Chapter 24
Chapter 24
baya, "tace wai nufinki dambe zakiyi Dani,?haba wuce nan Wlh, toke inbanda abinki inban girma yanzuba seyaushe zangirma?ace har haihuwa biyu Amman bandena dambe da yar wrestling ba, kinga, rufamin asiri, akan tarbiyyar Dana nake ,ina gudun yataso yaga ina hada kashi dake yadauka abune mekyau,kema nasan kinayi ne sabida ko kashi me tauri baki taba yiba bare ace kinsan zafin haihuwa, Dan haka ni banida lokacinki nayi nan. Tana gama fadamata tajuya zata bar gurin. Azafafe aisha tabi bayanta,dasauri Al-ameen yasha gabanta Wanda tun dazu tsaye kawai yake yana kallonsu,kokarin tureshi takeyi,Amman ina yafi gaban wannan rainin.tsawa yadakamata, Sannan Yancey, "is enough Aisha,i say is enough, yafadi cikin tsawa Wanda ba Aishan ba har surbajo seda ta tsorata, shiko Yusuf dake hannunshi, farkawa yayi agigice yana kuka. surbajo dasauri taje taamshi danta ahannunshi,gudun kar yayarmata dashi garin fadan. cigaba yayi da fadannasa,tainda yashiga batanan yake fitaba, Aisha ce takatseshi dacewa, "dalla yaisa haka mijin tace, Tunda tariga data wanke tabaka kasha ay dole kazo kaina kana balai.surbajoce takatseta dacewa, "lalle keko Aisha andade da baroki abaya,ayni nafi karfin nawanke nabashi yasha sede yasa bakinshi yasha.hala ke wankewar kikeyi shiyasa kika dauka kowama garane irinki. Tsaki tayi tawuce dakinta, tabarsu tsaye baki bude. Aisha kuka tarushe dashi agurin,wai surbajo tamata gorin haihuwa,sosai take kuka,Dan bata taba jin ciwon rashin haihuwartaba se yau. Al-ameen ko dakinshi yawuce,bebi takan kowaba, dan gaskiya abinda suke yafara kaishi bango, badama suhadu sesunyi fada,kuma laifin na aisha ne, Tunda ita take fara tsokanar surbajo. Ranshi yabaci sosai yau dinnan duk wata shaawar surbajon tagudu sabida bacin rai. Wanka yayi yashirya, sannan yafice agidan,restaurant yanufa,yasiyo abinci ,sannan yadawo gidan. tunshigar surbajo dakinta,gado tafara gyarawa, yayinda Yusuf ke goye abayanta ,bayan tagama gyaran gadon, kwantar da Yusuf tayi akai, sannan taci gaba dasauran ayyukan. fes tagyara koina takunna turaren wuta,koina se kamshi yakeyi,kitchen tashiga taduba store taga komai akwai nabukata, refrigerator tabude taga awai nama Kala Kala duk sunyi kankara sabida rashin amfani dasu, girki tashiga hadawa Wanda tasan Al-ameen naso ,se kamshi yake tashi, Tana gamawa,tajera kulolin abincin akan dinning table, sannan tanufi toilet tayi wanka,tana fitinanniyar tashirya acikin wasu ubansun English wears, tayi kyau sosai,barin turare tayiwa jikinta sannan tanufi dakin Al-ameen. sallama tayi tatura kofar tashiga, fuskarta dauke da faraa, Faraarce tagudu daga kan fuskartata,yayinda taci Karo da al-ameen zaune yanacin takeaway din dayasiyo dazu, rai abace taje takwace abincin agabansa,dagowa yayi dasauri danyaga wacece,yawun bakinshine yakafe,sanda yay arba da amaryarsa wacce bata laifi kota wanke plasma da laptop. itako Fara magana tayi Tana diddire kafa, kamarde yadda yara sukeyi inzasuyi rigima. "haba dear, yanzu kamin adalci kenan?Tunda nadawo ban zaunaba, seda natabbatar nahada maka abinci, shine kaje kasiyo awaje ,salon kajamana zagi, ace babban mutum kamarka baa girkamasa abinda yakeso agidansa,kuka tamasa na shagwaba juyawa tayi zata bar dakin dasauri yakamota tafado jikinshi,tana cigaba da kukannata. shiko Al-ameen mamakin kanshi ne yakamashi,ganin tun baaje koinaba yadena fushin, shida da cewa yayi seyayi wata bekulasuba. rarrashin gimbiyarsa yashiga Yi,dakyar tahakura, sannan tace yataso suje suci abincin,ba musu yarukota suka nufi dakinta, sun fito kenan, suka ci Karo da Aisha tafito cikin shirin fita anguwa, kallonsu tayi tawatsar tafice agidan. Al-ameen kada kai kawai yayi, sabida kobaa fadamasaba, yasan gidan aminanta tanufa. Janshi surbajo tayi,ganin yabi Aishan dakallo, sunci abincin sun koshi,kuma abincin yamasa dadi, Dan dakyar yaiya hakura da abincin badan bakinshi yagajiba sedan cikinsa daya cika. daganan duniyar maaurata suka fada,Al-ameen jiyayi kamar kanshi zejuye,sabida sabon test din dayaji game da ita. bayan komai yanatsa, sunyi wanka,lokacin Yusuf yatashi, wanka tamasa tashiryashi taba Al-ameen shi yarike , Itakuma tanufi dakin Al-ameen din