Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

Chapter 33

Budurwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,242 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

musu b'acin ranshi,hak'uri sukai ta bashi dakyar ya hak'ura suka koma zamansu kamar da. Yau Surbajo ce da girki dan haka tun safe take ayki sabida sunk'i yarda ad'aukomusu me ayki ba yarda beyi dasuba amman fafur sunk'i yarda, se azahar tasamu tagama kintsa komai,da sauri tashiga wanka tafito ta shirya acikin wasu shegun kaya tayi kyau ba kad'anba,d'akin Al-ameen tanufa sabida yakira ta yace mata yadawo.tana shiga da gudu taje tarungumeshi takaimishi kiss, rungumota shima yayi yana Murmushi yace, "Haba Baby wannan runguma haka ay Seki karyani,koda yake John cena ce ke bakyawa mutum dukan rashin imani",yafad'i yana dariya duka takaimishi sannan tasa kukan ahagwaba tace, ."Wlh bazan yardaba nice John cenar?,kai shikenan kafi son mukyale su suzo su wargaza mana gida, muna zaman lfy su kunno mana bala'i wlh k'aryarsu dole mud'au mataki",tafad'i tana murgud'a masa baki . Dariya abun yabasa Dan haka rungumota yayi suka fad'a gado yana fad'in, "Da kyau tawan Shiyasa nake sonki bakya d'aukar non sense, dan haka nima bari nad'au mataki anan, "romance d'inta ya shigayi kota ina tun tana tureshi harde Itama tabi yarima akasha kid'a. Seda komai yalafa sannan suka sake wani wankan suka shirya suka fito zuwa dinning inda Aisha Itama fitowarta kenan, d'auke da Hanif d'ayan hannun rik'e da hannun Yusuf,cin abinci sukayi cike daso da k'aunar junansu. Rayuwa taci gaba da tafiya cigaba ta ko ina zuwa yake musu komai tare yake musu ba banbanci, amman matsayin Surbajo aranshi dabanne yana mata son dashi kanshi besan iyakarsa ba, kuma Itama haka ko kad'an bata had'a soyayyarshi data kowa, iyayenta yana ganin darajarsu haka Itama tana ganin darajar nasa iyayen, rushe gidansu yayi a rugar yamusu gini na zamani dede da rayuwarsu,sannan yabasu jari me kyau dansu dunga sana'a, Surbajo har rasa bakin godiya tayi,sede fatan gamawa da duniya lfy data dunga yimasa. B'angaren Aisha ma rushe gidansu yasa akayi akayi musu gini nagani nafad'a yaba mamanta jari me yawa dan ta dunga juyawa Tana kulawa da yaranta, Wanda hakan yasa Aisha K'ara nadamar abinda ta aykata masa abaya sosai tayi masa godiya har tana kuka. Surbajo tasake samun wani cikin,Allah sarki Aisha murna takeyi fiye da ma Surbajon, tattali da kulawa daga Aisha har Al-ameen babu irin Wanda basayiwa Surbajo,tun cikin nak'arami Aisha tafara siyan kayan Babies tana tarawa unisex, Surbajo har dariya take mata. Cikin na wata takwas sukaje scanning akace musu Baby girl ce,Wayyo dad'i rasa inda zasu sa kansu sukayi dan murna. Siyayya suka shigayi kamar hauka don murnar Baby girl dazasu samu, basu da hira Seta cikin ahaka har Allah yasauketa lfy, tahaifo ta mace me kama da ita sak,babu inda ta barota har gwalo suka dunga yiwa Al-ameen na rashin d'aukoshin da Babyn tayi. Ranar suna baby taci sunan maman Surbajo, wannan Karon harda Ard'o seda yazo suna jin ansama Babyn sunan masoyiyarsa,suna kiranta da Hanifa. So da k'aunar da Al-ameen ke nunawa iyalanshi abin koyine ga duk magidanci kud'i basusa yarasa lokacinsuba duk kulawarsa nakansu bashida Lokacin komai senasu da iyayensa. Lokacin aykin hajji yazo dukansu yabiya musu ta international suka tafi harda yaransu, sunyi addu'oi sosai Akan Allah yaba Aisha haihuwa domin Alfarmar Annabi da Alqur'ani. Haka ranar tsayuwar arfa ma suka tsaya gurin yin addu'ar,suna kuka Surbajo tafi kowa yiwa Allah kukan yaba Aisha haihuwa domin girmansa. Lokacin dasukaje d'awafin bankwana da kyar Al-ameen ya b'anb'are Surbajo ajikin Ka'aba tana kuka tana sake rok'on Allah, ahaka har suka dawo gida Nigeria kullum addu'arsu kenan. Maman Yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *This page is dedicated to Zahra Muhammad Hausa novels group's nagode da irin soyayyar dakuke nunamin wlh acikin masoyana kune first Allah yasa yadda kuke sona Allah yasa inna mutu ku nunamin irin wannan soyayyar gurin yimin addua ngd banda kamarku yan uwana sonku ajinina yake love you all from the bottom of my inner heart.