Chapter 9
Chapter 9
yi jajur. Suna haɗa idanu da Zakin ya yi wata irin kururuwa ya yo kanta gadan-gadan..... _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [30/11, 14:41] Umma Amjad: _*🧟♀️ALJANAR GIDANMU 🧟♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ _Masu son littafin *ABBA NE* complete N500 ne ku tuntubeni ta WhatsApp number na👇🏻_ *بسم الله الرحمن الرحيم* 0️⃣5️⃣ Hannu Amra ta ɗaga sama sai ga wata takobi ta bayyana a hannunta, cake takobin ta yi a ƙasa har sai da ƙasar gurin ta yi wani irin girgiza. Ja baya Zakin ya shiga yi tana binsa riƙe da takobin, cikin kakkausar murya ta ce" Ni har zan baka umarni kaƙi bi? Yaushe ka soma taurin kai ban sani ba Aliyu? Mai wannan yarinyar ta maka da ka firgitata haka? Kasan kalar hukuncin da nake yiwa mutane idan suka taɓa Auta? Babu ruwana da tsakanina da kai tsam zan iya aikaka lahira indai ka ce za ka taɓa mini Ƙawata" Ta ƙarashe maganar tana ɗamko wuyan Zakin." Ƙoƙarin kwace kanshi ya shiga yi amma ina ta masa ƙwaƙƙwaran ruƙo, sai da taga ya galabaita kana ta sakeshi ya faɗo ƙasa tim. "Ka kula bana son shiga abin da bai shafeka ba.. Cikin fushi Zakin ya soma rikidewa ya dawo wani kyakyawan saurayi matashi mai tsananin kyau, jikin shi sanye da ƙananan kaya, kallon Amra ya yi data saɓa Auta a kafaɗa ya yi, cikin shashekar kuka ya ce" Haba Yaya Amra yanzu ke kina ganin abin da kike yi daidai ne? Ko kin manta da abin ahalin yarinyar nan suka mana ne? Gaskiya ki canja tunanin dan ta taimakeki dhi kenan sai ki zubar da makaman yaƙinki ki ce ba za ki iya rama cutar da aka mana ba? Kina nufin sunci banza kenan? Wallahi ba zai yiyuba da Yaya Amina tana nan ai kin san ba ki isa ki fara wannan alaƙar da yarinyar nan ba, ko kuwa dan kinga ba ɗaki ɗaya muka girma ba shi ya sa kike abin da kikeso? K.. Ya isa Haidar! Ta faɗa a tsawace tana kallom shi, a kufule ta ɗamko hannun shi suka iso bakin duntsen ta shafa a fusace ta ce" Banza mai manta alkhairi kalli nan ka gani" Ta ƙarashe maganar tana nuna masa inda ta shafar.. Auta ya gani a cikin yara tana raba musu abinci sai murmushi take saki, wani makaho ta hango zia tsallaka hanya da sauri ta aje hular abincin ta nufi inda yake da gudu, taimaka masa ta yi ya tsallaka hanyar kana ta dawo ta ɗauko abincin dayawa ta kawo masa.. Murya makahon suka ji yana cewa" Yarinya kina da kirki Allah ya kareki daha dukkan sharri, in sha ba za ki wulaƙanta ba a idon Duniya." Amin ta faɗa tana murmishi kana ta wuce. Amra ta shafa jikin dutsen ta kuma cewa" Kalli nan ɗan rainin hankali." Autar ce dai ta fito daga ciki jin hayaniyar Babanta, Maigadi ne durƙushe Daddy na masa faɗa hakan, tana gefe sai da ya gama ya fice ta iso ta tashi Maigadi tana ba shi haƙuri, tambayarsa ta shiga yi akan me Daddy ke masa faɗa haka baiga girman shi ba? "Auta albashina nakeso wata biyu kenan bai bani ba, kuma Ƴata ake yiwa aure idan har bai bani ba ban san da mai zan fita kunya ba" Ya ƙarashe maganar yana zubar da hawaye.. Ranta ne ya yi matuƙar ɓaci ta bashi ta juya ta ce tana zuwa yanzu za ta dawo, daret ɗakin Daddy ta nufa ta buɗe lokar gefen gadonsa, kuɗi ne ɗauri-ɗauri a ciki daga