Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Budurwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,259 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yayi ta baya dasauri Surbajo tajuyo dan ganin waye yarungumeta, ganin Al-ameen ne yasa tasaki ajiyar zuciya. Juyowa tayi Itama tarungumeshi tana fad'in, "i know my dear bazaka iya fushi daniba don Allah kayafemin Inna b'atamakane bazan sakeba", D'ora hannunshi yayi akan bakinta alamar tayi shuru sannan yak'ara sassauta muryarshi yace, "Baki b'atamin ba baby kawai nayi fushine sabida ina ganin kamar baki damu dani bane Shiyasa amman yanzu komai yawuce kiyi hk'r kinji my lollipop,"yafad'i yana kaimata kiss abaki,janyewa tayi ajikinshi sannan tace, "To yazancan dawo da Aisha d'akinta da nayi maka d'azu,?kaamince ko har yanzu baka yardaba,?" Kunnenta yaja da hannunsa yana murmushi yace, "Ya na iya da gimbiyata tunda kince ta dawo naamince amman ba yanzuba gaskiya". "Se yaushe",Surbajo ta tambaya. "Se nasa ajiya anan"yashafo cikinta yana dariya,ture hannunshi tayi zatayi magana yadakatar da ita dacewa, "Wlh this is my final decision Inkuma baki aminceba to nafasa dawo da itan",dasauri Surbajo tabashi amsa da cewa, "Aradu na amince Kado,"dariya gaba daya suka sa sabida tuno da irin maganarta tada da takeyi. Rayuwa suka cigaba dayi cike da so da k'aunar juna, kullum Surbajo na k'ara rok'onshi yadawo da Aisha shiko dagewa yayi akan se Surbajo tayi ciki sannan ze dawo da Aisha,hakanne yasa Surbajo tafara tsayuwar dare tana rok'on Allah yabata ciki dan Aisha tadawo d'akinta. Bangaren Aisha kuwa ciwon zuciyar tane yatashi kuma tashi me tsanani, dan Inna har ta cire ranta akan Aisha dan kowa yaganta ze d'auka inyafita kamin yadawo ze tarar ta mutu,batasan waye akantaba ko numfashi ta oxygen take shak'arsa abun gwanin ban tausayi,Inna da sauran k'annanta sede susata agaba suna kuka,likitocin dake dubata sunayin iya bakin k'ok'arinsu dansuma suna tausaya mata. Ajidad'i yau tashirya kiran Al-ameen dan haka bata batayi tunanin komai ba takirashi,seda takira yafi so biyar ba'a d'aukaba can taji yad'aga ,tace, "Haba namijin duniya ba fad'a me yakawo gaba kuma,"tunda ta fara magana yaganeta ranshi ne yay masifar baci da kiran data mishi sabida ta tuno mishi abinda yafaru tsakaninsu katseta yayi da cewa, "Banyi mamakin kiran da kikamin ba sabida nasan wacece ke,kuma dama duk inda karya take ba'a rabata da bin maza, nayi danasanin had'uwa dake Jameela,ke shaid'aniyace me kai jama'a wuta, daga yau se yau inkika k'ara kirana sena miki abinda baki zataba stupid kawai, be jira amsartaba yakashe wayar yana huci kamar tana gabanshi. Itako Ajidad'i bata d'auki zancan nashi serious ba kullum seta kirashi baya dauka kuma bata denaba,dataje gurin bokanta yamishi asiri hkr yabata yace baze iya ba sabida Al-ameen akwai tsari ajikinshi. Duk da haka bata hkr ba sabida tasha alwashin Seta lashi zumarsa,ci gaba tayi da kiranshi shi kuma yak'i yasata a blacklist ne acewarsa ita bata isa tasashi yin hakanba tai ta kiranshi harta mutu. Allah maji rok'on bawa. Yau Surbajo da zazzab'i ta tashi ga kasala,danko Yusuf takasa yimasa wanka Abbanshine yashiryashi driver yatafi kaishi makaranta,sannan yadawo kanta, Wanka yamata Itama yashiryata sannan yabata abinci taci tana gama ci ama'i yataso mata da gudu tayi cikin bayi tafara kwara aman,binta yayi bayin yataimaka mata ta gyara jikinta sannan ya wanke inda ta b'ata suka fito, be jira komai ba yad'auketa suka nufi Asibiti,awon farko likita yatabbatar musu da tana da ciki har na wata biyu, ga mamakin Al-ameen Surbajo tafishi murnar samun Cikin har sujudul shukur tayi, murna sukayi bata wasa ba babu kamarma Surbajo sabida burinta ze cika nason Al-ameen yadawo da Aisha. Suna isa gida tasamishi daru akan wlh seyaje Kaduna aranar yadawo da Aisha in ba hakaba wlh seta cire cikin,hankalin Al-ameen inyayi dubu yatashi rasa yazeyi da ita yayi dan yasan ta sarai bata fad'in