😍😍😍😍😍😍😍* Na jinjina muku.. Mrs fawwaz Anty khady garkuwa fareeda feedyluv Maman sultan Zee yabour hafsey Momyn janan Maman ihsan Kunada yawa wainda kuka dace a jinjinamuku Wanda bankira sunanshiba afuwan abinne da yawa mutuwa tashiga kasuwa,Allah yak'aramuku basira,yakuma d'aukaka pml up up up. p.m.l backward never insha Allahu. *pure moment of life writers* *p.m.l* *last page* *page 96-100* Allahu gafurur raheem watansu biyu da dawowa Allah yaba Aisha ciki zokuga Surbajo har azumi tayi na nuna godiyarta ga Allah daya amshi addua'rsu,Al-ameen yayi murna sosai itako Aisha harda kukanta gurin nuna godiyarta ga Allah. kulawar da Surbajo take bata abin gwanin Sha'awa dole su burgeka duk abinda Aisha takeson ci shizata bata ko menene, dayake cikin Aishan me kwad'ayine abubuwa da dama se anbar kaduna za'a samo mata shi in kwad'ayin abunda ba lokacinshi bane a kadunar ya motsa mata.ko kad'an basa gajiyawa da hidimarta wanda ita godiya kawai take musu da fatan alkhairi. Cikin Aisha se girma yake wanda girman cikin har tsoro yake ba su Surbajo sabida girmane na sose,gashi lafiyarta k'alau ba ciwon komai se na kwad'ayi gashi yanzu tazama rumbu cin abinci kamar hauka intaci kuma takasa tashi sesun d'agata. Watan cikin bakwai suka kwasheta zuwa scanning dan su girman cikin ya tsoratasu,koda sukaje cemusu akayi komai normal kawai de twins ne a cikin. Wayyo dad'i 💃💃Surbajo sujjada take yi tana k'arawa ga ubangiji shiko Al-ameen duk girman Aisha da cikinta be hanashi d'agata ba yana murna. Daga gurin scanning kasuwa suka wuce suka barta a mota suka shiga wani boutique na babycare suka shiga jidar kaya kamar hauka,daganan gida suka nufa. Har walima seda sukayi dan murna inda akai addu'ar Allah ya sauketa lfy. Watan haihuwarta yatsaya kullum cikin addu'a suke Allah ya raba Lfy, wata jumma'a Aisha ta tashi da ciwon nak'uda da sauri suka d'auketa zuwa asibiti. Da isarsu labour room akasata, Surbajo kamar zatayi hauka dan tausayin Aisha, addu'a kawai sukeyi dan shima oga hankalinshi atashe yake. Suna nan tsaye wata nurse tafito tamusu albishir data haihu Lfy ansamu twins duka mata,rungume juna sukayi Surbajo da Al-ameen suna nuna farincikinsu ga Allah. Bajimawa aka fito da me jego da twins d'inta kyawawa dasu aka kaisu d'akin hutu.Surbajo tunda ta d'auki yaran kasa ajiyesu tayi sabida kyan da Allah yay musu kuma abin mamakin yaran da Surbajo suke kama kowa seda yayi mamakin hakan. Aisha kallon Surbajo tayi murya araunane tace, "Sister nagode da addu'ar ki gareni,wlh base kin ce kina k'aunataba inda banyarda ke me sona bace yanzu dole nayarda duba da kammanin da yarannan sukeyi dake, nayi imani inba nagartacciyar soyayya hakan bazata yiwuba,nagode miki sister da addu'ar ki gareni Allah ya rabaki da bak'incikin duniya da Lahira,"tafashe da kuka da sauri Surbajo tamik'awa Al-ameen yaran tarungume Aisha tace, "Haba Aunty yau ranar murnace agaremu ba kukaba Allah ya amshi addu'ar damuka dad'e munayi danhaka godiya kawai zamuyi masa, kimance da komai Aunty na ni mesonkice." Koda aka Sallamosu Surbajo ce d'auke da yaran tun kan su k'araso gida gidan yacika da y'an uwa kowa murnar haihuwar su twins yake. Al-ameen yanajin son yaran har zuciyarshi badan komaiba sedan Kama da Surbajo dasukeyi bame kallonsu yace ba ita ta haifesuba, Allah Kenan. Ranar Suna Surbajo ba k'aramin mamaki tayiba, dataji yaran duka sunanta Aisha tace asa musu d'aya Zahra d'aya fatima suna kiransu da mamah da mimah, amman Al-ameen me suna zahran Surbajo

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});