Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ci gaba da kukanta. Auta! Auta! Kina ina ɓoyewa kika yi ne wai? Ki zo mu tafi ɗaukan Mommy ta kusa isowa" Sudas ne ki kwalla mata kira yana nufo ɗakinta.. Wani irin tsaki Auta taja tana sake yin miƙa ta kuma cewa" Nidai ka dawo bamu gama magana ba." Buga ƙofar Sudas ya soma har ya gaji ya rabu da ita ya koma ƙasa. Wani haske ne ya haske fuskarta kana daga bisani ya shige jikinta, kamar ƙiftawa da bismillah bacci ya kwashe ta.. Zau ne suke a cikin wasu furanni masu kyau gefe guda kuma ruwa ne ke ta gudu tsintsaye nata shawayi a saman ruwan, gyara za ma tafi ta dube shi cike da shagwaɓarta mai narka masa da zuciyata ta ce" Shi ne har za ka gudu ko?" Dan murmishi ya saki kawai sai ya kamo hannayenta cikin nuna kulawa ya ce" Afra ai ba zan taɓa guduwa na barki ba har abada ni dake mutu ka raba, ke ko kin mutum ma ba zan auri kowacce mace ba zanke magana da ruhinki." Lumshe idanu ta yi tana jinjina kai alamar gamsuwa da maganar shi, ɗago da idanunta ta yi ta ce" Bobby kasan yau mai Anty Fadila ta mini kuwa?" Tuni annurin fuskar shi ya ɗauke ganin fuskar abar ƙaunar tashi babu annuri, Afra me ta miki maza faɗa miki yau saina rama miki hankalina zai kwanta." Shuru ta yi ta zuba masa idanu ganin yadda nasa idanun suka canja kala, ta riƙe hannunsa tana murmishi ta ce" To ka duba da kanka mana ai nasan kama san komai kawai rama mini ka ki yi, shi kenan yanzu ka dena sona shi ya sa ake cutar dani baka rama mini" Ta ƙarashe maganar tana sa kukan ƙarya." "A a kar ki zubar da hawayenki abar ƙauna, yanzu kafin ki gama magana naga komai , ki rabu dasu zan koya mu su hankali ɗaya bayan ɗaya, ɗazu naga Namir a tare dake nu na bashi tsaronki na yi wata tafiya mai nisan gaske, zo nan kar ki yi fushi dani kinji abar ƙauna" Ya ƙarashe maganar yana rungume ta tare da bubbuga bayanta yana mata kalamai ma su daɗin sauraro.. Murmishi ta yi ta kuma shigewa jikinsa tana lumshe idanu. "Bobby yaushe za mu yi aure wai? Ta faɗa idanunta a lumshe.. Murmishi ya saki tare da shafa gashin kanta ya ce" To ai aure da kin shirya ko yanzu kawai mu yi ni a shirye nake ina so ki dawo inda nake muci gaba da rayuwarmu mai daɗi ki haifa mana yara masu kama dake, bana so na taɓa ki har sai mun ɗaura aure." "Ke dan uwarki maza tashi ko yanzu in zuba miki ruwan sanyi. Zabura Auta ta yi ta tashi sai kawai ta fashe da kuka, sake da baki Sauban ke kallon Auta ganin yadda take kuka kamar ya rabata da wani tsagin rayuwarta, zama ya yi akan gadon ya kamo hannunta ya ce" Buɗe idanunki Auta kina ta bacci ƙarfe biyar da rabi naga ba ki ce kin mana iyayin da ki ka saba ba ne, shi ya sa nace bari na leƙoki ko lafiya kike kuwa ashe kina nan kina bacci yau dai ba ki takura mana ba ki ce ba mu sallar La'asar ba, kinga yau kema kin za ma irinmu tun da ba ki yi sallar ba" Ya ƙarashe maganar yana mayar da eapis ɗinsa kunne ya miƙe ya fita daga ɗakin yabarta baki buɗe tana kallonsa jin abin da ya faɗa mata.. "Subhanallah! Ya furta jin zuciyarta na bugawa, da sauri ta sauko daga