Chapter 16
Chapter 16
dasu suke magana sosai hankalinta yakwanta dantasan aminan nata basa mata karya kuma Tana da tabbacin se Sun ramamata kwanciya tayi ranta fes Dan tasan gobe kashin surbajo yabushe Damisalin karfe hudu naasuba karar wayar alameen yatashesu abacci da kamar baze daukaba cande yadaure yadauka jin wayar se kira akeyi sunan oganshi yagani akan wayar dasauri yakwantar da surbajo yadauki wayar gaisheshi yayi cike da girmamawa kamar yana kallonshi dagacan bangaren ogan yace alameen duk abinda kakeyi kaajiyeshi ka komo office gobe jirgin daze daukoka is ready by 7:30am katabbatar kana airport sabida wani aykine yataso nasauri Wanda your attention is needed so am sorry nasan bazakaji dadiba amma kadaure de ran alameen besoba Amman bashida zabi Danhaka yacema ogan don't worry sir consider it has been done godiya ogan yayi sannan sukayi sallama yaajiye wayar bekoma bacciba sabanin surbajo dake ta aykin bacci dakinshi yaje yadauko duk wani abu daze bukata yasa a trolley yadawo dakin surbajo itama yahada mata abinda yasan zata bukata acikin trolley din wanka yayo yadauro alwala doguwar riga yasa sannan yatashi surbajo dakyar ta tashi toilet yarakata yace tayi wanka tayi sallah kamin yadawo bata musa ba sabida ya hadamasa ruwan wankan jamata kofar yayi yawuce masallaci koda zefita kulleta yayi tawaje Dan yasan abinda tayiwa Aisha jiya ba hakura zatayiba karfe shida yadawo daga masallaci surbajo tuni tayi wanka tayi sallah Tana zaune akan darduma Tana lazimi ganinshine yasa ta kudundune fuskarta ahijabin jikinta wai kunya takeji murmushi yayi yakarasa inda take yace baby na kunya ta kikeji kuma yanxu kinga tashi maza inshiryaki anguwa zamu dasauri tamike Dan surbajo kafar yawo gareta Waldorof yaje yadauko mata wata doguwar riga yar kanti fara har kasa yadauko su pant da bra da gyale da boy friend jacket tsaf yashiryata har makeup shiyamata amma simple one yamata surbajo ko duk kunya tagama cikata kallon kanta tayi mirror taga tayi kyau sosai ita kadai take Ta murmushi ba abinda yafi burgeta irin acuci mazan daya mata da gashinta yakuma yimata rolling din gyale ja akanta takalminta lowfas ne shima ja se boy friend jacket baka gaskiya tayi kyau dakinshi yaje yashiryo cikin kakinshi na soja dakin Aisha yaje Tana bacci kobaa fadamasaba yasan ko sallah batayiba tashinta yayi dakyar tamike tace meyakawoka dakina yanzu murmushi yayi yace uwargida sarautar mata Allah huci zuciyarki zankoma gurin aykine nazo naji mekike bukata wani dadine yakamata wato zasu Jidadin cin uban surbajo dakyau cikin sakin fuska tace babu abinda nake bukata se kudi dubu dari hudu yabata taamsa yace to senadawo kikula da kanki adawo Lfy tabashi amsa daga inda take alameen yayi mamakin yadda tamasa adduar yadawo Lfy abinda batayimasa dakin surbajo yadawo mamakine yakamata gamida tsoro ganinshi sanye cikin kakin soja yaganota amma seya basar jakarsu yadauko yaja hannunta yakulle kofar suka fice daga falon suna fitowa wani soja yataso yaamshi kayan yasa aboot suka shiga direba yajasu zuwa airport yayinda excode dinshi ke take bayansu suna zuwa ba bata lokaci suka shige jirgi kamin jirgin yatashine yakira iyayensa awaya yamusu bayani albarka suka samasa musamman dasukaji da surbajo yatafi hakuri yabasu gameda rashin zuwa yamusu sallama lokacine zewuce shiyasa bakomai suka bashi amsa Allah de yamasa albarka Godiva yayi yakashe wayar gaba daya surbajo ko inbanda zare ido baabinda takeyi rungumota yayi jikinshi bayan yadaura mata belt jirginsu yadaga zuwa rivers state. maman Yusuf Zahramuhammadmahmud. blogspot.com ?????????????????? *SURBAJO* ?????????????????? Zahra Muhammad mahmud *sugura Abdullahi, maman Irfana,fatima Radda,maryam Taheer. Don Allah ina kuka shiga kwana biyu pls inkuna tare damu munason sani am really miss you all* *page 37-38* Dan