domin tagyara maman yusuf ?????????????????? *SURBAJO* ?????????????????? Zahra Muhammad mahmud *This page is dedicated to Maman gidado,juwairiyyatu,maman Irfana, Hafsat Dahir,maman Muallim, Mrs Lukuman,mrs Shamsur.thanks for the care and support am really appreciate it* *page 61-62* Tunda Al-ameen yadawo da surbajo gidan kullum ba ranar banza da Aisha bazata nemi surbajo da rigimaba. Itako bata kulata ko kadan,lokuta da yawa dakinta take shigewa tabarta Tana 'ba'batu. Yau asabar tun safe surbajo keta shiri,sabida Al-ameen yace, tashirya suje makarfi,murna gurin surbajo baa magana,kamin Tara tayi tuni tagama shiryawa ita Da Yusuf,oga kawai take jira yafito,dayake ba girkinta bane Aisha ce dashi, Se karfe goma Al-ameen yafito cikin shirinshi na tafiya,lokacin surbajo duk tagama kosawa,koda yashigo dakinta, kauda kanta tayi gefe, ita ala dole tayi fushi. Karasawa yayi kusa daita,yaruko hannunta yace, "haba my charming princess, menayi kuma ake fushi Dani? Turo bakinta tayi gaba, alamun shagwaba,tace, "ay bandauka yanzu zaka fitoba,nadauka se wata safiyar, Dariya yayi kawai,azuciyarshi yasan kishine yamotsa nanko batasan shikadai yakwanaba.amma afili cewa yayi,"am so sorry baby it will never happen again OK, yadaga mata gira daya??ya kashe ido daya. Murmushi tayimasa, metafiya da hankalinsa,sannan,tamike tadauki jakar kayansu,shikuma yarungumo Yusuf suka nufi mota. Tafiyace sukayi mecike daso da kaunar junansu,Al-ameen ne ke driving din dakansa. Se wajan shabiyu na rana suka isa garin,wayyo dadi, surbajo rasa inda zatasa kanta Tayi,suma 'yan gidansu kowa se tattalinta yakeyi,Yusuf ko, tuni ardo yaamsheshi yanamasa wasa,sosai kowa ke murna da zuwansu,kankice me gari yadauka duka surbajo tazo da mijinta harda Danta,nanfa jama'a sukaita zuwa ganinta,kowa yazo da tsarabarsa yake fita. Al-ameen har mamakin farinjinin surbajo agurin yan garinsu yake,yaga kowa da farincikinsa yake zuwa ganinta. Surbajo babu inda batajeba acikin garinnasu,tagaida kowa kuma tamusu abin Alheri. Shide Al-ameen behanataba,yana zaune tare da ardo da Yusuf,Dan ardo hana surbajo tafiya yawon gidajen yayi da Yusuf din,wannan Abu da ardo yayi,yafaranta ran Al-ameen sosai. Se magaruba suka baro garin,dan fafur yahanata kwana, ba irin magiyar dabatayiba amma yaki,ardo ma kuma yagoyamasa baya,shiyasa suka tafi. Karfe takwas na dare suka shiga gida,dayake girkin surbajone sallama kawai yaje yayiwa Aisha yadawo bangaren surbajon, adaren, tamusu girkin abinda zasuci, Dan ta tsani siyan abinci awaje. *********** Bayan shekara daya, Rayuwa taci gaba da tafiya, inda abubuwa da dama suka faru,aciki harda auran munawwara inda ta auri wani custom suna zaune a Legos. Bangaren Al-ameen ko, sauyin gurin ayki yasamu gamida Karin girma ,yanzu andawo dashi Abuja da Ayki, Da surbajo yatafi, Inda yanemar mata university anan abujan, tafara zuwa, Tana karantar low. Tuni ta yaye yusuf sabida yaron akwai girman jiki, ga wayo sosai bame zaton shekararsa daya Da wata biyar sabida girmansa,a kaduna tabaroshi, gurin iyayen Al-ameen din,tundaga yaye suka rikeshi. sede duk sanda al-ameen yasamu dama,yazo kaduna gurin Aisha, yay sati biyu Yakoma Abuja, Bangaren soyayyarshi da surbajo se abinda yayi gaba, kullum burin kowa yafaranta ran Dan uwansa. Surbajo takara gogewa, yanzu tayi kiba, ga wani haske datayi, bame cewa tahaihu har so biyu. wani zuwa kaduna da Al-ameen yayine yatarar da Aisha kwance afalo ba Lafiya duk tayi amai tabata guri,arude yadauketa yamata wanka yashiryata suka nufi asibiti, Bayan aune aune daaka matane likita yamusu albishir dacewa Tana da ciki natsawon wata uku,murnar dasukayi fadinta bata lokacine,koda suka dawo gida tattalinta yakeyi kamar kwai, su Aisha abunnema yasamu,se kara narkemasa takeyi,shikuma yana biyemata.sati biyu yazo da niyar yi,amma seda yayi sati hudu,dan kulawa da Aishan, sabida cikin me laulayine sosai, Koda yafadawa surbajo,murna tayimusu gamida fatan Allah yasauketa Lfy, itace ma tabashi shawarar yakara kwanaki,dan yakula musu da baby da kyau, Ranar daze tafine, yaje gidansu Aishan yadauko mata kanwarta danta tayata Zama,su Aisha harda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34