoba yana masallaci seyanzu Addua yake Yi azuciyarshi Allah de yasa Aisha taga dama ta tashi daga baccinnata na qaddara Tundaga shigarshi falo yafahimci adduarshi bata amsuba duba da ganin falon dayayi ahargitse kamar filin dambe duk da de dama sabon falonne zama acikin wannan yanayin Jikinshi asanyaye yahaura sama inda dakinta yake Ilai kuwa Tana kwance akan gado tana sharar bacci Binta yayi da kallo zuciyarshi nakuna sabida tun jiya yashaida mata zekoma bakin ayki yau jirgin karfe takwas zehau zuwa phortercot amma shine ko tashi a bacci batayi ba Inda sabo yasaba da halinta Juyawa yayi yakoma dakinshi domin yayi wanka sabida yasan ko toilet dinta yace zeshiga yayi wanka seyakusa amai sabida karni da zarnin da toilet din yakeyi Cikin Rabin awa har yagama shiryawa cikin kakinshi na soja yayi kyau sosai sabida dama kyakkyawanne Jakarshi yadauko sannan yadauko key din motarshi dakinta yanufa haryanzu Tana bacci Tashinta yayi Koda tabude ido taganshi tsaki tayi sannan tace Amman wallahi al-ameen kaidan rainin wayone yanzu fisabilillahi ina bacci zakazo katasheni Beyi mamakiba Dan yasaba dajin abinda yafi haka daga gareta Nizan wuce yabata amsa Kudi yaajiyemata kimanin dubu Dari uku a kan bedside drower kallon kudin tayi awulakance sannan tace namenene wannan Nacefanene kiyi amfani dashi kafin nadawo sabida inna tafi wata uku zanyi kafin nadawo kan ubance inji Aisha tafadi tana sakkowa daga kan gadon sannan tace wallahi kayi kadan zakayi wata ukunne zaka mikomin 300k wallahi baze yiwuba tafada yayinda ta zubar da miyaun daya taru abakinta ajikin bangon dakin Al-ameen bameson hayaniya bane Dan haka yace se nawa kike so 500k tabashi amsa bemusaba yadauko yakara mata sannan yace senadawo pls kiyimin addua Agayas tabashi amsa gamida komawa takwanta Fita yayi wani kurtun sojane yazo dasauri yaamshi kayansa yasa aboot sannan yabudemasa bayan motor yashiga sannan Shima yazaga mazaunin direba yatada motor sukafita yayinda motoci biyu na sojoji sukasa motor atsakiya suka nufi Airport suna zuwa kai tsaye jirgi yashiga Dantuni aka gama shirya komai jirginsu yadaga zuwa rivers state Safe trip alameen Love you all Maman Yusuf πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ *SURBAJO* πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€ Zahra Muhammad mahmud *page 2* Tunda alameen yafita taci gaba da baccinta bata tashiba se Tara sannan tamike tashiga 🚽 tayo alwala tayi sallar asuba 😳 Tana idarwa kitchen tanufa madara ta kwaba akofi da Milo tazuba ruwan sanyi tajuya yayi kauri kamar chocolate Tadauko gorar faro tadawo falo tafarasha Aduniya babu abinda Aisha ta tsana irin girki Sam batason yinshi shiyasama bata iyaba Zamanta keda wuya taji ana ringing bell dasauri taje bakin kofar taleka Dan ganin waye Ihu tasa tun kafin ta bude kofar Tana budewa suka rungume juna ita da bakinnata kawayentane su biyu Kai tsaye dakin Al ameen tamusu masauki dan batason su rainata insukaje nata dakin Afalonshi suka zauna hira suka shigayi dawadda tadace dawadda bata daceba suyi gulmar wannan suyi ta waccan Can kuma tafara basu labarin yadda suke kwanciyar aure da mijinta kamar yadda suka saba (waiyyazu billah) Shewa suke kawai suna kara zugata suna fadin eshat baby baki da wasa Dariya tayi tabasu labarin yadda suka rabu yau da alameen Daya daga cikin kawayennatane mesuna Ruky tace wo mutuniyar kina wuta muna binki da petur ina namu salary din tunda kin tatsa muma seki sammana koya kikace zuly baby A wannan gaskiyane wacce aka Kira da zuly tabada amsa eshat ce tafara mgn haba sisters harse kun roka ay kunwuce hakan agurina danhaka ku kwantar da hankalinku nifa wlh kunfiyeminshi so dubu agurina Danni Al ameen dashi da banza duka