Chapter 2
Chapter 2
fito taga sojane ke sallama da ita cikintane ya murda dakyar suka gaisa sannan yamata bayanin abinda Aisha tafadamasa yakara dabata hakuri sannan yadauko kudi a aljihunsa kimanin50k yabata yace tayi hkr duk sanda yasamu lokaci zedunga lekosu godiya Mama takeyi harda hawaye sallama yamata yakarasa gurin motarshi yashiga yanufi gida *wacece Aisha* love you all Maman Yusuf πππππππππ *SURBAJO* πππππππππ Zahra Muhammad mahmud *Page 3* Aisha Bello Musa shine asalin sunanta haifaffiyar garin kadunace acikin anguwar Badarawa Sunan mahaifinta malam Bello mahaifiyarta kuma sunanta maimuna suna kiranta da inna Su ukune agurin iyayensu Aisha itace tafarko se kannanta guda biyu zaituna da Umar Shekarar Aisha 18 mahaifinsu yarasu tun Tana js1 Mahaifiyar itace taci gaba da kulawa dasu har zuwa yanzu da Aisha ke ss2 awata makarantar gwamnati dake anguwarsu Kannanta ma duk government schools sukeyi Rayuwace suke mecike da kunci Dan abunda zasuci yafi karfinsu se inna tayi wankau suke samu suci abinci so daya arana Aisha yarinyace me dogon buri arayuwarta kuma bata da godiyar Allah ko kadan Tahadu dasu Ruky da zuly ne amakarantarsu inda halinsu yazo daya suka kulla kawance Basuda ayki dayawuce suyi gulmar kawayensu har gida ansha biyo Aisha akan tayi gulmar wata akureta Mahaifiyarta macece me sakaci da tarbiyar yaranta tun bayan mutuwar mijinta Wanda hakan yasamu asaline asanadin zafin talaucin dasuke fama dashi kwasam segashi Allah yaturomusu alameen Tunda alameen yatafi besake zuwa gidanba hasalima baya biyowa ta unguwarsu Aisha tafi inna Damuwa darashin zuwannashi sabida tunda tadora ido akanshi taji takamu dasonshi Har bakin titin anguwarsu take zuwa tatsaya kozata ganshi babban abinda yasa takesonshi mijine na nunawa kawa itako bata da buri dayawuce ace taburge kawayenta Yau jummaa dawuri alameen yataso daga ayki ta Badarawa yabiyo har yawuce layin Su Aisha se yatuno da ita danshi harga Allah yamanta dasu tun bayan barinshi gidansu kwana yayi yashiga layin Dede kofar gidan yatsaya Aisha ce atsaye azauren gidan Kai ba dankwali takira me agwaliba Tana siya tun agurin tafarasha fadi take Kai malam wannan da tsami Mamakine yacika alameen ganinta dayayi ahaka gashi tasa wata π Data bayyana halittar kirjinta Dan har ta saman rigar ana ganinsu Hon yamata dasauri takai dubanta inda taji hon din dagudu takarasa fitowa tanufeshi dasauri alameen yadauke idonshi daga kallonta sabida yadda take gudun yasa halittar kirjinta yin wani juyi na musamnam sabida Allah yawadata ta dasu Karasowa tayi jikin motor Tana dariya Sannu dazuwa soja sunan data kirashi dashi kenan daurewa yayi yayi murmushi yace yauwa kanwata Kashigo mana daga ciki tabashi amsa Fitowa yayi suka shiga zauren gidan gaisheshi tayi Yaamsa sannan yace lalle bakyason shiri Dani tunda bakya muamala da dankwali kunyace takamata dagudu tajuya Tashiga gida tasako hijab sannan tafadawa inna sojan rannan yazo murnace takama inna dasauri tace uwaki Aisha shine kika barshi awaje yisauri kije ki kirashi yashigo dasauri tadawo gurinshi tamishi iso zuwa cikin gidan Kan tabarmar da inna tashimfidamasa yazauna gaisheta yayi cike da girmamawa sannan yasanar dasu sunanshi dana mahaifinshi Inna da Aisha ne suka hada baki gurin cewa Alhaji jibrin sulaiman de Wanda mukasani mamaki tambayar tabashi sabida arude suka masa ita eh shi yabasu amsa Ajiyar zuciya sukayi dukansu daganan inna tabashi tarihinsu yatausayamusu sosai inda daga karshe yayi musu alkawarin kulawa dasu tundaga wannan lokaci alameen yamaida gidan inna kamar gidansu inyazo sallama kawai yake yashiga sosai yake musu hidima dantuni yasauyawa su Aisha makaranta ita da kannenta Yayinda ita kuma Aisha kullum sonshi Karuwa yake azuciyarta zuwa yanzu har waya yasemata iPhone6+ burin aisha yafara cika dantuni tasauya tayi kyau namusammam ga sutura Tana shiga ta alfarma bata da wata damuwa data wuce ta auri