Chapter 32
Chapter 32
TO ALHAJI ALIKO DANGOTE FAMILY ALLAH YAY MUKU JAGORA AKOINA KUKE A FAD'IN DUNIYA NAGODE* *pure moment of life writers* *p.m.l* *page 89-90* Duk abinda yadace su tanadarwa bak'uwar tasu shi suka tanada.suka dawo falo suna jiran isowarta. Aji dad'i tunda ta iso k'ofar gidan yawunta ya k'afe sabida kyan da gidan yay mata,take zuciyarta ta ayyanamata dama ta auri mamallakin gidan.koda tazo gurin sojojin dake gadin gidan basu hana ta shigaba sabida madam tace zasuyi Bak'uwa in tazo su barta ta shiga. Shigewa tayi cikin gidan tana wani karayraya ita adole tazo kwartanci, cikin falon gidan tashiga inda megadine yanuna Mata hanyar, Su Aisha ko jin motsine yasa suka tashi da gudu suka b'oye a cikin labulen bakin k'ofar shigowa har ta shigo bata Lura dasub, kan kujera taje tazauna tadora k'afa d'aya kan d'aya aka k'ara baza gashin atachimen d'in datasa tana taunar cingom ji tayi kamar alamar akwai mutum atsaye akanta da sauri ta juyo zabura tayi tamik'e,ganin Aisha da Surbojo kowa d'auke da muciya sun nufota neman hanyar gudu take amman ina sun cimmata ayko nan suka shiga kirb'a mata muciya ta ko ina,ihu take tana neman taimako Amman ina babu me cetonta,dukanta suke bada wasaba, daganan suka kwantar da ita ta k'arfi suka yimata matsi da garin barkono wani azababben ihu tashigayi bana wasaba ga jikinta duk inda suka fasa seda suka cikeshi da garin yaji Aji dad'i ihu take har numfashinta na d'aukewa. Dede lokacin Al-ameen yashigo gidanshi ganin masu gadi yayi tsaye cirko cirko abakin k'ofar falon gidan tambayarsu yashiga Yi akan abinda ke faruwa, nan suka shaida mishi bak'uwa ce tashigo gidan yanzu shine kuma suka jiyo kukanta ga kuma sautin dukanan sunyi sunyi su bud'e k'ofar sunkasa,da sauri Al-ameen yafara dukan k'ofar yana kiran sunansu amman ina ba wacce ta kulashi cigaba sukayi da operation d'insu, ganin bazasu bud'ebane yasa yabi ta kofar part d'inshi wacce d'azu daze fita tanan ya fita kuma besa key ba, dagudu yabi hanyar yak'araso falon ganin abinda sukeyi bak'aramin mamaki yabashi ba tunaninshi me yakawota gidanshi?,tayama tasan yadawo kaduna?, ganin baze samu amsoshinbane Yasa yaruga dagudu yayi kansu dakyar yakwaceta a hannunsu se zunduma ihu take iya k'arfinta tana tsalle tsalle sabida yajin da suka yimata matsi dashi,Surbajo ce tace afusace, "Dan kan ubanki kad'an muka yimiki dan wlh yau so mukayi muyi miki abinda ko sunan namiji kikaji an ambata sekin firgita bare har kice zaki yi mu'amala dashi shegiya tsinanniya me lalata mazan mutane,"Aisha ta amshe da cewa, "Bar matsiyaciya de muna nan muna tattalin mijinmu ke kinaso ki b'ata mana ginin damuka dad'e munayi wlh kinsha k'arya kuma koda wasa kika sake bin mijinmu wlh semun sauya miki halitta tsinanniya kawai," Al-ameen ne ya katsesu dacewa, "Haba ku kuwa yanzu abinda kukayi kunyi adalci kenan?yazaayi kukama y'ar mutane kuyi mata irin wannan izayar wannan ay zalincine ina laifin kuyi mata warning da baki amma shine harda irin wannan azabtarwa,"Aisha ce takatseshi dacewa, "wato abinda mukayi munyi laifi ko ?sabida munmata hukuncin daya dace da ita shine har Kake cewa bamu kyauta ba to wlh semun mata wanda yafi wannan muddin takuma kallon mijinmu,"Surbajo tace, "ke kika tsaya ma yimasa bayani wlh Aunty kawai kijawo mana ita muci gaba da cin uwarta inyaso seya zab'a ko mu ko ita," tana gama fad'in haka ta finciko Aji dad'i dake b'oye abayanshi suka ci gaba da shirgarta harseda suka karyata a k'afa duk yadda yaso ya amsheta yakasa seda suka gaji dan kansu suka kyaleta, suka wuce d'akin Aisha suna dariya suka barshi tsaye akan Aji dad'i wacce ko numfashi batayi, kiran driver dinshi yayi yabashi kud'i da shot note yace yakaita asibitin sojoji kinkimarta driver yayi yanufi asibitin da ita