Chapter 23
Chapter 23
bambance tsakanin aya da tsakuwa.... _________________________ Ihu ne yake tashi a cikin palon tare da kiɗa an ƙure sautin wakar, 'yan mata da samari suna ta tikar rawa wasu a zau ne wasu kuma na gefe.. Hon ake yi Maigadi ya fita a guje ya buɗe get jikinsa na rawa ya dinga faɗin" Barka da zuwa Hajiya sannu." Murmishi Mommy ta sakar masa kana ta fito cikin takunta irin na manyan hajiyoyi ta iso kusa da shi cikin sanyin murya ta ce" Baba sannu da gida, wannan kiɗan da yake tashi duk a gidan ne?" "Kwarai ma kuwa Hajiya ai in faɗa miki Fadila ce tare da abokanta suka shigo wai ta ce yau take yin birthday. Jinjina kai ta yi ranta a matuƙar ɓace ta wuce ciki tana cewa" Na gode Baba zan yi maganin ƴar iska." Ko da ta shiga ba wanda yaji shugowarta, sosai ta kamu da tsananin mamaki da al'ajabi ganin Fadila tasha ado ta saka riga bakin guiwa wadda da ita da babu duk ɗaya ne, dan kana kallonta za ka hango pant ɗinta ta bra ɗinta wadda itama brar kusan na fulaninta rabi a waje suke. Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Ta faɗa jikinta na ɓari, lalle abin gaba yake wato iskancin na Fadila ya wuce inda take tunani, wai yau ƴarta ce take gani namiji ya nanike mata yana bata cake a baki itama tana bashi? Kai wannan wani irin zamani ne Allah ya kawo mu ni Azima ?" Ta faɗa a bayyane. Da sauri ta isa gurin speaker ta cire soket ɗin saboda tsananin ɓacin rai har wani ɗaci take jin bakinta na mata.. Fadila dake gaban saurayinta jin an kashe kiɗan ta ce" Mufy bana son iskanci fa uban wa ya ce ki kashe mana muna cikin nishaɗin mu?" "Ubaki ne ya sa banza shashasha sakarya, ku kuma kafin na ƙirga uku ku ɓaci mini da gani a cikin palo ko kuma yanzu na sa a ɗaure mini ku, shashashun banza ƙattai da ku ko kunya bakwa ji ku shigo gidan aure gidan sunna ku kunna kiɗa, har da samun guri kuka zau na ku gaku 'yan zamani ko? Maza na ce kafin na juyo naga kun tafi!" Ta faɗa cikin matuƙar ɓacin rai yau ji take kamar ta shake Fadila yarinya bata san komai sai kiɗa da wulaƙanta mutane.. Fadila ta ɓata fuska tana kumbura baki tana magana ƙasa ƙasa cikin jin haushin an hana su jin daɗi, a masifance ta ce" Baby kar ku tafi ku tsaya ai sai da na faɗawa Daddyna zan kawo ku mu yi shagalin birthday na a nan kana mu ka zo, amma shi ne za ta wani hanamu kar wanda ya tafi." Sake da baki Mommy take kallonta dama tasan za a runa wai an saci zanan mahaukaciya, juyowa ta yi ta kuma musu gargadi tare da ɗaukan wayarta za ta kira police, amma ga mamakin ta ba wanda ya motsa sai ma Fadila data miƙe ta isa gurin speaker ta kunna tare da ƙure sauti ta iso gaban saurayinta ta kamo hannunsa suka soma takawa.. Bata ƙara tankawa ba ta wuce sama ranta ba daɗi, daret ɗakin Auta ta nufa tare da buɗewa tana faɗin" Autar Mommy kina ina ne?" Can ta hangota a tsakiyar makeken royal ɗin gadonta ta rufe kanta da pilo ta takure a guri ɗaya, da sauri ta isa gareta tare da ɗago ta ta ce" Auta lafiya dai kike? Me ya sameki? Yunwa kike ji?" Duk ta jero mata tambayoyi a jere tana ɗago da fuskarta." Zaro