Chapter 4
Chapter 4
ta kai sujjada tana faɗin" Subha rabbiyal a'ala.. "Kan buhun uban can! Ta faɗa tana ɗaura hannunta kan hannun ƙofar ɗakin. Auta na gama yin tahiya ta salamce ta ɗaga hannayenta sama ta soma faɗin" Ya Ubangiji ka shirya Daddy da Anty Fadila da Yaya Sudas da Yaya Sauban da ma dukkan wanda suka kauce hanya, ya Allah ka dawo mini da Mommyna lafiya ka tsare mini ita a duk inda ta nufa, Allah ka ƙara mata lafiya mai amfani, Allah ka aurar da Anty Fadila mu huta da jin kaɗe-kaɗe a gidanmu" Tana kaiwa nan ta karanto Fatiha ta shafa tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya... "Iye! Auta ni kike cewa na yi aure ku huta dani ko? Ba shakka mandiya sannu Hajiya uwar Daddy , kuma yaushe ma ki ka shigo ɗaki har ki ka yi alwala ki ka yi salla? Ba a palo na baroki ba kina zau ne za ki kunne TV?" Fadila ta ƙarashe maganar zuciyarta na harbawa da sauri-sauri kamar za ta faso ƙirjinta ta fito saboda tsananin tsoro da tashi hankali, yanzu ji take tsoronta ya ƙara lumkuwa akan na ɗazu.. Sake da baki Auta ke kallon Fadila dan ita a iya saninta ta kwanta a kan gado bata tashi ba in ba yanzu ba data farka dan ta gabatar da sallar daren data saba yi, miƙewa ta yi ta cire hijabinta ta aje a gefe ta dawo bakin gado ta zau na, addu'a ta yi ta shafa a jikinta kana ta gyara ta kwanta sai a lokacin ta kai dubanta ga Fadila da ta yi tsaye tana zare idanu... "Da alama dai yau Anty kin Sha kodin ko wiwi, ina ha dai ko jimawar can kin kalli film ɗin abin tsoro shi ya sa ki ka kasa bacci har kike gani kamar ina miki gizo, to ni yaushe ma na fita har naje palo na kunna kallo a cikin wannan talatainin daren? Ko kuma kin zo ki zalinceni kamar yadda ki ka saba ne?" Tana gama faɗin haka ta juya ta ɗauko ƴar Teddynta ta rungume tana shafa kanta kamar ta rungume mutum. "Baby gobe Daddy zai kaimu kasuwa zan sayo miki blanket mai laushi saboda da sanyi ya kusa zuwa" Ta faɗa tana ƙara rungume ƴar Teddyn.. Fadila ganin fa in ta tsaya jin tsoro sai ta haukatar da kanta ta kawo wata kundumemiyar ashar ta yiwa Auta sannan ta banko mata ƙofar tabar wajan.. Murmushi Auta ta yi ta ce" Allah ya shirya ki." A guje Fadila ta iso ɗakinta ta rufo ƙofar har da murda key ta zau na a gado jagwab, dafe kanta ta yi da yake sara mata tana tunano abubuwan data gani ɗazu, tunani kala-kala take a zuciyarta tsoro na ƙara shigarta, da sauri ta tashi ta isa jikin drower ɗinta ta buɗe ta fito da schoolbag ɗinta, zarge zip ɗin ta yi ta fito da wata leda baƙa ta mayar inda ta ɗauko jakar ta dawo bakin gado, buɗewa ta yi ta fito da wasu kwayoyin magani bata tsaya duba ta ga ko nawa ba ne ta afka a baki tare da binsu da ruwa ta hadiye, wata kwalba ta kuma fiddowa ta buɗe ta ɗaga ta sama ta shaye tass sannan ta ɗauke daga bakinta, ajiyar zuciya ta shiga saukewa tuni ta soma ganin bibiyu ba jimawa tà zube akan gado bacci ya yi gaba da ita.... Washe gari Auta cikin hanzari ta fito daga ɗakinta dan ta makara zuwa school, koda ta sauko su Daddy ta samo zau ne suna karyawa. "Good morning Daddy " Ta faɗa tana za ma