Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shi dai inba bacci ba babu abin da yake hana shi jin kiɗa sallar ma sai yaga dama yake, Jinjina kai ta yi tare da kawar da kanta gefe tana kallon bakin hanya. Suna zuwa daidai inda ta haɗu da Amra cikin sauri ta ce" Yaya please tsaya inaso mu gaisa da Ƙawata." Jan birki ya yi ya tsaya, kallon gurin ya yi yaga ba kowa ya dubi Auta ya ce" To ina ita Ƙawar taki take?" Murmishi ta yi ta ce" Ka bari za ka ganta ina so na bata abincin nan ne muje ka rakani." Ba muso Sudas ya buɗe musu suka fita ita dashi, can tsallaken hanya ta yi ta waiga ko ina bata ganta ba, har ta haƙura za ta juyo taji muryar Amra na cewa" Ƙawata kin ganni nan." Da sauri ta juyo ta ganta a bayanta tana nufota, kafin ta iso itama ta nufeta suka rungume suna cikin nuna farincikin ganin juna. "Amra kin tashi lafiya ya jikin Innar yanzu?" "Lafiya lau Auta Inna ta samu sauƙi na barota a gida, ba ki ga nima na yi wanka ba na canja kaya kudin da ki ka bamu jiya na sayo magani sauran na sayo kaya 'yan gwanjo kala biyu, shi ne na saka ɗaya in mun haɗu na nuna miki... Tausayinta ne ya rufe Auta har bata san lokacin da hawaye ya zubo mata ba,tana cewa a ranta. " Allah sarki Amra ashe kayan sakawar ma bata da shi, kalli kanta babu alamar gyara, in sha Allah zan taimakeki matsawar ina da shi.. "Auta ya ki ka tsaya zo mu tafi mana" Sudas ya faɗa sai idanunsa ya sauka akan Amra da ta kafe Auta da idanunta farare tass. Murmishi ya saki yana binta da wani irin kallo yana lashe lips ɗinsa na ƙasa sannan ya ce" A a Auta wannan Ƙawar taki yaya sunanta?" Murmushi ta yi ta kamo hannun Amra cikin jin daɗin bai nuna kyama akan Ƙawartata ba ta ce" Yaya sunanta Amra itace Ƙawata" Ta faɗa tana sauke schoolbag ɗinta ta fito da ledar dake ciki, miƙa mata ta yi tana murmishi ta ce" Amra gashi ki kaiwa Inna kuci gobe zan kawo miki wasu daga cikin kayana." Goge hawaye Amra ta yi ta amsa cikin zazzakar muryarta ta ce" Ƙawata bani da bakin miki godiya kina da kirki, ke ɗin mai zuciyar salihan mutane ce Ubangiji ya miki albarka." "Babu komai Amra karki damu Allah zai fitar daku daga ciki halin da kuke... "Am na ce ba. "Ka ce mai Yaya? "Na ce ki shiga mota ni zan rakata da kayan kar ta ɓata kayan jikinta kinga ta yi wanka ta yi kyau gwanin birgewa.. Murmushi Auta ta yi ta ɗagawa Amra hannu ta nufi mota ta shiga ta rufe. Kanta a ƙasa bata ɗago ba tana jiran ya mata magana. Baby gaskiya fa kin haɗu sosai kinga kuwa yadda kike da kyau? Muje can gangaran muyi magana kar lokaci ya wuce" Ya faɗa yana kama hannunta... Da kallo tabi hannun nashi tana ji yajata suka nufi can ganganre.. Suna zuwa ya zaunar da ita akan wani ice ya zau na shi ma sai murmushi yake saki. Ita dai Amra na takure zuwa yanzu tsoro ya kama ta ganin yana matsowa kusa da ita, bakinta na rawa ta ce" Yaya meye haka kake yi?" "Haba my Baby babu wani abu da zan yi inda in taɓa nan inji" Ya faɗa yana damƙar na fulaninta.. Waiyo Allah! Inna z.... *Ku hanzarta ku biya naku kuɗin karatun akan farashi mai sauƙi N300 kacal* _*Taku har kullum Iyar Nusy mai abin mamaki inji kabeji😂*_ [26/11, 