Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 12

Chapter 12

Aljanar Gidanmu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

baki tana kallon Kande dake jera mata sannu, kasa daurewa ta yi ta ce" Wai Kande kina nufin duk wannan ta'asar da aka yi a palon nan ba ki ji ba ko me kike nufi da kika fito kina jero mini sannu?" "A a ni gaskiya babu abin da naji ni na ɗauka ma kun fita ne taryar saurayin naki da ki ka ce zai zo daga Abuja zuwa nan Katsina, to amma mene ne ya fasa miki goshi faɗuwa ki ka yi ne? Tsaki Fadila ta yi amma zuciya cike da mamaki take na abin da Kandan ta faɗa yanzu, to taya za ace duk wannan ɗibar albarka da aka musu amma ta ce wai bata ji komai ba kai anya kuwa ba aljannu ba ne a gidan nan? Fadila ta faɗa a ranta. Tsaki ta kuma ta miƙe da ƙyar ta janyo ruwan da Kande ta kawo ta kwarawa Jon a fuska. "Innahu Sulaimanu! Ya faɗa a firgice yana zare idanu, shuru ya yi yana binsu da kallo baki buɗe. "Kai dalla can banza ka wani saki baki kama kallonmu ko mun canja kamannin ne ba mu sani" Cewar Mufy tana aiko masa da harara fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye da majina kamar wani ƴar 3 years.. kashewa da dariya ya yi duk da hannun shi dake masa azabar ciwo, da hannu yake nunata yana dariya ya ce" Wai ina ruwan gajala kalli hancinki ya fage kamar an taka makilin a rana, Fadila ki kira mana wanda zai gyara mini hannuna, ina fa jin na goce ne amma dai kuna da Aljannu a gidan nan ko?" Tashi ta yi da ƙyar suma suka taimaka masa ya tashi suka dawo kan kujera. "Wallahi Fadila da alama kuna da Aljannu a gidan nan, yanzu bari na kira ƴar Maigado ta zo ta koran mana su, haba kalli fa sai tsami wasu suke muje ku yo wanka a ɗakin Fadila wasu kuma ku yi a nan falo" Cewar Mufy tana kallon Fadila.. Fadila ta yi tafi ta ce" Chass ashe ma ke kin san ƴar Maigad? To ki kira mana ita ta zo ko na saka direba ya zo ya kawo mana ita dan Wallahi ba zan dena birthday ɗina ba saboda wata aljana can, kira mana ita yanzu yanzu nake so ta zo ba sai an jima ba.." Ok kawai Mufy ta faɗa tare da danna mata kira, ringing biyu ana uku ta ɗaga tare da yiwa Mufy kirari. "Yarinya mai tashe mai abin mamaki, gwamnoni naki Ministoti naki.. Wani Farr Mufy ta yi da idanu kana ta ce" Yawwa ƴar Maigado kina jina yanzu ki nakeso ki zo gidan su Ƙawata aljannu ne suka shigo mu su , inaso ki zo ki ci ubansu." "Ba ki da matsala ta hannun dama ta, yanzu za ki ganni na iso kawai kwtance nakeso ki mini. Kwatance Mufy ta mata sannan ta kashe kiran... Babu jimawa sai ga ƴar Maigado tun daga ɓakin get ta afka turaren hayaƙi tana karkada gashin kaza dake hannunta, Maigadi ya rafka tagumi yana sallallami tare da kallon ƴar Maigado tana yin wasu yaruka da bai san wani kala ba ne. Daret cikin palon ta shigo da jagorancin Mufy ta yada zango a kasan carpet sai sunbatu take.. Fadila ta miƙe ta iso kusa da ƴar Maigado ta sakata a gaba ta soma rattabo mata bayani kamar an jonata. " Ranki ya daɗe ƴar Maigado ki taimaka ki korar mana wannan aljannun dake gidanmu, yanzu haka sai da ta mana dukan tsiya ina so ma ki duba mini Ƙanwata dan na lura