Chapter 15
Chapter 15
ɗin data mata bata kuma kallon inda take ba. " E lalle su Autar tawa an soma za ma 'yan mata" Ta ƙarashe maganar tana murmishi.. "Ku ba za ku ci abinci ba je ko mai? Yamutsa fuska kowa ya yi sai kuma suka tashi suka isa kowa yaja kujera ya zau na, Auta ta janyo babban filet ta cika shi tam da shinkafa da miya ta nama manya-manya, ba mata lokacin ta dinga kamar wadda ta shekara bata samu irin wannan abincin ba.. Sake da baki Mommy ke kallon Auta. "Kici abincin a hankali mana Auta. Jinjina kai kawai ta yi, Fadila ta buga tsaki ta zubawa idanu . Mommy ta juyo dan ta yiwa Auta magana taga wayam kan darning ɗin, baki ta saki tana bin kwanukan da kallo Auta dake zau ne ta yi rashe- rashe tana mayar da numfashi sai zare ido take, cikin ya zama babban kamar mai shigar dan wata huɗu.. Innalillahi! Mommy Alkur'an Auta ta handime komai na kan darning ɗin, dama tun da ki ka tafi take yin wasu abubuwa, mun shiga uku mun lalace! Yanzu duk wannan abincin Auta kin dura shi a cikinki? Kuturu! Gaskiya gaban nan buhu guda za ake dafawa a gidan nan" Cewar Fadila tana tafa hannu.. Miƙewa Auta ta yi shuuu kamar wadda ake turawa suka ga tabar wajan ta yi sama.. Dariya Sudas ya yi ya ce" Auta fa ta haukace Mommy samo mata magani." "Dole na nemo magani wannan wacce irin masifa ce haka da Magaribar nan? Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Dama haka take yi wai tun da na tafi? Labari Fadila ta shiga bata tiryantiryan, tafa hannu kawai Mommy ke yi ta miƙe da sauri ta ɗauke mahafinta ta fice a gidan... Bala mai shayi ƙarfe shadaya daidai ya tashi daga wajan sana'ar shi, sauri yake yi dan ya yi dare gashi gidan shi sai ya bi gindi wata makabarta hakan ya sa yake sauri dan dama matsoraci ne.. Yana zuwa saitin makabartar ko numfashi da kyar yake yi saboda tsoro, sai da ya wuce ya sauke ajiyar zuciya, ya zo gindin wata bishiyar mangwaro ya ji ana surutai sai mamaki ya kama shi yana tunanin wasu yara ne haka suke wasa har wannan lokacin.. "Kai baka isaba ni na rigaka zuwa da minti ɗaya. "A a nine na rigaka lokacin da na yi nutso a tekun maliya saida na kai can kasa ina hutawa kafin ka zo, taya ma za ka ce ka rigani zuwa? "To ai kaima lokacin da na isa bangon duniya na kudu sai da na yi hutun awa ɗaya, har sai da na soma bacci kana ka zo kaga ai na rigaka yanzu dai ni na riga amma ka ce wai ka rigani zuwa kasan tekun.. Rikice ne ya rikice kowa na cewa shi ya riga ɗan uwansa. Jikin Bala shayi tana ya ɗauki rawa dan ya duba har haskawa ya yi jikin bishiyar amma baiga kowa ba a gurin, ji ya yi ana damke sai sautin dukan yake ji, giririf! Kawai yake ji kamar ana dukan ƙarfe. Cikin Bala mai shayi ne ya bada kuuuuuu bai sna lokacin da ya saki futsari ba, runkuyawa ya yi zai cire takalmansa yaji an zabga masa mari ji kake gauuu. Wata irin sufa Bala ya yi ya watso kwanar gidansa a guje yana faɗin" Dije! Dije! Dije masa buɗe mini ƙofa Dije kina ina? _*One love masoya ina sonku irin sosai ɗin nan, ina matuƙar godiya a gareku yadda kuke mini fatan Alkhairi na gode Ubangiji ya barmu tare daku, da wanda nake gani da wanda ban gani ba masoyan ina Alfahari daku a duk inda kuke na fili dana ɓoye.