Chapter 22
Chapter 22
ɗan adam, Allah ya shiryeka" Tana gama faɗin haka ta kashe wayar saboda jaririyar na kuka ta mayar da ita ta ci gaba da shayar da ɗiyarta, Allah ya rabani da wannan ƙaddara" Ta faɗa tana goge hawaye.." Iye! Lalle Hafsat wuyanki ya isa yanka, wato ni kike yabawa magana? Zan yi maganinki. Yana zau ne yana kallo aka kira Magariba aka yi salla bai motsa ba aka kira Isha'i nan ma bai tashi ba yana kallon wani Indian film.. Sallama yaji ana yi a ƙofar shigowa, tsaki yaja ya miƙe ya nufi ƙofar yana faɗin" Waye haka da daren nan ya zo muni gida yawo, to inma neman Hafsat ku ka zo bata nan tan can daga gantalin ta wuce gidansu acan ta haihu." Buɗe ƙofar ya yi ya leƙo yaga ba kowa wayam, tsaki ya kuma yi ya rufe kofar ya dawo ya ci gaba da kallo.. Zubar ruwa yaji daga kitchen abin ya bashi mamaki ya miƙe ya nufo kitchen ɗin, rufe pampon ya yi ya dawo ya zau na, faɗuwar kanuna ya dinga ji ta ko ina sai kuam dariya mai haɗe da kuka yake ji a palon, a 380 ya watso da gudu ya nufi ɗaki, kafin ya isa ƙofar ta rufe ji kake bamm... Ƙaran tafiya ya dinga ji a bayanshi ya yi saurin juyowa, zabura ya yi ya kurma ihu ganin wani ƙaton kare baƙi narkeke da manyan manyan idanun shi jajaye ya nufo shi, ban san lokacin da ya saki futsari ba ya yi baya luuuu..... _*Taku har kullum Maman Nusaiba*_ [06/12, 20:42] Umma Amjad: _*🧟♀️ALJANAR GIDANMU 🧟♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ *بسم الله الرحمن الرحيم* 1️⃣0️⃣ Wani irin kurnani Karen ya dinga yi yana kusanto mijin Hafsat dake sheme a ƙasa ya yi warwas, yana ƙarasowa ya rikide ya dawo wata kyakywar matashiyar budurwa mai tsananin kyau kamar ita ta yi kanta. Dariya ta dinga yi wadda duk palon ya ɗauki amsakowar muryarta, hannu ta miƙa ta ɗamko wuyan mijin Hafsat tare da zabga masa lafiyayyen mari wanda ya yi sanadiyar dawowar numfashinsa daga suma. "Allahu akbar! Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Na shiga uku ku gafarceni je. "In ka sake magana saina datse maka harshenka mugu azzalumi marar imani, kai har kana da bakin yin magana dama kasan Allah kenan? Kasan da ubangijin da ya halicceka ashe? Kenan kana tunawa da wanda ya halittoka amma ka kasa bin dokokinsa? "Waiyo Allah! Na tuba nabi Allah na biku a rufa mini asiri please ba zan sake saɓawa Ubangiji na ba, na muku alƙawarin dena komai karku kasheni zan yi duk abin da kuka buƙata koma mene ne shi" Ya ƙarashe maganar yana zaro idanu waje kamar za su faɗo.. Hahahaha! Kowa ya tuba da wuya ba lada" Ta faɗa tana nuna shi da hannunta wanda yake dauke da zaƙo-zaƙon faracuna masu kaifi. Kwalalo idanu ya yi ganin hannuwanta na yin tsawo suna neman rufe mata fuska, a kidime ya ce" Ki taimaka ki barni da raina Mama karki kasheni banga ba matata Hafsatu mai hankali matar aljana. " A fusace ta kai masa naushi a gefen fuska, ihu ya kurma yana sakin zawo palon ya cika da tsami, hannunta ta ɗaga sama sai ga wata ƙwarya mai dauke da ruwa a cikinta yana turiri dariya ta shiga yi tana karkato ƙwaryar akan shi. "N...Na... Natuba Mama ki taimaka karki kasheni zan miki d.. Bai ƙarasa ba ruwa ya soma kwarara tun daga kanshi har ƙasa, wani kalar azababben zafi yaji wanda yake