akan kujerar dake kusa da Sauban ta ɗaura masa ƴar Teddynta akan cinyarsa. "Morning my baby love da fatan kin tashi lafiya?" Murmishi ta yi tana juya cokalin dake cikin indomie dake gabanta sai kuma ta yamutsa fuskar ta ce" Daddy nifa bana son wannan abincin a soya mini kwai guda shida a haɗa mini ruwan zafi a flas da suga da laptop in na isa school sai na ci, na makara yanzu haka tsoro nake a zaneni malamin yau bashi da mutumci, yawwa na manta Daddy a haɗa mini da apple guda uku" Ta ƙarashe maganar tana hararar Sauban da ya saki baki yana kallonta jin yadda take zano abubuwa kamar ba ita kaɗai za ta zuba a cikinta ba.. " Tsuww Wallahi Daddy yarinyar nan inaga Mommy ta ɓata ta, jiya fa haka ta nufi ɗakina tana ta buga mini ƙofa, wai ma kusan me?" Ta faɗa ranta a matuƙar ɓace.. Dariya Sudas ya yi ya ce" Kai Fadila banda ƙarya dai yaushe Auta har za ta iya zuwa gurinki da dare bayan ba daɗi take ji a gurinki ba? Kar ki mata sharri malama ba sai kin ce komai ba mun san duk ƙarya ce za ki faɗa." Cokalin dake hannunta ta wurga mata cikin sa'a ya cafe yana dariya. Daddy ya kallesu yana murmishi ya ce" Kunga ai da dai mun saurari abin da za ta faɗa mana, ku ka sani ko sun shirya ita da Auta." Sauban da yake dariya ya ce" To ai shi kenan sweetheart rabu da Sudas ni faɗa mini mai ku ka shuka jiya ke da Autar?" "Yawwa Yaya Sauban dama na san kai kafi sona fiye da wannan ɗan rainin hankalin, in faɗa maka jiya Auta t... Bata ƙarasa ba taga Auta na yi mata wata irin harara idanunta sun soma canja kala, ai tuni ta kame bakinta ta yi saurin sunkuyar da idanunta, amma duk da haka bakinta bai mutum ba ta shiga cewa" Za ki ci uwarki yarinya da kin dawo daga school yau sai kin wanke mini kayana a gidan nan... Banza ta mata kamar bata ji abin da take faɗa ba, tana nan zau ne Kande mai aikinsu ta haɗo mata duk abin da ta lissafo ta kawo mata a cikin leda, amsa ta yi ta mata godiya sannan ta miƙe ta goya schoolbag ɗinta ta ce" Bye Daddy sai na dawo. " Da sauri Sudas ya miƙe ya ce" tsaya Auta ni zan kaiki da kaina yau tun da bani da abin da zan yi." Daɗi sosai ya kama Auta ta yi tsalle ta rungume shi tana masa godiya kana suka juya za su fita, tsinkayo muryar Fadila suka yi tana faɗin" Yaya Sudas zan biku ku saukeni." "Wani dan iskan ne zai kaiki iye? Nine zan yarda na daukeki a motata ki dumama mini ita da warin dauɗa? Karma ki biyomu dan ko kin zo ma Wallahi sai na miki wankan hayaƙi a wannan fuskar taki mai kama data jakuna" Yana gama faɗin haka ya wuce abin shi ... "Hahaha kai Alkur'an is very good Sudas ka birgeni" Cewar Sauban yana barin palon shi ma. Kuka Fadila tasa tana kallon Daddy, lallaɓa ta ya yi ta kyale ya ce su fita tare sai ya ajeta a school ɗin nasu, to ta ce amma ranta a matuƙar ɓace yake saboda abin da Sudas ya faɗa mata, in kuma ta tuna irin kallon Auta ta mata sai taji tsoro ya kama ta... Suna fita daret hanyar school ɗin su Auta Sudas ya nufa, kiɗa ya kunna yana bin waƙar. Tagumi Auta ta yi tana binsa da kallo, wato
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31