alameen insuna waya so tari tasha yunkurin sanardashi halin datake ciki seta kasa yau alameen ne yakawomusu ziyara bayan sungaisa da Inna ta tashi tafice dama zata barkane Aisha dawowa tayi kusa dashi tazauna tace Yaya alameen kamar yadda take kiranshi juyowa yayi Yana kallonta ganin yadda tanatsune yasa yagane mgnr dazatayi me muhimmaci ce sabida kwatakwata Aisha bata da natsuwa yaakayine kanwata yatambaya kunyace tarufeta amna bata dazabi dayawuce tasanar dashi yaya Don Allah zaka iya aurena? Jin tambayar yayi kamar saukar aradu danshi Sam bayason Aisha amatsayin wacce ze Aura danyafison mace me natsuwa AA yabata amsa kuka tasamishi tana Don Allah kataimaka kaaureni wlh tunda nafara ganinka naji inasonka katausayamin sonka zeiya kasheni wlh tafadi Tana ruko kafarshi dasauri yamike yace amma Aisha bakida hankaliko taya zan iya auranki Bari kiji infadamiki bakya cikin jerin macen danakeson in Aura Danhaka bazan boyemikiba wlh banasonki kiyi hkr kinemi wani yana gama fadin hakan yajuya yafice daga gidan ranshi abace innace tashigo taga Aisha kwance akasa dasauri takarasa kusa da ita ga mamakinta farin kumfa tagani yana fitowa daga bakinta agigice tadagota ina babu numfashi ajiyeta tayi tafita tsakar layin Tana neman taimako napep akasamo akasa Aishan aciki inna Tashiga suka nufi asibiti πππππππππ *SURBAJO* πππππππππ zahra Muhammad mahmud *page 4* Koda isarsu asibitin likitocine suka rufu akanta seda suka share awanni biyu sanna suka fito Inna dasauri ta sha gaban daya fara cikinsu Likita ya jikinnata Dasauki yabata amsa Sannan yace kibiyoni office yajuya yanufi office dinshi inna nabinshi abaya Bayan sunzaunane likitan yace mama meyasami yarinyarki hartake yunkurin kashe kanta tahanyar shan fiyafiya Hankalin inna ne yatashi dajin abinda likita yace Dakyar tabashi amsa da wlh bansaniba nide nasan bata dawata damuwa danko yauma lfy nafita nabarta dawowa nayi naganta a yadda nakawomuku ita Murmushi doctor din yayi sannan yace kituntubeta tabbas akwai abinda yake damunta zaki iya zuwa kiganta dan tajima dafarkOwa godiya Inna tayiwa doctor din sannan tanufi dakin da Aishan take Tana shiga suka hada ido daita dasauri takarasa bakin gadon tarukota Kuka Aisha keyi tanacewa Inna nashiga uku alameen yace baya sona wlh inna Δ―nasonshi zan iya rasa raina akansa kitaimakeni Inna Dankari itace kalmar data fito abakin Inna ajiyar zuciya tayi sannan tace Aisha inbanda rigima irin taki inake ina Aminu yafi karfinki nesa bakusaba shine Dan shirme harda yunkurin kashe kanki sabida shi to wlh inbacci kike kifarka Aminu baze sokiba sabida ke ba tsarar auransabace Kuka tasawa Inna kamar zata mutu hankalin Inna tash yayi rarrashinta tashigayi dakyar tayi shuru bacci yayi awon gaba da ita Yau Monday Alameen ne yataso daga ayki gidansu Aisha yanufa sabida tunda yajita shuru kwana biyu bata dameshi dawayaba yasan tahakura dason datake mishi Shiga gidan yayi kamar kullum kannen Aishan ne kawai agidan suma daalamun fita zasuyi ganinshi yasa suka nufeshi gaisheshi sukayi sannan yatambayesu inasu innanfa Suna asibiti suka bashi amsa meyafaru sukaje asibiti waye ba Lafiya Aunty Aishane tasha fiyafiya tun shekaranjiya shine aka kwantardasu innalillahi wainna ilahirrajiun itace kalmar da alameen yake nanatawa aranshi ko shakka babu yasan shine silar shan fiyafiyanta Arude yatambayesu wanne asibitine amsa suka bashi dacewa suma can zasu Kai abinci juyawa yayi yace to kutaho mutafi Sun isa asibitin lokacin Aishan na bacci Inna seda tayi mamakin ganinshi Gaisheta yayi gami da tambayar me jiki amsawa tayi cikin sakin fuska inda takara dabashi hkr abisa katobarar da Aishan tayimasa Kunyace takamashi matuka inda yagaza cewa komai Muryar Aishan ce takatsesu dacewa yaya kazo dubanine dasauri yanufi gurinta yayinda Inna taja kannen aishan suka fice daga dakin Gefen Gadon yazauna yakamo hannunta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34