*_ _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [03/12, 21:49] Umma Amjad: _*🧟♀️ALJANAR GIDANMU 🧟♀️*_ Daga Alƙalamin _Sarat Alƙasum (Maman Nusaiba)_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ *WhatsApp number.+966599791573* بسم الله الرحمن الرحيم 0️⃣8️⃣ "Dije maza buɗe mini ƙofa ki taimaka Dije na, Innahu Sulaimanu ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba Dije ki yiwa girman Allah ki buɗe mini ƙofa kar ki rasa haɗaddan mijinki Dije" Ya ƙarashe maganar yana ja da baya ya yi wata irin sufa ya buga ƙofar da ƙarfi gaske ya ci sa'a ta buɗe.. A firgice Dije ta fito daga banɗaki tana kallon Bala, ƙanƙance idanu Dije ta yi cikin masifa ta ce" Kan uban can! Bala waye ya baka izinin buga mini ƙofa kamar ka samu tabin hankali? Wai lafiya ma tun daga ƙofar gida naji kana kirana? Salon iska ta ɗauki sunana ko mayu ayi ta yawo dani aje a lika mini maita, to Wallahi ba ka isaba yau ba za ka kwanan mini akan gado ba kai ɗakin ma za ka kwana ba sai dai ka kwana a shagon shayin naka, ina jinka yau da zaka fita kana ce mini wai juya bana haihuwa,to ka yi da shegiya a gidan nan dan za kaga rashin mutumci yadda baka tunanin maza ka fitan mini a ɗaki ko yanzu na maka ɗan banzan duka a cikin daren nan" Ta ƙarashe maganar tana turashi bakin ƙofa." "Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Yake faɗa yana kallon Dije sake da baki, tun da yake da Dije bai taɓa jin ta tanka masa magana ba ko dukanta ya yi bata zuwa gidansu za ta yi haƙuri ta zau na, duk gurin da yake mata bata taɓa tanka masa akan hakan ba, kuɗin cefane sai ya yi wata bai bata ba kawai sai dai ya ce mata ta tafasa ruwa tasha shi ne abincinta, amma yau gashi Dije ce ke masa tsawa har tana cewa za ta masa duka. Anya kuwa ba wani ya zuga mini Dije na ba? Ya faɗa a bayyane.. Kafin ya yi wani yunkuri Dije ta ɗamko hannun shi tana aiko masa harara ta ce" Shin za ka fita ko saina lallasa ka a ɗakin nan?" "Don girman Dije na ki yi haƙuri gamo na yi a hanya shi ya sa, Aljannu fa naji suna muso a tsakanin su wai anje bango duniya da kudu,kuma k.. Bai ƙarasa ba aka ɗauke wutar ɗakin, hankali tashe ya lalibo Dije ya maƙale a jikinta kamar zai koma cikinta. "Kai ka sakeni dalla can so kake ka shiga cikina ko me? Ganin fa yaƙi sakinta ta taƙarƙare ta zuba masa dundu a gadon baya. Ba shiri ya saketa ya dawo bayan yana cewa" Shi kenan na shiga uku sun biyoni har g.. Marin da Dije takai masa ne ya hana shi ƙarasa maganar, dukansa ta shiga tako ina har da ƙafa take sakawa, cikin wata iriyar murya ta ce" Ni za ka yiwa wulaƙanci har kasa hannu kake dukana? Yau saina karya maka hannu da ƙafa." Ihu Bala yake yana roƙon Dije da ta rabu dashi, ita kuwa sai ma ƙara kaimi take ganin dukan da hannu bai mata ba ta juya gefenta ta ɗauko muciya ta shiga zuba mi shi ita tana cewa" Gobe ma ka sake dukana za kaga mai zan yi maka a gidan nan, ni Ƙawar uwarka ce har ka ɗaga hannu ka dakeni?" "Waiyo Allah jama'a a kawo ɗauki, Dije nine fa Bala ɗinki ki dena dukana na miki alƙawarin ba zan sake dukanki ba, Dije mijinki ne fa kar ki nakasa ni ki taimaka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31