Chapter 23
Chapter 23
da gaske ita wai yabata kunya Kamota yayi yana fadin to sannu mekunya bakiji medaddy yacebane kinga so nagaskiya baa kunyar idon kowa nunashi ake aduk inda yakama kuma mu nan gidan baruwanmu da wannan kunyar taki muna rayuwane so simple nande suka buge da romancing din juna Kwankwasa kofar akayi suka bada izinin shigowa amal ce dauke da Yusuf yafara kuka dasauri alameen yaamsheshi yasoma yimai wasa Dena Kukan yayi alameen yace that's good my resemble Dariya surbajo tayi tace ah lallefa su resemble anji jiki nima zanhaifo my resemble dinne ingata iko se bayan laasar alameen yabar kaduna cike da kewar surbajo da yaronshi itama surbajo kuka taitayi bayan yatafi sabida har ga Allah batason tanayin nisa da mijinta sabida bukatunsa madam Aisha kuwa bakincikin abinda alameen yamata yasa takasa ko cin abinci aminanta tafadawa suko abun yamusu dadi Amman afili nunawa sukayi suna tausayinta harda cemata zasu dauki mataki takwantar da hankalinta rayuwa tacigaba da tafiya inda har surbajo tayi arbain tambayar alameen tayi zata ruga ganin gida cewa yayi tabari yazo tukuna sesuje tare bayadda batayiba amma yaki har mommy tasa baki fafur yace sujira yazo tukuna shida kanshi ze kaisu abin yama surbajo zafi tsawon shekara biyu da auransu bata taba zuwa gidaba Amman yanxu tace zata shine zece tajirashi Kiranta alameen yayi yanamata gargadi akan karta sake tatafi seyazo ayko rufe ido tayi tanata fada hardacewa in akan babynkane kahanani zuwa asalina tozanbarmakashi agida inje nikadai danna fahimci kana gudun innaje dashi ruga ze cutu ne to ni kabarni inje tunda ni dama acan nataso maganganude marasa dadi tafadamasa alameen runtse ido kawai yayi yana sauraronta ranshi namishi kuna kashe wayar yayi yahiga tunani tabbas surbajo tayi gaskiya beso taje da Yusuf rigar gudun yakamu da wani ciwon shiyasa beson taje sedashi to amma ay Tunda befadamataba bedace tafadamasa maganaba har haka itama surbajo sebayan yakashe wayarne hankalinta yatashi tuno irin maganganun data fadamasa tabbas bata kyautaba kiranshi tashigayi tabashi hakuri Amman fafur yaki daukar wayar tamasa text shima baamsa .hankalinta tashi yayi tashiga rusa kuka har mommy tashigo dakin tasameta tambayarta abinda yafaru tayi bata boyemataba tafadamata abinda tayimasa murmushi mommy tayi tacr baki kyautabs surbajo Amman kibari zanmasa mgn konan gaba Karki sake yimasa irin haka kinjiko sosai surbajo tagamsu da zancan mommy itade burinta abashi hkr ?????????????????? *SURBAJO* ?????????????????? Zahra Muhammad mahmud *page 57-58* Waya mommy tadauka takira al-ameen,bayan sungaisa, hakuri tabashi akan abunda surbajo tamasa. Godiya yayiwa mahaifiyartashi, sannan sukayi sallama bayan yatabbatarmata da yahakura. Surbajo murna tayi dajin yahakuran, sabida duk abinda sukecewa taji don wayar a speaker take.itama godiya tayiwa mommy tare da alkawarin bazata kumaba. Tundaga ranar,surbajo kotakirashi awaya,baya sakin jiki suyi hira kamarda, sede yatambayi lafiyar danshi shikenan. Abun yanama surbajo zafi Dan bata Saba irin hakan dashiba. Yauma kamar kullum,kiranshi tayi awaya suna gama gaisawa yafara kokarin kashe wayar,dasauri surbajo tace, "Abban Yusuf Don girman Allah kayimin afuwa, nasan namaka laifi amma zuwa yanzu yadace kayimin afuwa kodan darajar mommy datasa baki please" Karashe zancan tayi Tana kuka. Al-ameen baze iya jure jin kukantaba,zuciyarshi zafi takeyi jin kukan surbajo akunnensa.dasauri yakashe water. Surbajo kifewa tayi agurin Tana kuka,kukantane yatashi Yusuf dake baccinsa hankali kwance. Mika hannu tayi tadaukoshi tasamishi nono abaki yafara sha itakuma taci gaba da kukanta. Al-ameen jiyayi gaba daya garin yaisheshi, dama next week yake saran zaa bashi hutu, Dan haka jiyayi kamar tayi tsuntsuwa yaje gareta yakeji. Ranar jummaa dawuri yashirya yabar garin, Dan karfe takwas ta Safiya a kaduna tamasa, besanar Dakowa zuwanshiba Illa driver dinsa,kaitsaye gidan iyayensa yanusa, sunyi mamakin ganinsa,bayan yagaishesune yawuce dakin da madam take. Tana kwance Tana kuka, yayinda yusuf keta bacci. karasawa yayi gurinta