iya cewa kamar fatar jikinsa tana ɗayewa, kururuwa yake yana birgima yana kiranta da Mama ita kuma tana dariya duk inda ya juya yana neman guduwa sai ya ganta a gaban shi ta bayyana, haka ta dinga zuba masa ruwan yana kurma ihu har ruwan ƙwaryar ya ƙare kana ƙwaryar ta ɓace daga hannunta.. Tsawa ta daka masa har sai da ya kuma sakin futsari a karo na barkatai. "Zau na a nan ɗan iska marar mutumci! Yadda ta yi maganar ya kuma sa shi a duniyar tsoro mai tsanani, jikin shi na rawa ya zau na yana ƙanƙame jikin shi. Wani irin kallo ta watsa masa kana ta ce" Kai! Ya sunanka?" Baki na rawa ya ce" Sus... Suna. Tsawa ta kuma daka masa har sai da ya wutsila ya kifa zai faɗa kan wani ƙaton madubi tasa ƙafa ta kai mata masga a gadon baya ba shiri ya gyara zamansa ram. "Ina jikin maza ya sunan ka? "Mama sunana Shu'aibu ne matata kuma sunanta Hafsat.. Jinjina kai ta yi ta ce" Mugu azzalumi matar taka ta kiraka a waya amma kaƙi ɗauka, bayan ka kira ma sai kawai ka yi ta faɗa mata magana marar daɗi dan ka rainata ko?" Da sauri ya ce" Wallahi Mama bazan sake ɓata mata rai ba na miki alƙawari gobe ma zanje gidan nasu da safe na dawo da ita ki yi haƙuri.. "Karka sake ce mini Mama. " To ba zan sake ba, kuma na.. Ji ya yi shuru ya yi saurin ɗago kansa yana bin inda ta zau na da kallo, wayam ba kowa a gurin ya yi saurin tashi yana waige waige , kafin ya yi wani motsi yaji TV na magana ya zabura ya kalli TV . Wani ƙungurmin daji ya gani a TV babu kowa sai bishiyoyi, wata yarinya ya gani zau ne a bakin wata rijiya sake tsakiyar dajin a cikin wani fili, kwalalo idanu ya yi yana ja da baya zai matsa yaga yarinyar ta ɗago da kanta sama tare da wage bakinta wani ƙatoton maciji ya fito daga bakinta ya dabaibayeta... Innalillahi! Ya faɗa yana rintse idanu. Hannu ta miƙo sai gashi a waje ta kuma ɗayan shima ya fito daga TV, kamar wata kifi haka ta fito daga jikin TV bakinta jini na malala tana wani irin kurgunki, wajan Shu'aibu ta nufo tare da macijiyar a hannnunta sai huci take.. Numfashin Shu'aibu ne ya ɗauke na wucin gadi yana ja da baya yana kuka tare da rokonta.. Tana isowa ta ɗaga macijin sama ta dawo kare ta jefawa Shu'aibu, Karen nan ya shiga yagon Shu'aibu yana keta masa riga ita kuma tana dariya ta koma gefe.. "Waiyo!Waiyo! Ki taimaka karki kasheni" Haka yake faɗa. Sai da karen nan ya masa jina-jina duk ya yage mata jiki kana ya ɓace bat. Da ƙyar Shu'aibu ke ɗaga hannun shi saboda azaba nadama kuwa ya yita tafi cikin kwando yana kiran sunan mamansa da Hafsat. Sake bayyana ta yi sai ta dawo a suffar namiji ƙaton gaske baƙi hannun shi ɗauke da bulala, ja baya Shu'aibu yake har ya ƙure jikin bango ya takure yana rufe fuskar shi da hannu, dukan shi ƙaton nan ya shiga yi baƙi ba gani shi kuma yana ihun neman ceto . Sai da ya farfasa masa jiki kana ya barshi ya kuma ɗauke ruwan nan ya dinga zuba masa a jikinsa, wuliliya Shu'aibu ke yi yana kurma ihu duk inda ruwan nan ya zubo masa ji yake gara ma ayi ta dukanshi zaifi da ruwan nan mai zafi.. Sai da ya jera suma a jere tafi goma da ya suma za'a dinga zane shi har sai ya dawo daga sumar, ranar dai Shu'aibu ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31