misalin karfe Tara nasafe su Ruky suka dira gidan Aisha lokacin ko sallah batayiba Tana ganinsu wani farincikine ya lullubeta kai tsaye dakin surbajo suka nufa Dan suna da tabbacin alameen bayanan Dukan kofar suke iya karfinsu kamar zasu karyata amma shuru baalamar zaazo abude can suka fara dura mata zagi gamida cewa inhar taisa tazo ta bude kofar jin shurun yayi yawane yasa sukace bari sutambayi masu gadi ko tafitane duk da suna tantamar hakan Duka su ukun sukaje gurin megadin Aisha ce ta tambayeshi ko Amarya daaka kawo jiya tafitane Baki yawashe yace ah madam you are so lucky oga yatafi da Amarya rivers state dazu Dan su Sunday ne ma suka rakasu airport ihu Aisha ta kurma tafadi agurin Tana kuka fadi take alameen kacuceni shine katafi da amaryarka ni kabarni agida nashiga uku nalalace ina zansa rayuwata Dakyar su Ruky suka jata zuwa cikin gidan hkr suka shiga bata itako ina kuka take kamar ranta zefita ita ba bakincikin rashin rama dukanta takeyiba bakincikin surbajo tarigata sanin gidan alameen nacan har azahar Aisha bata Dena kukaba gaba daya tarasa meke mata dadi aminannata se hkr suke bata gamida zugata akan tamasa rashin mutunci karta yarda da wannan wulakancin Ranarde Aisha basallah bare salati daga ita har aminannata ********* Karfe goma nasafe su alameen suka sauka a patacot Motocin excode dinshi nacan yatarar suna jiranshi Yana rungume da surbajo suka shiga mota aka jasu zuwa gidanshi dake gra din garin Tunda suka isa gidan kan surbajo kusan juyewa yayi sabida tsabagen haduwar gidan gudun karta kunyatashi agaban yaranshi yasa yayi sauri yajata zuwa cikin gidan Tafiya gagarar surbajo tayi sabida kallon datake alameen daukarta yayi yahaura da ita Sama dayake gidan six bedroom ne duplex daki yaajiyeta sannan shima yazauna itako zaman yagagareta sabida zabar kauyanci har bangon gidan shafawa ta dungayi da hannunta jawota jikinshi alameen yayi yace to madam surbajo Kalle kallen yaisa haka zomuje namiki wanka kici abinci Dan ni office zanwuce ana nemana Harara tawurgamasa sannan tace nifa kado banason abinda kakemin ina laifinma kace inje inyi wankan amma katuwa Dani kace zaka dunga yimin wanka ni aradu naiya wankana tafadi gami da murguda masa baki Murmushi yayi yace to shikenan naji muje inhadamiki ruwan wankan ba musu tabishi atoilet dinma seda sukasha daru Dan ita wai tsaron toilet din takeji sabida gabadaya glass ne toilet din gashi gurin wanka Jacuzzi ne dakyar de tayarda tashiga shima seda tayi addua sannan tashiga kulle mata kofar yayi yafito yabata guri wayar kukun gidan yakira yace yashiryamusu dinning gasunan zuwa yana gama wayar dakinshi yaje shima yayi wankan yasauya wasu kakin yanufo dakin surbajo atsaye yasameta daure da Towel Dede gwuiwa ta rufo wani kuma akanta tana ganinshi tajuya da gudu Zata koma toilet din gudun karyaganta ahaka aytana fara gudun towel din data dauro yakwance yafado kasa ihu tasa itama tazauna agurin habawa alameen mezeyi inba dariyaba gefen gado yazauna bayan yadauke tawul din dayafadin dariya yacigaba damata surbajo kuka tasamishi akan yabata tawul din amma alameen ko ajikinshi dariyarshi kawai yakesha nakanta tacire daniyar daurawa wuf shima alameen yakwaceshi ay surbajo kwanciya tayi agurin rub da ciki Tana kuka dakyar alameen yadena dariyar kuma shi bakomaine yabashi dariyarba se ganin ita megudun karyaga cinyoyinta segata tayi tumbur kuma agabanshi karasawa inda take yayi daukota yayi cak yadorata akan gado dasauri surbajo tanade jikinta da zanin gadon kukanta taci gaba dayi ita ala dole taji haushin ganinta dayayi tsirara niko nace inbanda shirme irinna surbajo ay gado ba bakon tsirarabane dazata dunga damun kanta trolley din kayansu yanufa yaciro mata wasu English wears riga da wando pink color wandon three quarter
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34