Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Budurwa Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cikin barin jiki tace aradu nayafemaka kudin kuma Don Allah karka kiramin wainnan mugayen mutanan niko ganinsu banaso yin sabida nataba ganin yadda sukayiwa wani mutumi dukan tsiya akasuwa suka ciremishi kaya aradu mutumin yabani tausayi Danhaka kayafemin aradu bazan kumaba ganin ta tsoratane yasa alameen kwantar mata da hankali tahanyar cewa haba surbajo ayko nakirasu bazasu iya yimiki komaiba sabida kyanki ay surbajo najin haka tahau dariya sannan tace dagaske kakeyi basa Kama mekyau ehmana dagaske nakeyi kwace hannunta tayi daga rukon dayamata sannan tace to aradu nafasa yafemaka kudina seka bayani dariya alameen yayi yace ayko bazan bakiba sabida ke kikace kin yafemin kallonshi surbajo tayi sannan tace zaka biyanine tun biya nada dadi sunanan Ardo yadawo dafaraarsa ya tarbi alameen Yayinda yarufe surbajo da fadan meyasa bata kawomasa ruwa da shimfidaba alameen ne yace nine nace tabarshi base takawoba sannan Ardo yadena fadan mamakine yarufe surbajo tace a zuciyarta hoddijan aradu kado ko a makaryata shinadabanne kato dashi amma baya kunyar karya cikin gida ardo yaja alameen suka zauna suna hira sato jiki surbajo tayi tafito inda motarshi take tsinke tasa acikin tayoyin tasacemusu iska gabadaya Tana gamawa ta ruga gidansu arera Tana dariyar mugunta ita atunaninta hakan datayi baze Hana. motor tafiyaba sede yahanata yin sauri dalilin dayasa tasacemishi iskar kenan alameen hira tayi dadi Shina Shida Ardo besan magaruba takusaba seda yakalli agogon hannunshi mikewa yayi domin tafiya ardo nata samishi albarka kyauta yayiwa ardo metsoka sannan yafito daga gidan tsayawa yayi yana waigen ta ina ze hango cartoon dinsa tazo suyi sallama amma be hangotaba ardo yace aykawai kayi tafiyarka inde surbajoce takai takwas nadare bata dawoba tanacan suna wasa da saointa bahaka alameen yasoba Amman bashida zabin dayawuce yatafi sabida dare yafara Yi ga hadari yahadu sosai shiga motarsa yayi batare daya Lura da barnar da surbajo tamasaba seda yakunna motar security dake jikin motar yafara kara alamun akwai Matsala amotar fitowa yayi danganin meyasami motar innalillahi wainna ilaihi rajuun ita kawai yake maimaitawa ganin tayoyin motarshi a sace kobaa fada masaba yasan aykin surbajone dafe kanshi kawai yayi yana kallon motar yama rasa abinyi dama daya tasace dase yadauko spare din tayar dake boot yasa to duka hudunne gashi garin ko mashin babu me ita bare asamu Mesa iska wayarsa yadauko babu network sam kamin yagama yanke abinyi ruwan sama yafara sakkowa ardone yakaraso kusa dashi yace Aminu akwai matsalane kai yadagamasa sannan yamasa bayanin abinda yafaru da motar amma befada masa surbajo ce tamasa ba Dan yasan tsaf ze iya Zaneta suna nan tsaye ruwan yakarasa tsugewa kamar da bakin kwarya dasauri ardo yajashi zuwa wata bukka wacce dama anyitane sabida baki zama yayi akan gadon karan dake ajiye adakin ardone yajawo kofar bukkar yakare wacce take ajiye agefe itama takarace sunanan zaune ruwan betsayaba se misalin bakwai da Rabi nadare ruwan alwala ardo yaje yakawomasa yayi alwala yay sallah sannan ardo yakawomasa barguna guda biyu da fitilar aci balbal yace gashi yashimfida daya yarufa da daya yayi hkr yakwana anan inyaso gobe da safe ardon zeje cikin gari yakira mesa iskar yasamasa alameen bakinciki yagama rufeshi bakomai yake bashi haushiba se irin yadda ze kwana Abukka batare da wani tsaroba ko kofar arziki babu ga sanyi daaka fara kamar jaura tawuce shiyama zeyine gurin bacci akan gadon kara amma ya yaiya bashida zabin daya wuce hakan komawa motarshi yayi yadauko bindigarshi da touch light Wanda yaajiye amotar sabida tsaro surbajo se takwas tanufo gida itadasu arera dasuka rakota tabayan gida tashigo gidan Dan haka batasan alameen betafiba alwala tayi sallah sannan tafara tunanin oh kado koyaje gida yanzu oho sumayece takirata tace tazo takaiwa bako abinci yana