Chapter 27
Chapter 27
waye ya masa magana mai amo irin haka, hango wasu dogayen halittu ya yi masu kama da mutane sai dai ba'a ganin fuskarsu sai dai hannu shi ma hannun irin na biri duk gashi ya yanyame ga facuna masu tsowo da tsini, kwalalo idanu ya yi na ganin wannan halittun wanda shi dai a iya rayuwar shi bai taɓa ji ko a hikaya àn bada labarin irin wannan halittun ba, ɗaya daga cikinsu ya yo gaba hannnun shi ɗauke da jariri ya miƙawa Doctor yana faɗin" Gashi ka duba mini shi bashi da lafiya shi ya sa muka kawo shi." A rikice take kallon jaririn mai kama da gwaggwon biri yana watsu masa harara tare da zaro idanunsa wanda suke jajaye manya-manya babu ƙyan gani. "Maza amshi ka duba shi na ce za mu wuce." Yaji wannan mai ɗauke da jaririn ya kuma faɗa yana matsowa kusa dashi, ai kuwa Doctor ya kurma ihu yana neman inda zai ɓoye kamar zai tsaga bango ya shige ciki sai ƙara mannewa ya yi ya haɗa zufa sharkaf, futsarin da ýake ji tun a hanya ban san lokacin da ya saki futsarin ba yana ƙyarma kamar mai farfaɗiya, ɗauko hannun shi aka yi tare da murdawa ya bada sautin ƙararassss! Wani kalar ƙaran azaba Doctor ya saki yana huci fat! fat! fat! Tamkar numfashinsa na barazanar rabuwa da gangar jikinsa saboda tsananin azaba. Kai! Aka faɗa har sai da ya yi wani kalar zabura yana ja da baya bakinsa na rawa ya soma cewa" N...Ni ..Nifa ba Likita ba ne ku gafarc.. Bai ƙarasa ba jin saukar wani abu mai mugun nauyi akan gadon bayan shi kamar an daura masa buhun sumintin buhu uku da ƙyar yake iya fitar numfashi. Jaririn aka kuma miƙo masa aka ce masa ya duba lafiyarsa bashi da lafiya a wannan karon Doctor kasa magana ya yi saboda nauyin da aka ɗaura masa a baya sosai nauyin ke ratsa masa cikin jikinsa, wani kalar hayaƙi jaririn da ake miƙo masa ya hurawa Doctor nan da nan hayaƙin ya mayar da fuskarsa baƙa kamar an shafa gawayi ko kuma ɓakin panti a fuskar, ihu yake yana neman taimako sai kira sunan mamansa yake har da 'yan'uwansa gabaki ɗaya a wannan lokacin babu sunan wanda bai kira ba haka aka dinga gana masa azaba daga an masa wannan in ya soma bada haƙuri sai a kuma canja masa kalar azaba a masa wata daban, wani nauyi aka kai masa a saitin ƙirji sai ga Doctor ya yi can warwas ya sume ai kuwa aka kuma masa wani dukan sai gashi ya farfaɗo yana zabga ihu.. Buɗe idanunsa ya yi yai arba da wani narkeken Jaki baƙi ya tunkaro shi tuni Doctor ya kuma sakin futsari yana zaro idanu ganin Jakin nan na ƙoƙarin isowa gareshi jikinsa na rawa, mari aka sauke masa ya saki ihu cikin wata irin murya aka daka masa tsawa... "Yiwa mutane shuru mugu azzalumi marar imani. Yaji an furta a tsawace ana ƙara kai masa mari zazzafa mai shiga jiki, jikinsa ne ya bada kululuuu sai zawo haɗe da futsari a karo na barkatai dariya aka ɗauka kana aka soma cewa" Kai har kana da imani ko tausayin da za a tausayawa maka ne? Ko kana taimakon al'ummarka ne a yayinda suke neman taimakonka da har wani zai taimaka maka? Mara mutumci.. Ku yi haƙuri zan gyara halina ba zan sake ƙin taimakawa al'ummata ba kar ku kasheni na muku alƙawarin canja halayena daga yanzu" Ya ƙarashe maganar tare da haɗe hannayensa yana dan ja da baya daga cikim zawon