daya Suke. Kuma sabida nasan zanbaku naku kasonne yasa nace seyakaramin kudin Dankaka zanbaku 200k kuraba Ihu sukayi suka rungumeta suka hada baki gurin fadin heyyy se madam Allah de yabiya Hajiya. *ASALIN LABARIN* al-ameen jibrin sulaiman shine cikakken sunanshi matashine Dan shekaru 35 da haihuwa. dane ga rt major general jibril sulaiman Mahaifinshi Dan asalin garin kanone awata anguwa daake Kira lungun gabari canne asalin tushensu amma sanadin aykin soja yasa yadawo kaduna da zama a malali yake da zama alayin sultan road Hamshakin mekudine ajihar kaduna domin ajerin masu kudi nagarin in akace daya to tabbas shine nabiyu Matarshi daya mesuna Hajiya binta suna kiranta da umma yaransu hudu. Kabeer shine nafari sannan alameen se munawwara da autarsu amal gidan alhaji jibrin gidane gidan tarbiyya Dan yaransu gaba daya babu mehalin banza Mahaifiyarsu nabasu tarbiyya Dede gwargwado kudi besa tayi watsi da tarbiyyar yarantaba tunbayan da mahaifinsu yayi rt yakoma fannin business nakasa da kasa yanada kamfanoni a fadin jahohin nigeria mutumne shi metsoron Allah bashida buri dawuce a yaransa yasamu megadonsa a gidan soja kullum adduarshi kenan inda Allah yataimakeshi ya bashi alameen tunda alameen yafara mallakar hankalin kanshi yaji yana shaawar zuwa aykin soja Koda yatuntubi mahaifinsa da batun bakaramin farinciki yayiba baayi satiba yasamomishi aykin dayake akwai hanya shiko kabeer accounting yakaranta yanzu haka yana ayki a cbn yanada mata daya Da yaronshi guda daya mesuna Waleed kasancewar sunan abbansu yaci munauwara kuwa yanzu Tana js3 yayinda auta amal ke primary 4 tunda alameen yafara aykin soja gabadaya hankalinshi yamaidashi abangaren aykinshi kullum burinshi yataimaki kasarsa lokacin a kaduna yafara aykin kamin ayi posting dinshi zuwa Abuja kamar kullum yauma yataso daga ayki da misalin karfe shadaya nadare a nda yake aykin dan haka ta Badarawa yabiyo dan zefi mishi saukin isa gida yawuto bustop kadan Dede galadima road jikin katangar gidan Baba boss yaganta tsugune Tana kuka ga gurin yayi shuru babu mutane har yawuce seyaji yanason sanin meyasa ta kuka kuma take zaune abakin titi ribas yayi yadawo gurinta layin galadima road din yashiiga Dede gidan kallon kwallo yayi parking sannan yafito yatako da kafarsa zuwa inda take sallama yamata agigice tadago kanta tana kallonshi kara matsawa kusada ita yayi yace yanmata meyafaru ne kika zauna anan kina kuka ganin uniform din soja ajikinshi ne yasa tace aranta bari infada masa maybe yataimakamin cikin kuka tace wlh mamanace tawuni yau Tana wankau har zuwa dare sannan tasamu kudin dazamuci abinci dashi tunsafen bamuci abinciba shine yanzu ta aykoni insiyo garin rogon dazamu sha bansan yaakayiba kudin suka fadi shine nake kuka dannasan yau seta kasheni tafadi Tana sake rushewa da kuka yaisa haka alameen yafadi yana kallonta balaifi tanada kyau dede gwargwado kuma yarinyace dabazata wuce 18years ba yasunanki yatambayeta sunana AISHA tabashi amsa inane gidannaku nunamasa gidan tayi da hannunta danba nisa taso muje yace da ita zaromishi ido tayi tace wlh najemata ba sakonnan yankani zatayi Dan Allah kawuce ka kyaleni anan bazata yankakiba nizan biyata kudin Amman Anshi Wannan Kijewancan shagon kisiyomuku kayan tea 2k yabata godiya tashiga yimasa kamar zatayi sujada dagudu ta tsallaka titin tasiyo kayan tean dawowa tayi tace nasiyo gaba tayi yana binta abaya harsuka isa kofar gidan yace shiga kiyimin Sallama da mamannaki wucewa tayi tana murmushi Dan ita yau jitake kamar sallah saboda zasu sha tea Wanda rabonta datashashi tun kafin babanta yarasu yanzu ko kimanin shekararsa hudu da rasuwa 😜 mamanta Data

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});