dakin baki mamakine yakamata nayaushe sukayi bakon daukar abinci tayi tuwan dawane da miyar kuka danya yasha manshanu Wanda aka zuba a akushi na musamman tanufi bukkar bakin dayake motor alameen bakace kuma akasan bishiyar mangwaro yayi parking dinta surbajo bata Lura da itaba sallama tayi kofar bukkar daga ciki aka amsa shiga tayi taajiye kwanon abincin tajuya zata fito fisgota yayi da karfi tafada jikinshi zata samasa ihu yarufe bakin da hannunshi haska Mata fuskarshi yayi sannan yasakarmata baki arude tace kado meya hanaka tafiya gida kallonta yayi sannan yace haba surbajo meyasa Zaki sacemin iskar tayakinsan motar kuma bazata tafiba inba iska tausayinsane yakamata hawayene suka fara zubowa daga idonta cikin kuka tace Dan Allah kado kayi hkr aradu bansan motor bazata tafiba nadauka saurine bazatayiba Dan Allah kayafemin nasa Zaka kwana a inda baka saba tausayinta alameen yaji amma hakan baze hanashi hukuntata ba danyayi alkawarin yimata hukunci bindigarsa yazaro ya saitata kan surbajo Maman Yusuf 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 *SURBAJO* 🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀🍀 Zahra Muhammad mahmud *ina barar adduarku gobe in Allah yakaimu zanyi tafiya so atayani da addua inje Lafiya in dawo Lfy Wanda nataba batawa rai pls agafarceni nima nayafema kowa ngd* *page 19-20* Surbajo idanuwantane suka fito kurukuru ganin bindigar datayi jikinta sebari yake Alameen yace umarni zanbaki inkika kuskura kika ki bi sena harbeki yafada in a serious talk Girgizamasa kai yakeyi alamar tayarda Cigaba yayi da magana yace surbajo yau kinbatamin raina sosai so dole ne nahukuntaki Dede da iri laifin dakikamin Don Allah kado kayi hakuri aradu bazansakeba Tsawa yadakamata wacce ta tilastata yin shuru jikinta nabari Kara matso da bindigar alameen yayi dede goshinta aytuni fitsarin datake rikewa ya kubce alameen seji yayi yajike da fitsari bedamuba yacigaba da cewa umarnina shine zan aureki ko kinaso kobakyaso kuma idan kika sake kika nuna cewa nina tilasta miki aurena harbeki zanyi surbajo wacce tunda yafara magana numfashinta ke barazanar daukewa dakyar tace Don Allah kado kayi hkr inada Wanda nakeso kumashi zan aura Bigemata baki yayi yace ay ba raayinki nakeson jiba umarni nabaki kuma dole kibi inkinki ko dagake har Jaen sena harbeku Jikintane yakama Bari kamar mejin sanyi tace kayi hkr Don Allah karka kashemini jae aradu naamince zan aureka Wani malalacin murmushi alameen yasaki alamun samun nasara cikin ruwan sanyi alameen bekyale surbajo tatafiba seda yagama tsoratata sannan yace tawuce da gudu tafito tayi cikin gida kamin takai cikin gidan tafadi yafi so uku sabida agigice take koda tashigo Kowa yashige dakinsa sabida sanyin daakeyi itama nata dakin tashige wutar jin dumi ta tarar sumaye takaimata dakin ga kuma abincinta a akushi Gaban wutar taje tazauna bayan ta karo kofar dakin kuka tashigayi Mara sauti duk da tabon daya bata mata kaya bata damu taciresuba ita kawai tunaninta alameen Dan fashine Dan inba Dan fashiba baabinda zekawo bindiga gurinsa itayau yazatayi da rayuwarta Ashe Dama basuda rabon aure da jae gaskiya kado mugune Allah seya sakamana tafadi Tana cigaba dakukanta Wanda babu mesharemata ranar azaune surbajo takwana kowanne motsi akunnanta Dan tsoro takeji takwanta kado yazo ya harbeta Shima alameen Tana fita ruwa yadiba yasa ajikinsa inda fitsarinta yashafa sannan yaci abinci data kawomasa gaskiya yaji dadin abincin ruwa yasha sannan yakwanta badan yayi bacciba seda yaji dadin tuno dramarsa da surbajo juyi kawai yake yana murmushin jindadin gano surbajo nada tsoro dayayi ayko yasamu abinyi shima ranar beyi bacciba da sassafe ardo yaje cikin gari nemo mesa iska yaci wuya kamin yasamu Wanda yaamice zebiyoshi zuwa rugarsu suna zuwa yasa iskar alameen Wanda tuni yashirya yabiya mutumin kudinsa sannan yakarasa gurin ardo domin suyi

Table of Contents

Chapters

34 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});