Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Budurwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,317 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kuka,dan taji dadin zaman dayayi da ita,rarrashinta yayi yace takwantar da hankalinta baze dadeba ze dawo,dakyar tasakeshi yatafi. Tarba ta musamman yasamu agurin surbajo Dan har airport taje tarboshi,tareda bodyguard dinsa. Suna zuwa gida,taimakamasa tayi, yayi wanka yashirya, suka dawo dinning yaci abinci.kara yimasa Allah yasanya alkhai'ri tayi game da samun cikin Aisha,sannan tace yakiramata ita tamata yajiki.bamusu yaciro wayarshi yakira Aishan bayan sungaisa yace ga surbajo zata gaisheta, da kamar tace a'a sekuma ta tuna yadace taba surbajo amsa,gameda gorin data Mara. Tace to abata sugaisan, kamar abun arziki, surbajo tagaisheta gami da mata fatan Allah yasauketa Lfy, ay kamar jira take,tace, "ameen idan takai zuci, kinki Allah yaso,da kindauka kekadaice me rabon haihuwa?tonima gashi nasamu,kuma Wlh ko kece shugabar matsafa na duniya, sede kiyi kibari wannan cikin yafi karfinki, yargidan masu tallan nono. Dasauri surbajo tamikawa Al-ameen wayarshi,tana danasanin cewa akirata sugaisa. maman yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *this page is dedicated to Aisha Usman,baidau,maman Huzaifa,jidda,baby,mrs smart,nafi Muhd Katsina,eshat Mustapha,fatima Muhd kaduna,raihanat,ummu basma,hajara Abdullahi, Fiddah,maman Mashkur thanks you all,I salute you all*👮 *page 63-64* Yanzu Aisha laulayi yayi sauki,bakamar da ba,iskanci kuma da takama da cikin se abunda yayi gaba,musamman datayi scanning,akace mata namiji zata haifa, karkuso kuga rawar kafa, kawayenta kullum suna gidanta wai sunje jinyarta,abun namata dadi,yadda kawayennata ke bata kulawa, Al-ameen tuni yagama siyayyar kayan baby,haihuwar kawai suke Jira,yanzu duk weekend a kaduna yakeyi sabida cikin Aisha daya tsufa, Surbajo tamaida hankalinta kan karatunta, Sam bata wasa dashi ko kadan,shiyasa al-ameen kekara sonta,dan har cikin ranshi yana takaicin rashin karatun Aisha,Wanda ita ko ko ajikinta. Wata safiyace aisha ta tashi da ciwon nakuda, Allah yataimaka lokacin Al-ameen yazo weekend, Ihu tadunga yimasa kamar zatayi hauka, duk yabi yarude,agigice yayi asibiti da ita,suna zuwa aka shiga da ita dakin labour. waya yaciro yakira mamanta, bajimawa tazo asibitin,shuru har yanzu Aisha bata haihuba,se addu'a sukeyi,zuwacan likitan ta fito dasauri,gurinta suka nufa suna tambayarta ya Aishan take,zufa tashare sannan tace musu bleeding takeyi ,dan haka Tana bukatar jini da gaggawa, inba hakaba anything can be happen, Tahaihune? suka tambayeta arude, as tabasu amsa kuyi sauri kukawo Jinin ko kuma ku biya akwai nasiyarwa, bamason nasiyarwa muje adebi nawa am group o±, Donor ne ni, Bamusu suka nufi lab dashi, bayan sun aunashi suka tabbatar bawata matsala, sannan suka dibi jinin,akaje akasawa Aisha, Allah gamu gareka,aishafa nacikin mawuyacin hali, duk me imani yaganta ze tausaya ,likitoci sunyi iya yinsu wajen ganin tahaihu da kanta,amma ina dole se ammata cs. Gurin al-ameen sukazo,wanda yazuba uban tagumi hankalinshi atashe,burinshi Allah yasauketa Lafiya,kiranshi office doctor din tayi,tayimasa bayanin abinda ke faruwa,ba musu yasa hannu a takardar cs din gami da fatan Allah yasa ayi asa'a. Gurin mamanta yazo yamata bayani,kuka tasa, Tana adduar Allah yafito da Aishan Lfy, Sunanan zaune akafito da Aishan fuskarta dauke da oxygen a hanci alamun numfashinta be wadataba,zaa kaita dakin operation,mamanta kuka tasa Tana mata addu'a,duk juriya irinta soja,Al-ameen komawa yayi kamar yaro, kuka yake sosai yana mikawa Allah rokonshi, Ankwashe sama da awa biyu,sannan likitocin suka fito,dasauri,su al-ameen suka nufesu,tamvayarsu Al-ameen yake ya aisha take,daya daga cikin likitocinne yace,she is fine,but am sorry to say,we lost the baby, Godiya ga Allah Al-ameen yayi, daya tsallakar da Aishan siratsi,yayinda agefe daya kuma yanajin dacin mutuwar babyn,gamida tausayawa Aishan duba da ganin yadda ta dora buri akan dan. doctor ne yakatseshi dacewa yanason ganinsu a office akwai magana,dasauri suka bi bayanshi zuwa office din,hakuri yasoma basu sannan yace Aisha tawahala da yawa wanda hakan baason faruwarsa ga me nakuda, kuma hakan