Chapter 29
Chapter 29
mata. A razane ta juyo jin wani irin ƙara kiiii, da gudu ta nufi wajan da taga mutane sun soma zuwa wajan tana isowa ta kwalla ƙara a matuƙar firgice ta ce" A a Khamiss! *Taku har kullum Maman Nusaiba ce* [14/12, 21:25] Umma Amjad: _*🧟♀️ALJANAR GIDANMU 🧟♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ بسم الله الرحمن الرحيم 1️⃣3️⃣ Mutanen dake gurin kowa salati yake sun kewaye Khamis dake gefen hanya kwance jini nata malala daga bakinsa da hancinsa har ma da gefen fuskarsa, fashewa da kuka Auta ta yi tana kutsa kanta cikin mutanen har ta iso gurin Khamis ta yi zaman 'yan bori tana taɓa hannunsa dake jumke rike da ledar ice cream, kallon mutanen ta yi tana kuka ta ce" Jama'a ku taimakeni ku kira mini Ambulance kar ya rasa ranshi don girman Allah." Wani daga cikin su ne ya yi kiran emergency call na police cikin sa'a aka ɗaga kiran ya yi saurin cewa" Hello taimakon gaggawa mota ta buge wani gashi nan a bakin titi ku yi sauri ku zo." Daga wayar aka tambayesa ina ne Unguwar ya faɗa musu kana ya kashe wayar tare da duban Auta ya ce" Yanzu za su zo." Jinjina masa kai kawai ta yi ta soma laliban jakarta taji bata nan, da sauri ta koma ta ɗauko har tuntube take za ta fadi Allah ya taimaketa bata faɗin ba ta iso cikin azama ta bude jakar hannunta na rawa ta ɗauko wayarta ta dannawa Mommynta kira , sai da ta gama ringing ba'a dauka ba zata kuma kira saiga Ambulance ta iso hakan ya sa ta miƙe tsaye tana kallon motar har suka yi packing suka fito, ɗaukan Khamis suka yi wanda yake tsakanin mutuwa da rayuwa suka sashi a mota. Da sauri Auta ta miƙe ta shiga motar Khamis taja ta bisu a baya hankali a tashe take driving tana kuka har suka iso Asibitin aka shiga dashi emergency room ita kuma ta tsaya a bakin ƙofar tana sharbar kuka. Tana nan zau ne taji wayar Khamis dake hannunta ta ɗauki ringing tabi wayar da kallo jikinta na rawa ganin sunan wanda yake kan screen ɗin wayar, hannunta na rawa ta soma ƙoƙarin ɗaga kiran sai dai kafin ta ɗaga kiran ya katse ta saki baki tana kallon wayar sai ga wani kiran an kuma yi cikin azama ta ɗaga tare da kara wayar a kunnenta ta yi shuru zuciyarta na bugawa hawaye na zarya kan kuncinta. "Hello my Son wai a ina kake haka tunfa ɗazu ake ta jiranka kai kaɗai muke jira ka zo muje kasuwa zaban kayan Afra na birthday ko lokacin bai zo ba ne? Wasu zafafan hawaye suka kuma bin kuncinta ta kai hannu ta goge baki ta buɗe da nufin magana amma ta taji maƙoshinta ya bushe, sake yin magana aka yi daga cikin wayar ciek da mamaki. "My Son wai ba ka jina ne ? A ina kake ka yi maza kazo bana son zuwa kasuwa da Yammaci fa kana jina iye? Wannan karon Auta fashewa da kuka ta yi cikin shashshekar kuka ta ce" Ammi Yaya Khamis n.. Da sauri ta katseta da cewa" Afra lafiya kike kuka?me ya faru da Khamis ɗin ina yake?" "Ammi mota ce ta bugeshi yanzu ma muna Asibiti Ammi ki zo please " Ta ƙarashe maganar cikin raunatacciyar murya.. Salati Ammi ke furtawa ta tambayi a wacce Asibiti ne ta sanar da ita kana ta kashe kiran, zama Auta ta yi zuciyarta na zafi ta rafka tagumi a sanyaye ta ce" Da nasan mota za ta buge da ban ce ina son wani abu ba." Kira ne ya