wanda yake mallakin sojojinne me suna 44 kuma babu nisa tsakaninsu da asibitin. koda aka kaita asibitin seda tayi kwana goma sannan ta ji sauk'i sallamarta akayi yayinda k'afarta dasuka karyata kuma akayimata D'ori aka bata sandar dogarawa,ta koma Abuja cike da danasanin sanin Al-ameen datayi arayuwarta tabbas tunda take bata tab'a danasanin karuwancin datakeyiba se yanzu dan haka had'a yanata yanata tayi takoma gaban iyayenta tanemesu gafara. Shiko Al-ameen gaba ya d'aura da matan nashi inda sukuma suka maidashi mahaukaci, inyashigo gidan suyi masa dariya inze fita su kwashe da dariya sunde maidashi kamar tab'ab'b'e abin yafara damunshi dan har tsarguwa yakeyi in suna dariyar se yad'auka wani abun suka gani ajikinshi suke dariyar har gaban mirror yasha tsayawa yana k'arewa kanshi kallo dan yaga mesuke wa dariyar. Rannande ritsasu yayi afalon suna masa dariyar Surbajo ya damk'o yace, "Yaza'ayi kumaidani mahaukaci kusani agaba kunamin dariya to wlh yau sekun ciremin abinda kukewa dariyar,"yafad'a rai ab'ace, dariyar suka sake tuntsirewa da ita suna nunashi sakin Surbajon yayi yakama dube dube ajikinshi, da gudu suka bar falon kowa ta gudu d'akinta tasa key,murmushin takaici yayi yawuce nasa d'akin yaganosu wato gasashi sukeyi dan yanuna b'acin ranshi akan abinda suka yiwa Aji dad'i.A ranshi yace, "to fita harkarku zanyi ko kunamin dariyar". Yau kuma su Ruky ne suka dira agidan bayan bak'ar wahalar dasukasha kamin su gane kwatancen da'aka musu,dakyar megadi yabarsu suka shiga,, afalo suka sami Aishan a zaune tana wasa da Hanif da Yusuf, da sallamarsu suka shiga falon mamakinsu ne k'arara a idon Aisha kallon tsana da k'iyayya take binsu dashi har suka zauna. Suna zama carab Zuly tace cabd'i Jan kice kece kika koma nani d'in yaransu ken...... bata gama fad'in abinda tai niyya ba Aisha ta kifeta da Wani lafiyayyan mari tasake k'ara mata wani, mamakine yahanasu yin wani yunk'uri, d'aga murya Aisha tayi tace, "Sister ki fito munada bak'i Wanda yadace ayimusu sanitation a brain d'insu,"da sauri Surbajo tafito daga kitchen hannunta d'auke da muciya guda biyu dan tun ranar dasuka daki Aji dad'i suka yi meeting akan duk sanda d'aya yaji d'aya yakirashi akan suzo suyi sanitation to abun dukane yasamu dan haka Surbajo harda d'amararta tana zuwa falon tamik'awa Aisha muciya guda d'aya ayko batare da b'ata lokaciba suka rufesu da duka ta ko ina k'arar hayaniyarsuce ta tashi Al-ameen a bacci da gudu yafito falon ganin yak'in da akeyi afalon ba k'aramin mamaki yabashiba,dakyar yak'arasa gurin ya rabasu da kyar su Ruky se kuka sukeyi sabida dukan dasuka sha,Aisha tace, "matsiyata marasa kunya wato har kuna da idon dazaku sake kallona da Sunan k'awance to daga yanzu bani baku kunyimin illar da har na mutu bazan manta dakuba kuma wlh bazan yafe mukuba kufice daga gidannan yanzu wlh,"jiki asanyaye suka fice a gidan ran Zuly yafi na Ruky b'aci sabida bata samu damar ida nufintaba. shiko Al-ameen masifa yarufesu dashi dacewa, "Wlh maganar dakuke d'aukomin tafara isata ace gidana yazama filin dambe ay dana sani tun farko anginamin filin wrestling agidan dannaga alamar Roman reigns and Dean Ambrose ne agidan yakamata agina muku filin dambe,"ko kallonshi basuyiba suka wuce d'akinsu ππ *SURBAJO* ππππππππ Zahra Muhammad Mahmud Kuyimin afuwa masoyana wlh raina ne yab'aci Shiyasa na kula.Amman Namuku alkawari bazan sake kulasuba kugafarceniπππ *Dedicated to, faty axland,rufaida umar, sadnaf,seemaluv,ummu yusura,maryam s bello,duka members na pml this page is yours love you all with all my heartπππππ* *pure moment of life writers* *p.m.l* *page 91-95* Al-ameen binsu yayi d'aki dukansu kowacce yay mata fad'a,yaja musu kunne sosai yanuna
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34