da an taɓa ta sai kawai kiga abubuwa suna ta faruwa, ko kuwa dai ɗiyar aljannu ce ba mu sani ba?" "Kwarai kuwa yarinya wannan ba shakka aljani ya yi cikinta ba mutum ba, maza kira mini ita nan na fitar da aljannun dake jikinta" Cewar ƴar Maigado tana kara zuwa ciyayi a cikin garwashin dake cikin wani ɓakin kasko.. Fadila ta yunkura kenan za ta tashi sai kawai taga Auta a zau ne a ķusanta, zabura ta yi ta fasa ihu tana cewa" Kin gani ko haka take fa kuna zau ne sai dai kiga ta bayyana wallahi aljana ce Auta, ki taimaka kar ta kashemu a gidan nan." Wani kalar murmishi Auta ta yi ta kalli Ƴar Maigado, ƴar dariya ta yi tana kaɗa kai ta ce" Anty Fadila wannan kuma ita wace ce daga ina ta zo? Ƴar Maigado ta ɗauko wani ruwa a cikin wata tsohuwar langa ta watsawa Auta tana cewa" Tun muna mu kaɗan ku fita daga jikinta kafin na muku hayaƙin Ƴar Mairo mai barkono, bana wasa daku maza ku yi magana na ce." Rintse idanunta Auta ta yi jin wani ruwa mai wari ya kawo mata ziyara, cikin shashshekar kuka ta ce" Allah ya isa muguwa azzaluma mai na miki kike zuba mini ruwa mai wari da tsami? Waye ma ya ba ki izinin shigowa gidanmu?" Iye! Wato ma ni ce azzaluma ko? Za kuga azzaluma ajin farko yau in baku fita daga yarinyar nan ba, miƙewa ta yi ta zaro wani bulala ta maina mai kauri ta tsaya akan Auta ta ce" Shin za ku fita ko kuwa sai na nuna muku ni a ƙasan gada aka haifeni na kuma gado iyayena da kakannina wajan bayar da maganin irinku? Zan nuna muku alnahin kamata yanzu nan in baku fita ba.." Auta ta zubawa Ƴar Maigado idanu dan ita dai ta rasa akan wa ake maganar nan, gashi kuma taga ta zo kanta ta tsaya tana mata wasu maganganun banza da wofi, tsaki taja tana ƙoƙarin tashi sai taji an mayar da ita an zaunar... "Ku ɗaure mata hannu ta baya har ƙafar ma" Cewar Ƴar Maigado. Kafin sakon biyar tuni sun ɗaurewa Auta hannu da ƙafa sai kuka take tana faɗin" Waiyo Allah Mommy! Wai mai na muku ku sakeni Islamiya zan tafi fa Anty Fadila ki ce su sunceni please and please" Ta faɗa tana zubar da hawaye." Bash ne ta dubi Ƴar Maigado ya ce" Haba ranki ya daɗe ya za ku ɗaure mata hannu da ƙafa kamar wata mahaukaciya, gaskiya ku since mata jiki ko ma mai za ayi ya kasance tana zau ne za ayi." Kai fa dama mahaukacin ne ɗan rainin hankali taya za mu yarda a Kunce ta sai kace ba yanzu aka gama lallasa ka ba" Cewar Fadila tana dungure masa kai.. Ƴar Maigado ta ɗaga bulala ta zabgawa Auta a gadon baya. " Innalillahi wa'inna ilaihin raju'un! Ta kasheni waiyo Mommy dama Anty Fadila ba ƙaunata kike ba shi ne ki ka kawo mai kasheni har gida me na miki a rayuwar ta duniya da har ki ka zaɓi kisa a kasheni? Anya kina da imani kuwa?" Ta faɗa cikin ƙaraji tana mutsu-mutsu dan ba ƙaramin zafi da azaba taji ba.. Sake ɗagawa ta yi za ta kai mata wani duka aka yi sama da ita aka sakota ƙasa tim! Bata yi ihu ba sai ta miƙe da ƙyar dan kar su ga kasawarta ta ce" Aljannun nata suna da lafiyar kai yanzu zan musu mai gaba ɗaya, sake nufar Auta ta yi da kanta yake ƙasa tana kuka wiwi har da majina, ɗagawa ta yi za ta sake

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});