Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

janta ake yi ana yin ƙasa da ita.. Wuta ce ƙarama ta bayyana a palon a inda Fadila take kwance tana neman taimako, a hankali wutar ta dinga nufar Fadila tana wani irin ci bal bal bal kamar wutar gobara, tana isowa kusa da Fadila ta ɓace fat abin da ya ƙara hargitsa su gaba ɗaya kowa ihun ceton rai yake, kaf cikin su ba wanda ya yi tunanin yin addu'a sai ihu da faɗin sun shiga uku. Kafar Fadila aka ja kiiiii zuwa bayan jujera aka haɗa ƙafar da jikin kujera aka buga da ƙarfi ji kake ƙasss! Wani irin ihu Fadila ta kurma saboda tsananin azaba ta saki zawo da futsari a tare , kuka take tana riƙe ƙafar dake jikin kujera an maƙala ta, ja take amma ta kasa fiddawa nan da nan ƙarfinta ya ƙare ta yi lakwas tana mayar da numfashi. Sudas na jikin Sauban a sume yayinda shi kuma Sauban jikin shi yake rawa haƙoransa sai gamewa suke saboda tsananin firgita da tsoro, da ya juya gefe sai ya ga Mage na ruƙo masa idanuwa sai ya yi saurin rufe idanu, in kuwa ya rufe ƴar Teddyn Auta zaike gani tana neman kai masa cafka sai ya yi saurin buɗe idanunsa. Ji ya yi an tsikara masa wani abu mai kama da allura a wuyan shi ba shiri ya kurma ihu har bai san lokacin da ya zabgawa Sudas mari ba , sake tsikara masa aka yi a kafaɗa ya zabura ya amma ya ƙasa tashi kamar an dasa shi a gurin kasancewar Sudas ya maƙale masa gashi da mugun nauyi kamar buhun suminti babba, gurin ya shafa aikuwa yaji damshi a wajan ga duhu ya kasa ganin ko mene ne, shinshinawa ya yi warin wani abu mai tsami ya daki hancinsa ya yi saurin gogewa a jikin rigarsa, cikin jin zafi da zugin da gurin yake nasa ya ɗaga ɗayan hannun ya laftawa Sudas mari wanda ya yi sanadiyar dawowar numfashinsa daga suma.. "Waiyo Allah! Cewar Sudas yana dafe kuncinsa cike da jin zafin gurin, ɗago kai ta yi ya buɗe idanunsa ya ga duhu ko tafin hannunsa baya gani abin da ya ƙara tsorata shi matuƙa, ɗaga kai ya yi sama duk da baya ganin komai sai duhu ai kuwa ya yi arba da Auta a saman ginin ta yi ringeshe tana kallonsa fuskarta ba alamun wasa, ihu ya kuma kurmawa yana ƙoƙarin komawa jikin Sauban yaji saukar duka a gadon bayan shi, kiran Mommy yake yana ta taimake shi ana ta ci gaba da dukansa, idan ya kira sunan Mommy sai a lafta masa tafi a fuska nan da nan fuskarshi ta kumbura saboda marin da yake sha, tun yana ihu har ya gaji ya dena sai dai na Sauban yaje jiyowa wanda shi kuma ake ta caka masa wani abu kamar allura a duk inda aka samu na jikinsa.. Dariya aka ɗauka a palon zuwa can suka ji sukuwar Dokuna suna ýowa inda suke zau ne, tuni kowa ya dinga ihu ga babu karfin da za su motsa koda ɗan yatsarsu ne hakan ya ƙara firgitasu ba kaɗan ba.. Tun da aka fara abubuwan nan Daddy ya manne a jikin wani lungu wanda yake dauke da kayan game ɗin Auta da sauran kayan kallo, a sauri ya ɗauko wani zobe jikinsa na rawa ya saka a hannunsa yana mayar da numfashi, kamar ƙiftawa da bismillah yana saka ya ɓace fat a gurin.. Mufy ta yi rashe-rashe saboda yadda ta buga ƙugunta a jikin ƙafar kujera, numfashi take mayarwa tana nishi kamar ana zare mata wani ɓangare na jikinta haka take ji, wani irin naushi aka