idanu ta yi tare da cewa" Subhanallah me zan gani haka Auta? Wannan ɗin mene ne a fuskarki?" Auta ta fashe da kuka jin muryar mahaifiyarta cikin shashshekar kuka ta ce" Mommy ba Anty Fadila ba ce ta mareni ita da Ƙawarta wai dan na dawo daga school na ce ta zuba mini abinci Kande bata nan taje kasuwa, shi ne fa Mommy ta mareni itama Ƙawarta ta mareni" Ta ƙarashe maganar tana kuka sosai.. Lahaula wala kuwwata illah billah! Wai mai Fadila take son za ma ne ? Ki yi haƙuri kinji da Daddyn ki ya zo ki faɗa masa komai zai mata hukunci, kwanta naje na dauko miki abincin. "Na koshi bana so" Ta faɗa da wata kalar murya abin da ya sa Mommy saurin kallonta." "To shi kenan koma ki kwanta ni ma zan je na kulle ɗakina wannan kiɗan ya yi yawa kuma bani da damar hanata tun da ubanta ya daure mata gindi. Fita ta yi tare da janyo mata ƙofar ta wuce nata ɗakin ta kulle... Su Fadila har ƙarfe tara na dare ba su tafi ba, ko da aka soma kiran sallar Magariba ba wanda ya kashe waƙar bare ma a kai ga yin salla, haka ma Isha'i duk suna rawa aka yi salla biyu.. Sai da su ka gaji dan kansu kana suka kashe kayan kiɗan, Fadila tasa Kande ta dafa mu su abinci kowa ya ci duk sun yi kaca-kaca da palon.. Suna zau ne suna kallo sai ga Daddy ya shigo gidan, da gudu Fadila ta isa gareshi ta faɗa jikinsa tana masa oyoyo. Murmishi ya yi cikin jin daɗi bai ma damu da shigar da ta yi ba ya ce" Daughter har an gama shagalin ba ku jirani ba?" Murmishi ta yi kana ta kama hannun shi suka ƙaraso ta gabatar mi shi da kowanne daga cikin friend nata, shi ko sai washe baki yake yana cewa" Wow so beautiful." Mommy ce ta fito cikin tsananin mamaki take kallonsu ganin ba su tafi ba, Hmm Allah dai ya shirya mana" Ta faɗa tare da kallon Daddy a dakile ta ce" Sannu da zuwa Daddyn su." Ido ɗaya ya kashe mata tare da ɗage mata gira ɗaya ya ce" Darling yau ba ko oyoyo ma na dawo ina son na ganku, ina Auta take?" Wani haushi ne ya turnike Mommy wai ta masa oyoyo a gaban futsararrun yaran nan dan shi ma ya zama sorry kawai, kwafa ta yi ta ce" Su 'yan birthday ɗin ko a nan za su kwana ne?" "E a nan za su kwana wani abu ne in sun kwana a nan ɗin?" Daddy ya faɗa yana sakin murmishi tare da mayar da kallon shi ga TV. Auta ce ta fito tana murza idanu tare da cewa" Mommyna Daddyn bai dawo ba ne?" Ta faɗa da wata iriyar murya wadda duk 'yan palon sai da suka juya suna kallon Auta.. "A a Auta kinfi na fari iye dama kina ɗaki shi ne ba ki ji na dawo ba?" Cewar Daddy yana miƙa mata hannu." Da hanzari ta iso tare da hayewa kan cinyar Daddy tana murmishi bata sake cewa komai ba illa haɗe rai da ta yi tana kallon kowannen su tana ɓata fuska. Daddy ka ce su tashi a palon nan a gyara kalli fa yadda suka masa ko tausayin Kande basa yi, yau fa sai da na tayata aiki kana ta gama baka ga yadda take shan wahala ba Daddy, ina so dama a ƙara mata 30 a cikin albashinta ya za ma dubu 40 saboda aikin gidan nan ya mata yawa sosai kaji Daddy" Ta faɗa tana mintsinin Mufy dake gefen Daddy ta ɗaya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31