shigo wayarta ganin Mommy ce ke kiran ta yi saurin ɗagawa tana jin muryar Mommy ta sa mata kuka tana cewa" Mommy Yaya Khamis mota ta bugeshi ya zan yi Mommy?" "Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Mommy ta furta da sauri ta ce ta mata kwatance ta yi mata ta kashe kiran.. Kusan a tare Mommy da Ammi duka iso Asibitin Auta na ganin Ammi ta isa gareta tare da faɗawa jikinta tana kuka marar sauti, bubbuga bayanta Ammi ke yi har suka zau na akan kujera ta ɗago ta ita cikin muryar rarrashi ta ce" Afra ki yi shuru mana kalli yadda idanunki suka kumbura. Ba kuka ya kamata ki masa ba addu'a kawai za ki masa." Jinjina kai ta yi ta kallo Mommy dake ɗayab gefenta ta ce" Mommy." Girgiza mata kai Mommy ta yi tana mata nuni da kar ta yi bata sake cewa komai ba Ammi ta kwantar da kanta a kan kafaɗarta. Sai da aka kwashi awa ɗaya a shigar da Khamis emergency kana aka buɗe ƙofar ɗakin, da sauri suka miƙe suna rige-rigen tambayar Doctor ɗin a tare suka ce" Doctor ya jikin nasa?" Kallonsu ya yi yana goge zufar data tsatstsafo masa a goshi kana ya mayar da glass ɗinsa ya ce" Ku biyoni Office." Ammi ta ce su zau na ta taje amma firr Auta ta ce itama zuwa za ta yi hakan ya sa Ammi kama hannunta suka nufi Office ɗin Doctor ita kuma Mommy ta zau na ta rafka tagumi tana jiran fitowarsu sai ga Mahaifin Khamis da Yayan shi sun iso, tambayarta suka yi ta nuna musu inda Ammi ta nufa suka wuce fuskokin su na bayyana tashin hankalin da suke ciki. Sun zau na kenan sai ga su Daddyn Khamis sun shigo suka samu guri suka zau na tare da bada hankalin su ga Doctor dan suji matsalar Khamis, sai da ya gama rubuce-rubucensa kana ya ɗago ya dubi su Ammi ya yi gyaran murya kana ya soma cewa "Gaskiya ɗanku ya naura arziki a yadda aka kawo mana shi ban taɓa tunanin za mu gama aikin nan rai baiyi halinsa ba, amma da yake Ubangiji shi ke yadda yaso da bawansa sai gashi ana gama masa dinki ya soma kiran sunan Afra." Ammi ta yi saurin cewa" Likita yanzu a wani hali yake ciki?" Jinjina kai ya yi kana aje barrow hannunsa ya ce" Am sorry Hajiya gaskiya da yaronku da wahala ya iya taka ƙafarsa, saboda ƙashin kwankwasonsa ya samu matsala mun masa duk wani gwaje-gwaje amma ko wani sakamako haka yake nuna mana ƙashin gurin ya tsage, sannan ya samu karaya a hannunsa na hagu haka ma gefen fuskarsa ya yi babban rauni mun yi masa dinki, alhamdulillahi ƙwaƙwalwar shi bata samu matsalar komai ba inda hali ya kamata ku fitar dashi waje ayi masa aiki, dan gaskiya yana buƙatar aikin gaugawa a kwankwason shi.. Daddyn Khamis ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" To Doctor mun gode in sha Allah yau ɗin nan zan nema mana ticket ko zuwa gobe ne mu sai mu tafi." Doctor ya dubi Daddyn Khamis ciki da tausayi ya ce" Zan haɗaku da wani abokina da yake Ƙasar Paris za ku iya can ko kuma ku tafi Ƙasar Saudiya ina ganin ma nan zaifi." Daddy ya ce" To Saudiyyar ma za tafi mun gode sosai yanzu za mu iya ganinsa?" "E za ku iya ganinsa amma ban da rubutu dayawa. Godiya suka kuma masa kana suka fito zuwa ɗakin, Mommy na ganin su ta tambayesu fatan ba matsala dai, Ammi ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31