kan gadon tana mamakin abin da ta gani a mafarki, to waye shi wannan ɗin? Ta faɗa a fili yayinda ta shiga toilet ɗin. Bata jima ba ta fito ta tada salla tana gamawa ta yi addu'a kamar yadda ta saba amma duk sai taji jikinta ba daɗi bata jin karfin jikinta, miƙewa ta yi ta ɗauki Teddynta ta sumbata kana ta shiga wanka ganin lokaci na tafiya Mommy ta za ƙaraso a ko wani lokaci.. Tana shiga ta haɗa ruwa ta shiga ta Lumshe idanunta sosai mafarkin da ta yi ya tsaya mata a rai, photon wanda ta kira da Bobby take haskowa a idanun zuciyarta, haka dai ta yi wanka ta fito ta shirya ta sauka ƙasa ta zau na bata kula Sudas dake mata dariyar makarar da ta yi a salla.. Hon suak ji ana ta yi, da sauri Auta ta miƙe ta nufi ƙofa tana faɗin" Oyoyo Mommy. Ɓata rai Fadila ta yi tana faɗin" Yanzu ƴar sa'idon nan ta dawo kuma ba dama ka yo abin da ranka yake so sai ta saka maka na mujiya tsuwww" Taja tsaki tana nufar ƙofar fita daga palon." Dariya Sudas ya yi yana rage volume ɗin TV da waƙa ke tashi ta turanci ya kalli Sauban ya ce" Ya dai kai kuma ka wani zau na ko ka dena zuwa taro Mommy ne?" Pilo ya ɗauka ya jefo masa yana nunasa da hannu ya ce" Babu ruwanka ɗan sa'ido ba dai ka ce aure za ka yi ba? To Mommy na hutawa zan antayo mata labari tun daga A har Z ba zan yi tsallake ba." "Amma Wallahi da ka birgeni matuƙa bro, ka rashi mu fita kafin ta nemi inda muke.. Motar na yin parking direba ya fito da sauri ya buɗe mata ƙofar mota, wata kyakyawar mata ce ta hakimce akan kujera sanye take da doguwar rigar material pink haka ma mayafinta pink ne, matar za ta kai shekaru 48 zuwa da 49 fuskarta dauke da murmushi ta fito daga motar tana sauke ajiyar zuciya. A guje Auta ta iso gareta ita kuma ta ware mata hannaye ta rugume ta tana faɗin" Miss you so much my darling daughter ina matuƙar kewarku ba ki ɗaya, ina 'yan uwan naki suke?" Auta ta ɗago za ta yi magana sai ga Fadila ta su Sauban na biye da ita sun iso, sakin Auta ta yi Fadila ta iso tana kumbura baki ta rungume ta ta ce" Mommy damejo ni dai ban yi kewarki ba, ya Amurka?" "Mi kike cewa Fadila?" Mommy ta faɗa tana ɗago da ita daga jikinta. "Cewa na yi mun yi kewarki gidan shuru ba daɗi da ba ki kusa." Murmishi kawai Mommy ta yi dan sarai taji mai ta faɗa, sakinta ta yi Sudas ya iso ya rungume ta yana cewa" Miss you Mom ya hanya?" . " Alhamdulillah my Son ina shi Daddyn naku yake? "Bai dawo ba. "To muje ciki.. Ciki suka shiga Auta na manne da Mommy suka shiga ɗakinta, sai ta taga ta shiga wanka kana ta fito tare da ɗauko wayar Mommy ta shiga kallon picture ɗin da ta yi a can Amurka.. Abinci mai rai da lafiya Kandeta haɗawa Mommy ta fito ta zau na akan darning, takaici ne ya kama Mommy ganin dukkansu waya suke dannaw wata ce kawai ki rungume ta Teddynta tana masa wasa,sosai ta yi mamakin ganin yadda Auta ta girma bata mata kukan data saba ba in har ta dawo daga tafiya ta yi ta binta duk inda ta yi banɗaki ne kawai bata binta, yanzu gashi ta dawo kuma sai taga canji daga welcome back

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});