18:14] Umma Amjad: _*🧟‍♀️ALJANAR GIDANMU 🧟‍♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum ( Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ *WhatsApp number +966599791573* بسم الله الرحمن الرحيم 0️⃣3️⃣ Waiyo Allah! Inna zai taɓa mini jiki" Ta faɗa cikin tsananin tashi hankali jikinta na rawa karr³ . Sudas da yake ƙoƙarin haɗa Amra da jikin shi ya ɗago idanun shi kamar wani ɗan meye ya ce" Baby ki tsaya mana babu abin da zan miki fa, zan kaiki kasuwa da kaina na saya miki kayan sawa masu kyau wanda za su yiwa farar fatarki kyau sosai, ki yarda dani zan baki kudi mai yawa sannan zan kai Mamanki asibiti a mata magani ta samu lafiya, duk abin da kikeso zan miki kuma zan aureki ki dawo gidanmu da za ma kinga sai kuci gaba da za ma da Auta guri ɗaya" Ya ƙarashe maganar yana riƙe hannunta cikin nashi." "A a nidai ka rabu dani zan koma gida ni ba ƴar iska ba ce, ai sai marar tarbiya yake irin abin da kake son mini bana so in ba ka rabu dani ba zan faɗawa Auta komai kuma na rabu da ita har abada ba za ta sake ganina ba, kai kuma ka fita hanyata ko na maka ihun kwarto a nan" Ta faɗa tana cuno baki gaba.. Murmushi ya saki yana bin bakin nata da kallo, a ranshi yana cewa" Hmm yarinya sai shegen kyau kamar ita ta yi kanta ga daɗin murya, kai dole ma na kaiki wani gurin in ban samu dama ba na aureki ki dawo karkashina.." "Ka sake mini hannu na tafi" Amra ta faɗa tana mintsinin hannun nashi.. Ƙin sakin mata hannun ya yi, ran Amra ya yi matuƙar ɓaci fuskar nan a haɗe, cikin kakkausar murya ta ce" Ka sakeni na ce! Ai a tsorace ya sakar mata hannun yana ja da baya.. "Ashe kaima kamar ubanka kake? Baka da imani kaji kunya dai, kenan dan ni bani da gatan kowa sai ka nemi ka lalata mini rayuwa? Yanzu in Auta ka gani wani na ƙoƙarin keta mata haddi za kaji daɗi? Ka kula kar ka bari na sauke fushina a kanka banza shashasha kawai" Tana gama faɗin haka ta fisge ledar dake hannun shi ta mishi wata irin bangaza ta wuce fuuu.. Da ƙyar Sudas ya miƙe yana mamakin yadda ƙaramar yarinya take da karfi kamar wata inkarman Doki, juyowa ya yi dan yaga ina ta yi yaga wayam ba kowa , mamaki ya kuma rufe shi ya duba ko ina bai ga inda ta yi ba, haka dai ya haƙura ya fito daga bayan dutsen ya nufo inda ya yi parking motarsa. Kicibus suka yi shi da Auta, ɗago kai ya yi yana kallonta yaga ta cika fam sai hura hanci sama take tana riƙe da ƙugunta. "Haba Yaya tsakani da Allah kai da na ce maka na yi lettin zuwa school ka yi kazo mu tafi amma kawai shi kenan sai ka yi zaman ka, ko har gidansu ka kaita ne?" Ta faɗa ranta a ɓace.. "Yi haƙuri" Kawai abin da ya iya ce mata ya kama hannunta suka koma cikin motar, ko a hanya tunanin irin tsawar da Amra ta masa yake yi har ya kai Auta ya sauke ta... Daddy da Fadila sun fito za su shiga mota sai ga mai gadi ya iso gurinsu jikin shi na rawa ya durƙusa.. "Kai kuma tsohon najadu lafiya ka wani zuba mana idanu" Cewar Fadila tana mishi kallon kyama da tsana. Sunkuyar da kai Maigadi ya yi yana tunanin rashin kunya da rashin tarbiya irin na Fadila, yarinyar da ya yi

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});