kan naira zuwa dollars, hannu tasa ta ɗauko ɗaurin 'yan rafa gida biyar ta zuba a cikin rigarta ta fito da gudu gudu, a palo ta haɗu da Fadila tana aika mata ruwan ashariya amma bata kula ta ba ta wuce ta dawo gurin Maigadi ta kama hannunsa suka shiga ɗakinsa, kuɗin ya aje a gabansa ta dubesa ta ce" Baba ka rabu da Daddy bashi da tausayin na ƙasa da shi, ka ɗauki wannan kuɗin kaje ka sayawa ƴarka kayan ɗaki zan cewa Mommy kana yiwa ƴarka aure sai muje ranar ɗaurin aure.." Baba Maigadi ya tsorata da ganin kuɗin da yake gabansa, ya ce ba zai dauka ba ya yi yawa, sai da ta ɓata rai kana ya ɗauka ya mata godiya sosai tare da mata addu'a, sannan ya haɗa kayansa tana tsaye ya fito ya yiwa sauran abokan aikinsa sallama ya tafi, sai da taga bayar layin kana ta dawo ciki ta shige ɗakinta... Juyowa Amra ta yi ta dubi Aliyu ta ce" Yanzu wannan kake so ka kashe Yarinyar da take taimakon al'umma? To wannan kaɗan daga cikin alkhairanta. " Ajiyar zuciya Aliyu ya sauke ya ce" Yo haƙuri Yaya Amra na ɗauka itama haka take amma daga yau na dena bibiyar rayuwarta, kin san kuwa shekarar data wuce na firgita Yarinyar nan amma ta dake ta dinga yin addu'a, ganin haka sai na rabu da ita dan ta nemi tsari a wajan Allah ya kare ta daga duk abin da zai cutar da ita kana ta kwanta, amma kuma Yaya Amra haka za mu rabu da wannan ahalin bamu ɗauki fansa ba?" Dafa kafaɗarsa ta yi tana kallonsa cikin saisaita murya ta ce" Wa ya ce maka kyalesu za mu yi?Ai dole mu rama abin da suka mana ba fashi, ita ɗin ce dai ba za mu taɓa cutar da ita ba.." Jinjina kai ya yi cike da gamsuwa da maganarta ya yi gaba ta bisa a baya.. Fadila ta samu Daddy zaune a palo, zama ta yi tare da zamewa ta ɗaura kanta a cinyarshi cikin shagwaɓarta ta ce" Daddy kasan dai gobe ake yin birthday na ko?" Shafa kanta ya yi yana murmishi ya ce" Na sani sosai to kike so ki yi a taron naki?" "Daddy nifa a gida nake so mu yi shagalin birthday bana son zuwa hôtel wannan karon.. "Ok to shi kenan kinga gobe Mommyn ku za ta iso Ƙasar sai ku tarbeta ayi shagali sosai, amma ni zan ɗan je wani meeting da aka gayyaceni ƙarshe goma zna fita, idan na dawo da dare sai mu yi koda hirar dare ne." Tashi ta yi daga kanshi ta kai masa runguma tana dariya ta ce" Godiya nake Daddy naga ka mini transfer ɗin kuɗi zanje nida su Mufy mu sayo duk abin da ya kamata.." Murmishi kawai ya mata ta miƙe tabar wajan, babu jimawa ta fito cikin shigarta na riga da sket kayan sunbi jikinta da ƙyar take tafiya tana wani ɗaga hanci sama ta wuce... ************************* Babu inda su Amra suka nufa sai cikin wannan dutsen, wani babban gida ne ginin laka, wata ƙofa suka nufa sai gasu a wani babban palo daret wani ɗaki suka nufa, akan gado Amra ta aje Auta tana sauke numfashi ta juyo ta kalli Aliyu idanunta sun yi jajur ta ce" Aliyu je ka kawo mini ruwa." Da mamaki yake kallonta wai ruwa to me kuma Yaya Amra za ta yi da ruwa?" Ya faɗa a cikin ranshi. Tsam ta gano abin da yake tunani ta saki murmushi ta ce" Kaga ka fita ka yi abin da na umarce ka." Jinjina kai kawai ya yi ya fice daga cikin ɗakin..
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31