Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Budurwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,251 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sabida Tana da exam, daga gidansu gidan Yan uwan Maman surbajo sukaje, Sunyi murna daganinta sosai, sunjima agidan sannan sukayo gida . washe gari da safe al-ameen yahadasu da driver yamaidasu Abuja,sabida shi ba yanzu ze tahoba se jikin aisha yakara sauki,duk da mamantace ke zaune da ita, se aminan ta dakullum suke gidan. sannu ahankali Aisha kesamun sauki harta warke gaba daya,lokacin tuni al-ameen yakoma Abuja gurin aykinshi.komawarshi bajimawa akasa Yusuf amakaranta, sabida Yusuf inyafado wata maganar zaka dauka bashine yayitaba. *jama'a albishirinku* aminan aisha de lokaci yayi inda kowaccensu tasamu mijin aure, kuma duka mazajen a kaduna suke sede anguwace kowa datashi. Se anriga yin bikin zuly da sati biyu zaayi na Ruky,wayyo rawarkai, ay Aisha ce tadauki nauyin yimusu setin kujeru dukansu, abun yamusu dadi sosai.yayinda azuciyarsu ko mugun fata suke mata. Anfara hidimar biki su aisha bazama sune can sune nan, ranar asabar aka daura auran zuly da mijinta Musa,sosai akayi bidiri abikin inda aka Kai Amarya gidanta dake makarfi road can hayin rigasa, layin tattali blocks, semuce Allah yabada zaman Lfy. haka lokacin bikin Ruky ma yazo aka sha biki inda ta auri wani mesuna baballe itama ankaita gidan mijinta dake unguwar dosa layin commissiona road. muje zuwa riders Maman Yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *this page is dedicated to my sweet Aunty,hajiya meelmoh, owner of meelmoh magazine.Allah yatsareki aduk inda kika shiga* *page 67-68* Al-ameen ne zaune, yayinda surbajo Tay matashin kai da cinyarsa, Suna hira. Al-ameen ne Yace, "madam yaushe zaki bani new baby ne?yafadi yana shafo cikinta,dariya tayi medaukar hankali,hannu tasa Tana wasa da dimples dinshi,sannan tace, "lalle ma my dear nan,nafahimceka sokake inyi saurin tsufa, inbanda abinka ay yanzu hutawa yadace inyi Dan haihuwa barkatai seyajawo natashi ayki dawuri,cuno baki tayi sannan tacigaba,dan haka ni kadena wannan maganar yanzu kabari sena gama karatu. Al-ameen mamakine yacikashi naganin zallar kuruciyar surbajo, wacce yafahimci dole seya setamata hankali,magana yafara da cewa, "baby yakike magana kamar bakida ilimi,menene aybu inkin haihu yanzu,karki sawa kanki akida tawasu mutane marasa tunani,tonide soyayyar dazaki nunamin itace kihaifamin yara,taya yaro daya kawai kice kinaso ki huta,hutun jaki da kaya ko?.itade Tunda yasoma mgn kallonshi take Tana murmushi, Dan dama tafadine taji mezece. Kallonta yayi yaga Tana dariya,dakatar da maganar yayi yana dubanta,rungumoshi tayi Tana dariya tace,my Legend kenan maida wukar surbajo tsokanarka takeyi,haifa maka yara inde Allah yabamu yanzu nafara so no need to be worry, rumgumeta shima yanada dariya yace, "lalle baby wato kinmaidani kakanki ko,seki fadi maganar dakikasan dole Sena tada jijiyar wuya ko?to daga yanzu naganoki bazan Kara bata bakina gurin maganaba wannanne hukuncinki, yana fadin haka yasureta yay cikin daki daita suna dariya. Muleka gidan amaranmu. Zuly da angonta Musa, soyayyace akashata bata wasaba har ta tsawon wata guda.bayaga haka, Yau tun safe Musa yafita yabar gida shuru bedawoba har karfe goma nadare,hankalin zuly inyayi dubu yatashi,gashi wayarshi takira Tana ringing Amman baa dagaba, Tana nan zaune afalo taji alamun bude get lekawa tayi ta window ganin motarshi ke shigowane yasa hankalinta yakwanta dasauri taje ta bude kofar, sannan tajuya dakinta takara gyara makeup dinta tafesa turare,sannan tadawo falon, sede me? Tana zuwa falon Musa tagani dawata yarinya maana karuwa tarukoshi yana tangadi ga kwalbar gulder ahannunshi yana korawa, Salati tayi Tana fadin, "nashiga uku Musa mezan gani acikin gidana,giya da karuwa , innalillahi wainna ilaihirrajuun, Wlh baze yiwuba, kan budurwar tayi tana fadin, "wlh yau se zina tazamemiki karshen aykinki aduniya