yafarune sakamakon shan kwayoyin hana daukar ciki datayi amfani dasu acan baya, sanadin hakanne yajawo mahaifarta tasamu matsala inde bawani ikon Allah ba ze wuya tasake haihuwa arayuwarta, Al-ameen gaba daya rikicewa yayi ,dajin zancan likitan,haka mamantama,hakuri doctor din yadunga basu daga karshe yabasu takardar data tabbatar da bincikennasu, Bayan Sun baro office din doctor, dakin daaka kwantar da Aishan bayan anfito da ita daga operation din suka shiga,tana kwance Tana bacci, har yanzu akwai oxygen din a hancinta,tausayintane yakamasu duka, suna nan zaune aka kawo musu gawar babyn Rufe cikin shawul kamar me rai, Al-ameen ne yaamsheshi yabudeshi,wasu hawayen ne suka zubomasa, ganin babyn ba inda yabaro Yusuf, maana shima dashi yake kama,mamanta yaba itama tagani tamasa addu'a,wayarsa yaciro yadunga daukar babyn hoto,sannan yaamsheshi yatafi gida domin amasa sutura, gidan iyayensa yakai gawar suma suntausayawa Aishan gamida yimata fatan samun sauki, shikuma Allah yajikansa, bayan sun shirya yaron suka masa sallah,makabarta suka nufa domin birneshi,itakuma Momy ita Da amal,da matar kabeer asibitin suka nufa,domin dubo Aishan. Maman Yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *this page is dedicated to Alhaji Auwalu Bauchi. Nagode da irin dawainiyar yada littafina dakakeyi a facebook dasauran guraren daban saniba,Allah ya albarkaci rayuwarka data zuriarka baki daya* *page 65-66* Su mommy sun iso asibitin Lfy, sede suma suna ganin Aisha sunyi matukar tausayamata,har kuka sukayi sabida tausayinta. Surbajo Al-ameen ne yakirata yasanar daita abinda yafaru,Allah sarki baiwar Allah kuka tadunga yi kamar ita abun Yasama, rokonshi tashiga yi akan zatasa driver yakawota tadubata,kin amincewa yayi yace tabari zezo sutaho tare,haka dole tahakura Dan tasanshi kaifi dayane, Kwanan Aisha daya a asibitin tafarka, abinda tahaifa tafara tambaya, duk cikinsu anrasa mebata ansa se al-ameen,shima daurewa yayi yamata bayanin,kuka tasamusu tana fadin "Wlh bazan yardaba wato takashemin shi hankalinta yakwanta,inna yarda Allah yatsinemin dole seta biyani yarona. Hakade taita zage zage dasauri suka Kira likita yasake yimata allurar bacci. Al-ameen ko ranshi yabaci dajin zantukannata,wato ita har yanzu bazatayi hklb kenan. satinta daya aka sallameta,koda tadawo gida kullum zancanta surbajo takashe mata da ita bazata yardaba,kawayenta se Kara zugata sukeyi akan lalle surbajo ce takashemata yaro. Kwanan Aisha goma da haihuwa al-ameen yakawo surbajo ta dubata, Tana ganin surbajo wani ihu tayi tayo kanta,dasauri al-ameen yariketa, kokarin kwacewa take amma takasa sabida jikinta ba kwari masifa ce kawai irinta Aisha, magana yafara dacewa, "aisha yakamata ace yanzu kingirma Don Allah yaushe zaki Dena batamin raine?sama da shekara goma kullum da bacin ranki nake kwana menayimiki haka Aisha kike burin kasheni? why Aisha?dama Ashe bada gaske kike sonaba kin aurenine domin kikasheni da bakinciki? Ina son dakike ikrarin kinayimin? Seyaushene zanfara jin dadin zama dake iye Aisha ninefa Aminu amma nikikewa tozarci irin haka ngd, yana gama fadamata haka yasaketa yabarsu agurin yawuce dakinshi, jikin Aisha gaba daya yagama mutuwa dajin kalaman al-ameen,kuka tarushe dashi agurin tarasa meyadace Tayi, Tunda suke da al-ameen yaune yamata kalaman dasuka dagula mata lissafi Amman batajin zata yafewa surbajo abinda tamata,surbajoce ta katsemata tunani dacewa, "aunty Don Allah kiyi hkr inna batamikine Allah yahuci zuciyarki, Allah kuma yabaki Lfy yajikan babyn yasa masu cetonmune, ko kulata Aisha batayiba bare tayi tunanin zata amsa,surbajo mikewa tayi tafice daga dakin. dakinsa tanufa tasameshi yana zuba kaya a wadrop,tayashi tayi suka gama zuba kayan, Lura datayi ranshi abace yake yasa tashiga kwantar mishi da hankali harseda yasamu natsuwa, daganan aka fada rayuwa medadi. Da daddare daukar surbajo yayi suka tafi gidan iyayensa, Sunyi murna sosai da ganinta, suma tamusu gaisuwar rashin dasukayi, dazasu wucene mommy tace suwuce da Yusuf Dan tasan sunfisu bukatarshi akusa dasu kawaici kawai suke musu, wayyo dadi,surbajo jitayi kamar ta goya mommy, godiya sukamusu sosai daganan suka musu sallama, Dan gobe surbajo zata koma Abuja

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});