abinda tasan bazata aykataba, bashida zab'in daya wuce yabi umarninta,shiryawa yayi driver d'inshi da excode d'inshi ne suka masa rakiya yatafi Kaduna.wanda hakan ba k/aramin dad/i yayiwa Surbajo ba. Se sha daya na rana suka isa Kaduna. Gidan iyayensa yafara zuwa yasanar dasu abinda yakawo shi sunyi murna sosai dajin zancan fatan alkhairi sukayi masa gamida yimasa nasiha akan yayi adalci atsakanin Matanshi godiya yamusu, mommy tafara tsokanarshi dacewa, "Allah ya soka bata gama iddah ba data gama sede kashiga layin zawarawanta,"dariya yayi sannan yamusu sallama ya nufi gidansu Aisha. Yana zuwa yasamu labarin abinda yasameta, hankalinshine yatashi dan bayason ganin wani na wahala sabida shi, Asibitin yanufa sanda yaga Aisha jiri ne yad'ebeshi ze fad'i da sauri excode d'inshi suka tareshi. Kuka Al-ameen yake sosai tausayi da soyayyar Aisha ne suka shiga zuciyarshi akaron farko fad'i yake, "Aisha kiyafeni bansan halin dakike cikiba namaida igiyar auranmu guda biyu dasuka rage don Allah kitashi wlh ina k'aunarki inkika mutu bazan yafewa kainaba please,"ko motsi Aisha batayi batama san yanayiba abinda ya sake karya zuciyarshi kenan yadunga kuka kamar yaron daya rasa uwarsa. Likitane yamasa bayani gameda cutar Aisha kuma yabashi shawara akan Inde da hali to afitar da Aisha kasar rasha domin duba lafiyarta.,Al-ameen yagamsu da shawarar likitan dan haka tun agurin yakira wayar masu yimasa visa inze fita yace yanason visa zuwa rasha nanda Kwana biyu ko nawane ze biya na mutum biyar yakeso yau komai dare ze kawo hotunan sauran dan ayi musu passport sabida basu dashi . Aranan akasa Aisha a motar Asibitin zuwa international hospital dake Abuja tare da rakiyar mamanta da Al-ameen da tawagarsa inda k'annan Aishan aka kaisu gidan su Al-ameen,iyayensa sun tausayawa halin da Aisha take addu'ar samun sauk'i suka mata Karfe goma na dare suka isa Abuja,adaren yakai hotunan Surbajo,Yusuf,Inna,Aisha,sabida shi yana dashi visa kawai za'a masa,harda passport,se sha biyu yashigo gida,Surbajo tafirgita da ganinshi nande yakwashe komai yasanar da ita, kwana tayi tana kuka da sassafe tasa Al-ameen yakaita Asibitin ananne tai kuka bana wasaba dakyar aka rarrasheta. Ranar da ita aka kwana a asibitin fafur tak'i komawa gida. Da sassafe jirginsu yad'aga zuwa rasha, to Aisha Allah yatashi kafad'a . Maman Yusuf ๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€ *SURBAJO* ๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€๐Ÿ€ Zahra Muhammad mahmud *ยฎPure moment of life writers* *P.m.l* *page 77-78* *Rasha* Sun isa lfy tun a Airport suka tarar da motar ambulance najiransu da kuma wata personal car,suna sakkowa akasa Aisha a Ambulance d'in zuwa Asibiti su kuma suka shiga d'ayar motar suka bisu abaya. Likitocin dasuka duba Aisha ba k'aramin fada suka rufesu dashi ba akan barinta da ciwo da sukayi yaci k'arfinta. Sude ba baka se kunne, angama yimata duk abinda yadace sannan aka sallami su Al-ameen,sabida ba'a jinya a Asibitin sede kazo kaduba Mara lafiya kawuce. Hotel yakaisu me kyau sosai,d'aki biyu ya kama d'aya na Inna d'aya nasu.tunda suka shiga d'aki wanka kawai sukayi suka ci abinci, suka rama salloli kowa yabi lafiyar gado sabida sun gaji sosai. Tunda sukaje Rasha jikin Aisha yafara sauk'i, kullum Al-ameen natare da ita yana bata kulawa sosai,Surbajo Ma ba'a barta a bayaba tana yi dede gwargwado gashi duk dare seta tashi tayi sallolin nafila akan Allah yaba Aisha lfy,cikinta bashi da laulayi shiyasa take samun damar yin komai,Inna ko har cewa take ita bata ga amfanin zuwa da itaba sabida komai da yadace tayi Surbajo ce keyi se albarka take sa mata. Abinda Surbajo takeyi game da Aishan bak'aramin farantawa Al-ameen rai yakeyiba sonta da k'aunarta kullum k'aruwa yake azuciyarshi ya yarda Surbajo me k'aunarsa ce ba kad'an ba shiyasa yabata wani matsayi a zuciyarsa wanda be ba kowaba se ita. Satinsu

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});