yazauna agefenta. jin motsin mutum ne yasata fara goge hawayenta dasauri Dan tadauka mommy ce kosu munawwara. Suman kwance tayi da ganinsa, fuskarta take mitsikewa Dan Tana zaton gizo yakemata "kukan mekikeyi? shuru tayi masa Tana goge hawayenta . Kamota yayi yarungume,aykamar jira take ,rushemishi tayi dakuka Tana fadin " haba dear,Ashe nangabama zaka iya rabuwa Dani har abada kenan,nace kayi hkr amma kaki Kayi, yakakeso inyi da raina? Bakinsa yasa acikinnata, dan bayason maganar datakeyi, soyake yamantar da ita bacin ran,kuma dama yamata hakanne gudun karta samu kafar rainashi, tadunga fadamasa magana son ranta kamar Aisha. surbajo jin bakinsa acikin bakinta yasa kukanta yatsaya, tuni gyaran da mommy taimata yafara ayki, dan sosai mommy take gyaratada magunguna masu kyau, shiyasa itama yana fara yimata kiss din, itama Tashiga maidarmishi da martani. ganin suna neman wuce gurine yasa takwace kanta dakyar Tana maida numfashi. shiko Al-ameen rasa yazeyi yayi, Dan gabadaya hankalinshi yagama tashi burinshi yakeba da matarshi. Mikewa yayi yadauki Yusuf sannan yace mata "dauko gyalenki mutafi gida" surbajo jiki har Bari yake gurin neman gyalen, Dan harga Allah tagaji dazama gidan iyayensa,wajen watansu uku agidan. jakar kayansu tajawo,yana gaba Tana biye dashi abaya har zuwa falo,boyewa tayi abayan Al-ameen, Dan abun da kunya,Amman bata da zabin dayawuce tabi mijinta. gabadaya falon kallonsu kawai sukeyi,bakunya Al-ameen yace "mu munwuce gida seda safenku" dariya gabadaya falon akasa,itade surbajo Tana boye abayanshi tarufe fuska tamkar Amarya. mommy tace "to Allah yabamu alkhairi shugaban marasa kunya,matar tazo wanka shine bazaka jira amaidatabako? dariya yayi,sannan yace "mommy to aydama nine nakawota dakaina,kinga balaifibane danmuntafi kuma tare yanzu". daddy dariya yayi sannan yace "baruwanki dasu, aminullahi kuje abinku Allah yatashemu Lfy". Dagudu surbajo tafice afalon, mommy nacewa tatsaya suyi sallama, amma ina tuni tafice Dan batason Su hada ido da mommyn. Al-ameen jakar kayan da surbajo tagudu tabari yaja da hannu daya, dayan hannun kuma yana dauke da Yusuf,yamusu sallama yafice yabarsu sunata faman tsokanarshi. Amota yasameta,direbansa yasamasa jakar abaya, sannan yabude masa baya yashiga inda surbajo take,direban yazagayo yatada motar suka fice. Seda taji anfara tafiya tadago fuskarta, Dan Tunda tafito take rufe da fuska. Murmushi tayi Tana kallon Al-ameen Wanda yadage dayiwa Yusuf wasa.dagowa yayi yakalleta sannan shima yayi dariya ,sannan yace, "wallahi ko alabari bantaba cin Karo da mara kunyar mejego irinkiba.kubiyu kawai nasani, daga ke se indon kauye ta Ali nuhu, masu gudowa daga gida tunkamin amaidosu dakunan mazajensu .yafadi yana dariya.cuno bakinta tayi alamar shagwaba tace, "au hakama zakaceminko? nagode .baka ma barni da kunyar su mommy ba, shine zaka soma yimin tsiya, ay gwanda ni akan indon kauyen, ni mijinane yaje yadaukoni,itako gudowa tayi, Kuma ba laifinkabane, laifinane dana biyoka, Danhaka ni asaukeni Nakoma. Tafadi Tana shirin yin kuka. Dasauri yarungumota tagefe, fadi yake,"kirufamin asiri my baby don Allah, inkika koma can kuma yakikeso inyi dawannan nauyin? "kaje matarka tasaukemaka" Tabashi amsa. kara rukota yayi sannan yaradamata akunne," no baby wannan lodin nakine, Dan haka dole kece me saukeshi . duka takaimasa nawasa hakade suketafaman raha a motar har suka iso gida Maman Yusuf ?????????????????? *SURBAJO* ?????????????????? Zahra Muhammad mahmud *This page is dedicated to ummun Yusura thanks for the care and support.*???? *page 59-60* Suna isa gida,afalo suka tarar da uwargidan.ganinsu atare bakaramin mamaki yabataba,dan zatonta daga patakot din suke. Sallama suka mata,amma bata samu damar amsawaba. "daga ina kuma akuya da dantaure"?itace maganar aisha tafarko. Amsa surbajo tabata dacewa "daga yawon Barbara muke balama" "kan bala'i,dan ubanki nice balamar ?wlh yau senayi maganinki agidannan shegiyar yarinya Mara kunya kawai"cewar Aisha Tana kokarin cakumo surbajon. Dasauri surbajo taja
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34