matsiyaciya tsinanniya, Musane yakatseta dacewa cikin muryarsa ta me Maye, "narantse da girman Allah kika kuskura kika tabamin blessing Wlh Sena fafemiki ciki, kuka tasa tace, " musa yanzu akan karuwa zaka hallakani? amsa yabata dacewa,"eh karuwar kuma Wlh tafiki daraja a idona, ke!bakebama uwarki wannan tafita mutunci a idona, Dan haka ki kula,yana gama fadin haka yaja hannun blessing suka shige dakinsa suka kullo kofa. Kai ta dafe tafada kan kujera Tana kuka iya karfinta. Tuge dankwalinta tayi Tana Ta share hawayenta dashi. ranar zuly bata runtsaba Tana zaune afalo, Tana jiyo sautin bidirin da akeyi akan gadonta na Sunnah . Washe gari da safe haka musa yasata agaba dole ta dafamusu ruwan wanka, kuma yace ta tabbatar ta hada musu breakfast kamin su fito,bata da zabin daya wuce tayi abinda yasata,dan bakaramin so takewa musaba Tana tsaron yasaketa takoma gidansu da zama, dama gashi ta juma batayi auranba. haka rayuwar zuly taci gaba da tafiya agidan Musa,zuwa yanzu bakoyaushe yake kwana agidaba,wanda hakan ita yafimata dadi Dan in agida ze kwana toko da 'yan tayan kwana yake zuwa biyu ko uku Dan yanzu likkafa taci gaba yafi karfin mace daya sede biyu zuwa uku, kuma ingari yawaye duk kayansu itace me wankewa inba hakaba taci duka,koda wasa bata taba ba kawayenta labariba bare takai kararsa gidansu. yau da wuri Aisha tashirya, sabida tanason zuwa gidan zuly tawuni,sabida Tunda akayi auran so biyu taje shima lokacin ko wata batayiba. karfe takwas na safiya a gidan zuly tamata,wanda zulyn seda ta firgita da ganinta,afalo tasauketa,Aisha ko mamakin abinda yaramar da zuly tayi baki takeyi,kasa daurewa tayi seda ta tambayeta tace, "kawas meke faruwane dake haka kika Yi baki kuma kika rame, kamin tabata amsane suka jiyo karar bude kofar dakin zulyn. Musane yafito shida 'yanmatansa guda biyu,kowacce ta rungumeshi gashi kayan jikinsu kadai yaisa yasanar dasuwaye su , Arude Aisha take kallonshi, takalleshi ta Kalli zuly wacce tasunkuyar dakai Tana kuka, Kasa cewa komai tayi se ido, Musa ko bakunya ya Kalli Aisha yace "madam ykk? ya gida kwana dayawa kinyi wuyar gani ,mamaki ne da tsoro suka hana Aisha bashi amsa, ko ajikinshi Illa ajiye panties and bras na yanmatanshi Wanda suka cire agaban zuly yace "gasunan washing and drying and then ironing kamin mudawo .bejira amsartaba suka fice shida 'yanmatanshi. Azabire Aisha takai dubanta gurin zuly, tace, "today I saw the thing that I have never think it will be happen to you ever in your life,please zuly wake me up kice mafarki nakeyi please, tafadi Tana girgiza zulyn wacce inbanda kuka baabinda takeyi. Dakyar Aisha tashawo kanta tabata labarin abinda ke faruwa, zugata Aisha tashigayi kamarde yadda sukemata, ga mamakinta seji tayi zuly ta dakatar da ita dacewa, "Aisha waimeyasa kika dauka kowama banzane irinki,tobari kiji infadamiki kinga halinde danake cikiko,to wlh har gobe inason mijina kuma babu wani dalili dazesa inbarshi, zugarki gareni ki adanata kibari inkin samu wata shasha irinki seki bata tadauka Amman bani zuly ba, uhm Bari kiga inje inyi aykin lada tamike gamida kwasar kayan da Musa yaajiyemata na'yanmatanshi ta tafi wankewa. kwakwalwar Aisha seda tadena ayki na 'yanmintina, zuciyartace take harbawa da karfi yayin da wasu hawayen bakin ciki suka fara biyo fuskarta,bata da sauran magana Jakarta tadauka tabar gidan zuciyarta na mata kuna. muje zuwa riders Maman Yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad Mahmud *PURE MOMENT OF LIFE WRITE (P. M. L. W)* *page 69-70* Aisha dak'yar take ganin gabanta ahaka harta k'araso gida,jakarta da key d'in motar ta yardar akan kujera sannan ta haura sama inda D'akinta yake Tana kuka me tsuma zuciya. Wayarta taciro domin kiran Ruky dan gani take Ruky bazata ci amanartaba, Tana kiranta bajimawa Ruky tadauka tace, "hello Ashanty ykk"? cikin b'acin rai tace, "Ruky dama gadar zare kuke kullamin bansaniba? "meyafaru"? Ruky ta tambaya,

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});