da futsarin da ya yi zaman 'yan bori a cikinsa hatta kayan jikin ya yi sharkaf da ruwn zawon kuɗaje na binsa yooo tamkar an yi sabon yankan rago a mayanka ana feɗe shi." Dariya aka kuma kana yaji ana cewa" ai yadda kake mugu ba wanda zai ji tausayinka dan haka dole ne mu daukarwa bil'adama da 'yan'uwanmu fansar cutarwar da kake musu ba dare ba rana, a matsayinka likita wanda za a sameka da tausayi da jin ƙai na duk wanda ya zo gareka ka duba lafiyarsa, amma sai dai kash sai ka kasance macuci azzalumi mai kwaɗayin abin duniya sai wanda kaga dama kake dubawa, la nuna cewa sai masu kuɗi za ka duba lafiyarsu indai mutum talaka ne ko yana neman taimakon gaggawa bashi da kuɗi a lokacin ya nemi ka taimaka ka dubasa amma sai ka nuna kai sam kuɗi ne a gabanka ba ceton rayukan al'umma ba kamar yadda ka yi ikiri lokacin amsar aikin, asibitin da iya kuɗi kati ake biya kyauta ne komai kai kuma da ka zo duk ka canja komai in an zo sai an biyaka kafin za ka kalli mutane, ka tafka babban kuskure a rayuwarka dan yau ba mai cetonka kamar yadda kaima baka ceton masu neman ka taimaka musu.." Haƙuri ya dinga basu yana ce musu zai gyara su kuma suka zaneshi ta ko'ina ba kakkautawa sai da aka fidda masa haƙurin gaba kana daga bisani aka dinga barbaɗa masa wani ruwa mai yauƙi, duk inda aka zuba masa a jikinsa sai yaji wata irin azaba marar musaltuwa yana ta birgima yana roƙon su masa rai za8 gyara mugayen hakinsa ba zai sake, sai kusan asuba kana komai ya lafa aka bar shi anan warwas a sume.. _________________________ Da sauri-sauri take fitowa zuwa harabar gidan tana kiran Ɗanladi direba ya fito da sauri yana washe haƙora ya ce" Barka da fitowa Autar Hajiya yau ma dai da alama kin makara." Ɗan cuno baki ta yi tana ɓata fuska ta ce" Yo Yaya Ɗanladi Mommy ce yau ta makara bata tasheni da wuri ba ga Anty Fadila komai da Mommy ta mata kamar wata babyn goye yanzu dai muje kar a zaneni kaji." Murmishi ya yi cike da jin daɗin ta kirasa da Yayanta shi ya sa yake matuƙar ƙaunar Auta saboda hankalinta ga kuma girmama na gaba da ita da sanin yakamata motar ya shiga itama ta shiga har ya tada motar ta ce masa ya dakata ta fito da sauri ta gaishe da Baba Maigadi, cike da kulawa ya amsa tare da saka mata albarka kana suka bar gidan. Suna isa inda suka saba haɗuwa da Amra ta fito da sauri tare da wata leda blue ta samu gefe ta aje haɗe da wata takarda akan ledar ta samu wani dutse dan ƙarami ta ɗaura dan kar iska ta ɗauki takarda kana ta juyo da sauri ta wuce mota suka bar wajan, sai da suka kama hanya ta tuna yau fa suna da exam kuma bata karanta komai ba hakan yasa ta rafka tagumi tana tsoron ace bata ci abin da za a musu ba, Ɗanladi ya dubeta ya ce" Auta lafiya dai ki ka yi tagumi?" Ajiyar zuciya ta sauke kana ta ce" Jarabawa garemu kuma ban karanta komai ba." "Karki damu in sha Allah ma za ayi wanda bazai baki wahalar ganewa ba.. Jinjina kai ta yi ta ɗago kanta sai taga sun ƙaraso makarantar, sallama ta masa ta fita. Da sauri ta iso bakin ƙofar ajinsu tana addu'ar ba malamin da take tunani ba ne ya soma koyarwa, tana leƙawa taga shi ɗin ne dai hakan yasa jikinta ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31