kawowa gefen bakinta ai kuwa ta fasa ihu jikinta ya ɗauki rawa sai futsari ta sume, gashin dokin data yi kitso dashi aka kama tass aka washe kitson gaba ɗaya, wani kalar raɗaɗi take ji kamar kanta baya jikinta ihun ma da take ta kasa sai dai ta dinga nufashin tana kurgumki. Ƙassss! Hannunta ya bada sautin ƙaran nan cikin wani irin amo Mufy ta zabga ihu tana juya kanta tare da jan jiki tana birgima kamar wata macijiya, "Waiyo! Na mutu na lalace a taimakeni zan mutu ban gaji da duniya ba z.. Bata ƙarasa ba taji an yi sama da ita aka shiga yin ƴar wurgiya da ita, tuni cikinta ya kaɗa tana ihun a taimaketa sai kwalalo idanu waje take yi ganinta ita ba sama ba ita ba ƙasa ba tana tsakiya.. Auta dake zau ne akan kujera ta maƙale ƴar Teddynta ta yi shuru idanunta a rufe, gizo masoyin nata ya dinga mata da zarar ta rufe idanunta shi take gani yana ware mata hannaye alamar ta zo gareshi, kamar iska haka aka ɗauki Auta aka yi ɗaki da ita. Daret gado aka yi da ita tare kwantar da ita, hamma ta dinga yi tana miƙa idanunta a rufe ta miƙa hannu ta janyo bargo ta rufa... Zau ne suke ta yi matashi da cinyar shi hannayen shi na kanta yana shafa lallausan gashin kanta, murmishi ta saki ta ɗago kanta tare da cuno baki gaba tana hararar shi. Ƴar dariya ya yi ya ce" Ya akayi ne shalelena?" Lumshe idanu ta yi sosai sautin muryar shi ta narka mata da zuciya, à hankali ta ce" Bobby miss you"Ta ƙarashe tana masa kukan shagwaɓa. Da sauri ya tasheta ganin zubar hawayenta hankalin shi ya tashi ya shiga tambayarta. "Shalele yi haƙuri kar ki mini asarar hawayenki masu tsada ki taimaka bana son ganin kina ɓacin rai, kwana biyu ina son mu haɗu dake amma aiyuka sun mini yawa shi ya sa ban samu na zo na kula dake ba, ɗago fuskarta ya yi ya zuba mata idanu suna haɗa idanu, wani haske ya fito daga idanunsa ya shiga nata idanun ta yi saurin sauke ajiyar zuciya ta yi baya zata faɗi ya hura mata iska ta buɗe idanu. Idanunta suak kawo ruwa ta kalle shi kamar za ta saka kuka jin yadda take jin son shi na ƙara nunkuwa a zuciyarta ji take kamar ta mayar dashi cikinta saboda yadda take ji har wani rawa jikinta yake yi, numfashi ta kuma saukewa tana ƙara ƙura masa idanu kana ta ce" Bobby!. Wani shu'umin murmushi ya saki yana binta da kallon ƙauna ya ce" Na'am Shalelena wai yau lafiya kike ta rigima?" Kuka ta saka masa tana kallonsa. Dafe kai ya yi yana murmishi ya kuma cewa" Me kike na miki yanzu ki dena kukan nan?" "Cikina Bobby yana dan mini ciwo bacci kuma nake ji, Bobby kuma zan ci abinci yunwa nake ji.. Ƴar dariya ya yi ya miƙa hannun shi baya sai ga abinci a cikin trey ya bayyana ya miƙo tare da ajewa a tsakiyarsu, nuni ya mata da ga abincin. Waro idanu ta yi tana kallonsa cikin jin daɗin ganin abin da tafi ƙauna macaroni da naman kifi ga miya a gefe ga ruwa ga lemon juice mai sanyi, wani irin yawu ta hadiye tana buɗewa ta soma ci yau dai ba bismillah ta shiga antayawa cikinta, shi kuwa ya zuba mata idanu yana sakin murmishi har ta gama, da kanshi ya wanke mata hannu ta wanke bakinta. Hamma ta kuma yi ta ce" Bobby bacci"،Ta ƙarashe maganar

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});